ABDUL JALAL 114

1K 19 2
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 6️⃣0️⃣113

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

_MY FIRST NOVEL _

Da sauri ta janye hannunta daga jikinsa, da kyar ta mike zaune ta janyo rigarta ta saka, a hankali ta sakko daga kan gadon, dan duk wata gaba ta jikin ta ciwo take mata, ta kunna switch haske ya gauraye dakin gaba daya, ta kalli inda Jalal yake har yanzu karkarwa yake kamar wanda ake girgizawa, a hankali ta tako ta zauna a kusa da shi ta dan dora hannunta a goshin sa zafin karuwa yake fiye da farko, a hankali tace

"Jalal meyake damunka ne?"

Shiru yayi be ce komai ba, gaba daya jijiyoyin kansa kaman an kumbura su har jijiyoyin fuskarsa seda suka tashi, ta tashi ta debk ruwa a container da towel me kyai ta dinga tsoma towel din a ruwa tana shafa masa tareda karanto duk addu'ar da tazo bakin ta, bude ido yayi yana kallon ta, seda gaban ta ya fadi ganin idon sa yana caccanzawa kaman yadda ta taba gani yayi kwanakin baya, salati ta dingayi
"Jalal ko Daddy zan kira ne?" girgiza mata kai yayi ya mayar da idonsa ya lumshe, MP ta dakko ta kunna karatun Alqur'ani ta dora akan mirror.
Ta cigaba da shafa masa ruwa, a hankali jikin sa yafara sanyi ya fara sauke ajiyar zuciya alamar bacci ya dauke shi, seda ta tabbtar yayi bacci ta mike ta tafi toilet dan gyara jikin ta, ji take kaman zata fadi gaba daya jikin ta babu kwari, ga ciwo da jikin ta yake mata, ta gargasa jikinta da ruwan dumi ta fito ta canza kaya, ta koma gurin Jalal ga mamakinta taga ya mike zaune amma har yanzu idonsa wani iri, takarasa gabansa tace
"Sannu ya jikin naka?"
Kallon ta yayi yai shiruu kaman wanda akayi wa dole yace "zan sha giya"
"giya kuma? Amma kasan gidana ba club bane ko?"
Kokarin mikewa ya keyi tai sauri tace "tsaya ina kuma zakaje? Bari in dakko maka ai inada ita"
Ya nemi guri ya zauna, ta fita ta dakko zamzam ta dawo ta tarar ya kashingida idonsa a lumshe tace
"bude bakinka" ba musu ya bude ta fara zuba masa zamzam din nan me dauke da tofin Al'qur'ani a ciki ya dinga sha ba tareda yasan menene ba, seda ya shanye shi tsaf kawai yafara Tari abu kaman wasa ya dinga tari kaman ze shide, zuwa jimawa kuma yafara amai, wani irin abu yake amayarwa baki kirin me kauri, tun Jalila na iya gogewa ta gyara gurin harta gaji ta zubawa sarautar Allah ido, ta koma gefe ta zuba masa ido tana hawaye.

Seda Jalal ya kusa fita hayyacinsa gaba daya, ya dinga aman nan ba kakkautawa, sedai in yayi yayi, ta goge, yayi awa yana aman nan baya hutawar minti biyar beyi wani aman ba.

Ba Jalal ba hatta Jalila ta galabaita, ga wahalar da ta sha a hannun Jalal shikuma ga wannan rashin lafiyar, da aman ya dan lafa masa ta dakko zuma ta dinga bashi da spoon yana karba.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now