ABDUL JALAL 88

384 24 4
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 3️⃣5️⃣88

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com




_MY FIRST NOVEL _

Mikewa Jalal yayi ze fice yabar dakin Amma Ilham ta mike ta sha gabansa

"Haba Jalal yanzu bazakaji magiyar
danake maka ba, dan Allah Jalal kayi hakuri, karkayi tafiyar nan, zan shiga mugun yanayi dan Allah Jalal, wallahi ina sonka, tunda kuruciya ta har kawo I yanzun"

"Ke waini sa'an wasankine? Wallahi koki matsa ko in tattaka ki"

Ya tureta gefe ya fice Abunsa, Abun duniya duk ya dami Ilham, Jawwad ne kadai ke iya sarrafa zuciyar Jalal wani lokacin, yanada matukar kafiya da taurin kai, gaba daya tunanin ta ya kwace.

Jalila takoma cikin gida ta tattara abubuwan dazata bukata dan gobe in Allah ya kaimu zata koma makaranta,
Karamar wayartace ta cika dakin da ringing, Jalila taga bakuwar lamba ta share tacigaba da Aikinta, amma still aka cigaba da kira har kusan karo uku, seda ta danyi tsaki sannan taja wayar tasa a kunnenta
Ajiyar zuciya akayi sannan akace

"Masha Allah, kin karyamin record bana kiran mutum sama da sau biyu, komai tsananin bukata ta kuwa, Amma ta dalilin son danake miki har sau hudu ina kiranki"

Sarai ta ganeshi amma ta maze tace
"ko zan iya sanin da wa nake magana?"

"Ohh am sorry dear, bankoyi miki sallama ba, balle mugaisai nafara miki surutu, Ahmad ne"

"Ok Allah sarki yakake ya gida ya iyali"?

"Alhamdilillah queen, kin tafi bako sallama, ban san zaki koma kano ba ai"

"Aikam abune na gaggawa ya tasomin, in ban manta ba ranar agabanka aka kirani"

"Hakane fatan kowa da komai lafiya"

"lafiya kalau, ya na baroku?"

"komai lafiya amma kintafi kin barni da kewarki, duk lokacin danake wani abu kona rufe idona ke nake gani Jalila, kitemaki zuciyar maraya"

ya karasa maganar cikin sigar magiya

Jalila tace "Kai karka bada maza mana, yanzu idan abokan Aikinka sukaji wannan aise suyi Maka dariya, babban soja kaman kai kana haka akan mace, macenma wata 'yar yarinya"

Murmushi yayi yace

"Jalila ai babu wani batun namiji ko soja in ana maganar fage irin na soyayya, ba ruwansa da matsayinka, girmanka ko mukaminka, ba ruwansa da na birni kona kauye, dan haka kidena wani batun maza"

"hmm Wannan bayani haka yakamata ka bude makaranta ka dinga bada darasin soyayya"
Murmushi yakumayi yace "Tunda haka kikeso ai se ayi, kece director mukuma dalibanki"
"Tab aini bansan komai a wannan harkar ba"
"Ahh haba dai?"
"dagaske nake fa"
"Aikam zan koyardake yadda yakamata"
"to shikenan seda safe, gobe in Allah ya kaimu zanje school"
"hakane hakan yayi kyau, Allah yabamu alkhairi, zamu hade a dreams zan biyoki har kano kan shinfidarki"
Murmushi Jalila tayi tace
"Allah yabamu Alkhairi"
Ta katse wayar ta danyi murmushi.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now