ABDUL JALAL 100

434 22 3
                                    

.🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                  *ABDUL JALAL*

             _Story, writing and edited _
                            
                            By
                  AISHA HUMAIRA
                  ( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

            PART 2        
                          _PAGE  4️⃣7️⃣100

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

     

             _MY FIRST NOVEL _

Shirye2 sunyi nisa sosai ana ta hada2, za'a shiga satin biki, Jawwad da Jalal sun kwana biyu a bauchi suka koma kano domin rabon invitation ga abokan Jawwad, Amma har suka tafi Jalila basu hadu da Jalal ba, duk inda amare suka shiga Jalila na biye dasu, tare sukaje gyaran kai, da kunshi na amare, hatta gyaran jiki da Jalila ake, se sheki take kamar itace Amaryar, in kaga yadda take zakewa kai kace itace amaryar, Ana gobe za'a fara bikin 'yan uwansu Jalal daga maiduguri suka zo (dangin su Mahmud) lokacin da suka zo su Jalila sun tafi gurin kunshi, tunda suka zo Antyn Jalal ke cigiyar Jalila, Amma aka sanar da ita sun tafi gurin kunshi, guri na mussaman aka tanadarwa dangin mijin Nana. Ana gobe a fara bikin su Jawwad suma suka dawo shida Jalal, duk inda zashi kafarsa kafar Jalal.

'yan uwa wanda sukazo daga wasu garuruwan, Inna ta dinga nuna musu Su Jalila Da Nana, tana gaya musu ga' ya'yan da jikokin kanwarta.

Yaya mairo kam da zuri'ar ta kaf babu  wanda yazo taron nan, sedai sauran 'yan uwa da abokan Arziki.

Se dare su Jalila suka dawo daga gurin kunshi, kallo daya zakayiwa fuskar amaren zaka gane yadda suke cikin farinciki, gashi sun dau kyau Masha Allah, suka tafi part din Anty fido a can suke kwana saboda estate din ya fara daukar harami da baki, kasancewar daddyn Hanan babban mutum ne asanshi sosai.

Hakama Abba yanada mutane sosai, ga dangin su Jalal, dan haka estate din cike yake da mutane.
Koda su Jalila sukayi sallar magariba, Hanan tace

"gaskiya sena kira Haidar yazo ya ga kunshin nan"

Jalila tace
"ke zumudin me kikeyi? Kwana nawa ya rage?"

"dan kwana nawa ya rage, se indena kula dashi? Se yaga kunshin nan, in yamasa ayi biki da shi, in yace be kyau ba a dirje shi a daren nan"
Gaba daya sukayi dariya, Nana tace

"ni dama muna gurin kunshi Mahmud yacemin; sunzo dazu suna tareda su Yaya Abdallah, ina son mu hadu da shi, inji ko yaci Abinci?"

Jalila kallonsu kawai take tana murmushi, tana mamakin ya sukeji a ransu game da soyayya haka? Ita dai tasan tana son Ahmad, Amma bata tunanin zata iya wannan rawar kafar akansa kamar yadda su Hanan sukeyi, ko lokacin da take son Yaya Jawwad bata tunanin zata iya abunda su Nana sukeyi, tana kallonsu suka canza kaya, sukayi waya da su Yaya Jawwad suka fice babban palourn part din.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now