ABDUL JALAL 92

390 25 1
                                    

..🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


*ABDUL JALAL*

_Story and writing_
By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girls_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️


PART 2
_PAGE 3️⃣9️⃣92

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724




_MY FIRST NOVEL _

Jalal nagama magana yasa karwa Maama hannunta, Jawwad kam mamaki da bacin rai ya hanashi magana, Maama bata taba marinsa ba, lokacin yaji yakara tsanar Naja, juyawa Jawwad yayi ya nufi part dinsa zuciyarsa tana suya, da sauri Jalila tabi bayansa ta bar su Agurin a tsaye, Jalal ma bin bayansu yayi, ita kanta Maama jikinta yayi sanyi da marin da tayiwa Jawwad, yadda taga ya sunkuyar da kai ya tafi bece mata komaiba da kuma maganganun da Jalal yayi, Amma ta maze ta cigaba da banbami.

Jawwad na zuwa ya zauna ya dafe kansa yayi shiru yana saka abubuwa daban2 a ransa, da sauri Jalila ta karaso ta zube agabansa tana kuka amma takasa magana se sheshsheka, dagowa Jawwad yayi ya zuba mata ido amma yakasa magana, Jalal ne yakaraso ya tarar dasu a haka, yasamu guri ya zauna a kusada Jawwad, ya kalli Jalila yace

"kidena wannan kukan haka, kikoma gida komai ze wuce Insha Allah"

Shiru tayi tacigaba da kukan a hankali cikin kuka tafara kokarin furta
"Am sorry Yaya Jawwad,...."
Maganar ta sarke takasa karasawa, Jawwad yace

"Jalila ke yakamata abawa hakuri, tashi kije kidena kuka, nasan abunda kikeji akan yadda akemiki a gidan nan but am really sorry komai ze wuce kinji"
gyada masa kai kawai tayi, tace "Yaya Jawwad karka canza lokacin tafiyar nan, kayita tanada mahimmanci"

"zanyi Insha Allah"

yabata amsa jiki a sanyaye, ta mike zata fita ta juyo ta kalli Jalal tace

"Ilham! Ilham.... Sekuma tacigaba da kuka ta fice da sauri ta tafi cikin gidan da yanzu takejinsa kamar prison.

Nana bata san me akeba, tana can tana manne da Mahmud a waya, dan haka koda ta fito palour Maama ta tarar tana sababi, ita zuwa yanzu lamarin Maama har tsoro yake bata, kullum cikin fada take, takoma halin 'yar uwatta na masifa ko gajiya batayi, Nana batabi kan maganar da Maama takeba ta wuce kitchen tadora girki.

Jalila ta shigo palour, Maama na kokarin shiga dakinta se hararta takeyi tana tsaki, sannan ta shige Naja ma wani tsaki tayi tace
"hmm nida ke naga wanda ze Nasara, duk wani iyayinki da iya munafurci da kinibibi na kafirai da kuka iya sedai kiyi kigama dan nafi karfinki wallahi kar nake kallonki nafiki iya tashanci, banza 'yar Arna kawai, wadda uwarta ta yasar ta tafi gararinta"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now