ABDUL JALAL (2020) 25

278 18 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

    _ABDUL  JALAL_
           (2020)

      _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
    (Daddy's girl)

               PAGE-  25

PART 1

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum
Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
Dama dukkan masoya wannan novel ina alfahari daku ❤❤❤
     
        -My First Novel-

Not Edited


Kallonta Jalal yayi da mamaki ya kalli inda Ilham ta tarwatsa masa waya ya dawo da dubansa kanta

"Baze yiwu ba Yaya Jalal, kana wahal dani kana garani kawai dan nace inasonka, amma kalli yadda wata take bayyana maka soyayyarta baka dau wani mataki ba amma ni kalli yadda kake wulakantani sau daya baka taba kallona da idon tausayiba
Meye laifina dan nace ina Sonka?"

Shi mamakima ya hana shi magana be ce mata ƙala ba ya durkusa yana tattara pieces din wayarasa, ya tattara ya nufi waje ze bata guri, tazo ta sha gabansa

"Magana fa nake maka Yaya Jalal, let me tell you something wallahi kai nawa ne nikadai babu wata Jaka data isa tayi takara dani wallahi kowace sena kauda ita gefe"

Hawayene ke fitowa daga Idonta tana masifa, wani irin kallon baki da hankali yayi mata ya kuma zagayeta da niyyar ya fita
Janyo shi tayi takuma tsayawa a gabansa ta kalleshi ido cikin ido cikin masifa tace
"Jalal baka isaba ina magana ka maidani mahaukaciya zaka tafi ka barni, I mean what I said wallahi, zan iya komai akan cinma burina, gara tun wuri ka gargadi zuciyarka kattayi gangancin fara soyayya kaidin nawane"

Bata rufe baki ba ya sauke mata maruka biyu masu kyau,

"Har kin isa ki tsaya a gabana kina gayamin maganganun dakika ga Dama, kin fasamin waya na kyaleki be isheki ba shine zaki tsaya a gabana kina gayamin abunda kika gadama, ko yaushe ma nafara wasa dake, da kika iya tsayawa kina gayamin wannan haukan,"

"Wallahi kozaka kasheni na dena boye soyayyata a gareka koni ko ita wallahi"

Hannu yadaga ze kuma marinta
"Jalal meye haka kakeyi"
Jawwad ya karaso da sauri ya rike shi
"Haba Jalal ba girmanka bane dukan mace, me tayi maka haka, kake dukanta"
Dawo da kallonsa yayi kan Ilham
"Ilham koma cikin Gida yi hakuri banni da shi tashi kikoma Gida"
Wani mugun kallo tayiwa Jawwad a ranta tace munafiki ai kasan komai amma a zahiri ta mike ta nufi cikin Gida tana kuka
"Haba Jalal me kayi hakane abunda kakewa Ilham yafara yawa gaskiya, koba komai kanwarka ce kuma mace ce, kadena dukanta hakan baze canza komai ba Fa"
Nunawa Jawwad wayarsa yayi
"Kalli abunda tayimin be isheta ba, ta tsaya a gabana tanamin hauka"
"Dukda haka kadinga hakuri, halin mata sekana hakuri, kasan shi so makahone waima tukuna, waima ya akayi wayarka taje hannunta har hakan tafaru?"
"Mtseww manta kawai"
Shine abunda Jalal ya fada kawai ya bi hanyar fita waje
Ita kuwa Ilham tana zuwa cikin gida taga mummy a palour jikin mummy tafada tana kuka
"Ilham lafiyarki kuwa me akayi miki kike kuka,?"
"Mummy Yaya ne baya sona kwata² ya tsaneni, ni kadai nake sonshi mummy kiyi wani abu akai Dan Allah, zuciyata zata fashe"
Tausayinta ne Yakama mummy
"Is OK my dear, yi hakuri kidena kukan, Insha Allah Jalal bashi da matar data wuceki insha Allah, komai ze wuce"
"Mummy me nayiwa Yaya Jalal ne dabaya kaunata baya so naje inda yake"
"Bikiyi masa komai ba Ilham, haka dai halinsa yake na rashin son mutane, ya za ayi yace baya son mace kamarki, karya yakeyi, kidena kukan haka kar kanki yayi ciwo"
Haka mummy tai ta kwantarwa da Ilham Hankali

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now