ABDUL JALAL

1.3K 25 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 6️⃣1️⃣115

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

     

              _MY FIRST NOVEL _

Mummy tace "kai gidan Jalal fa nace zaka kaini"
Driver ya ƙara risina kai yace "eh Hajiya shi din fa, Jiya da daddare yazo layin nan shida matarsa, yace inje in kaisu filin jirgi yau, ɗazu na dawo daga kaisu"

Bata tsaya ta ƙarasa ji ba ta koma cikin gida kirjin ta yayi mata nauyi take tambayar kanta

"wace irin tsana Jalal yayi min har yazo layin nan ya tafi be ganni ba, be leƙo mun gaisa ba? Yazo shida matarsa suje gidan su matar sa amma suka kasa shiga su gaisheta, take ta kara jin wata muguwar tsanar Jalila tasan tabbas wannan makircin Jalila ne"
Da ta sake tuna cewar Daddy zeyi aure setaji gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi, tarasa me yake damun ta, kowa ya guje ta ya juya mata baya ciki hada dan cikin ta, ga dukiya tari guda, dukiyar da take ta hari tana kwaɗayi gata nan a jibge amma sam yanzu hankalinta ba'a kan dukiyar yake ba, da anjima kuma idan ta sake tuna irin masifar shaye2 da Jalal yayi, da yadda take riƙe da Ilham kaman ita ta haifeta ta tuna Abunda Saudat ta aikata mata se taji kaman a duk duniya ita ka ɗai aka tsana tarasa me zatayi taji daɗi, bacci ya ƙauracewa idanun ta, bata jin yunwa ma balle tasaka ran zata ci Abinci, idan tasa Abinci a gabanta za taci kuwa ji take babu test babu daɗi, bata da aiki se tunani da koke koke, Ankwace mata miji, wata ta kwace mata ɗanta ɗaya tilo se yadda tayi da shi, gashi 'yar uwatta data yadda da ita taci amanar ta tayi mata cutarwa mafi muni, ga ba wanda yake son rabarta saboda izzarta da jin kai da wulaƙanta mutane, nan da nan abubuwa sukayi mata yawa, ta fara fama da wani matsanancin ciwon kai da yake sakkowa har wuyan ta ko gani bata iyayi sosai, tunda Daddy ya tafi ko message be mata ba balle ya kira ta, saɓanin da da idan ya tafi se suyi waya sau biyu zuwa uku, yanzu ya tattara ta ya watsar ya shiga harkokin sa da shirye shiryen maida Auren sa.

7 hours cif su Jalila suka shafe ana tafiya a jirgi sannan suka isa London babban birnin England, Jalila ta gaji sosai tun ana tafiyar ta marmari tazo ta gaji, ta fara yamutsa fuska daga karshe ta kwanta a jikin Jalal tai bacci.

Jalal ya tashe ta suka sakko daga jirgin, yanayin weather garin ce ta tabattar mata lallai ta baro Nigeria, wani irin sanyi ne me ratsa jiki taji yana dukan ta, ta ɗaga kai tana kallon yanayin garin dukda dare ne amma tasan akwai banbanci da gida Nigeria, komai nasu cikin nutauwa da tsari, bayan sun gama clearing komai Jalal ya ja hannun ta sukayi gaba, wajen wata mota suka nufa kafin su karasa inda motar take aka bude motar na cikin motar ya fito.
Mahmud ne mijin Nana yazo ɗaukar su.
Cikin fara'a yace "Sannunku da zuwa bros nasan kun sha hanya, da ganin idon Jalila a gajiye take"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now