ABDUL JALAL (2020) 22

282 18 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 24

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢
Your comments give me courage


-My First Novel-
Not Edited

Yayan Hanan se kallon Abba yake kaman yasan shi.

Tunda Jalila ta shiga office din taje tasamu guri ta durkusa kanta a sunkuye kai kace wata mutumiyar kwarai ce
Ga director na makarantar, ga Ummi, da Abban su Jawwad, sekuma baban Hanan da yayanta, se mukarabbansa da suke waje bakin office din sekuma Jalila da hanan dasuka shigo yanzu
Baban Hanan Bin Jalila yayi da kallo sannan yayi Murmushi a zuciyarsa indai wannan ce zata aikata don bata da tsoro

Kanta a sunkuye tace "Abba ina kwana"
"Lafiya kalau Jalila ya rashin ji"?
Shiru tayi ba tace komaiba
"Abbanki kawai kikasani ko Jalila,?"
Director ya tambayeta batace komai ba still shiru tayi

"Was nake gani haka kadai ace Yar baba ce wannan?"
Da sauri ta dago ta kalleshi dan murmushi tayi se yanzu ta ganeshi mutumin nan ne daya hana wannan sojan zaneta, Wanda ta tsinci wallet dinsa
"Sannu baba ina kwana"
"Lafiya kalau Yar baba"
"Dake akayi fadan kenan, dama haka kike da fada, ai wannan sister dinki ce" ya nuna hanan

"Ni ba sister na bace nikadai Ummi ta Haifa, se kanwata daya Nana" Jalila tai maganar ba tare data dago ba
Dariya tabasu gami da mamaki babu nadama a tare da Jalila ita haryanzu a ganinta ba laifi tayiba tunda ita aka takala da fada
"Daddy wai kasantane"?
Yayan Hanan yai tambayar yana kallon mahaifinsu
"Eh nasanta 'yata ce shekaranjiya Allah yabani ita"
Baban Hanan yabada amsa
Ya kalli Abba da Ummi
"Ai Dana San itace ma bazanzo ba yarinyarku mutuniyar kirkice, fitina CE kawai ta yara kuma ga dukkan alamu bata son wargine ko Yar baba?"
Ya tambayeta yana murmushi
"Komai ya wuce amma Yar baba kidena Neman magana kinji yarinyar kirki kin dagawa mamanki hankali da babanki, gaskiya suna sonki dayawa"
Gyada masa kai Jalila tayi

"To baba na dena insha Allah"
A ranta kuwa tace dama wai wannan shine captain din da ake ta fada wani salihi dashi haduwar mu biyu be tabamin rashin mutunci irin na sojoji ba
Ni na daukama zanga tunda ga bakin office anfara kwallo dani

"Daddy wai yanaga ka maida abun jokes jini fa ta fitar min kuma ta zageka"
Hanan tai maganar cikin shagwaba da hawaye a idonta
"Ohh sorry dear itama yata ce daga yau na hadaku kawance"
"What ba dai dani ba wallahi, Allah ya kiyaye"
Hanan tai maganar cikin tsiwa
"Baba nikuma na karbi kawancen nagode sosai daga yau tazama kawata"
Jalila tai maganar tana murmushi tare da kallon hanan
"Allah yayi miki Albarka Yar baba"
Abun ya daure musu kai yaushe mutumin nan yazo anguwar amma har yasan Jalila gaskiya a sojojin ma yana da matukar kirki, gaba daya kasa cewa komai sukayi

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now