ABDUL JALAL 97

345 18 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 4️⃣4️⃣97

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

_MY FIRST NOVEL _

Shiru Jalila tayi ta kalli kayan daya ajiye mata sannan tabi bayansa da kallo har ya fice daga gate, din shiru tayi ta tafi tunani, Ahmad yace

"my queen, meya farune?"
Da sauri ta dawo hayyacinta tace "bakomai fa"

"Amma waye wanan?" ya tambayeta yana me kureta da ido, ta dan sauke numfashi tace

"Yaya na ne"

"Yayanki queen, ba Jawwad ne kawai Yayanki ba?"

"Abokin Yaya Jawwad ne, dan haka Yayana ne kawai"

"Amma babu wani abu a tsakanin ku kuwa?"

"Meyasa kake min wannan tambayar? Ko baka yadda dani bane?"

"Ahh haba waneni ince ban yadda da gimbiyata ba, ina so ne in tabattar da abunda ke tsakaninku, dan da ganin idonsa yana shaye2"

Ba karamin haushi maganar Ahmad ta bata ba, kenan shima yanayi, in ba yanayi ba, ba abunda idon Jalal yayi dayake nuna yana shaye2, dan haka tace
"baya shan komai, kawai bashi da son magana ne, baya kula mutane"

Kyaleta Ahmad yayi yaga alamar bata son zancen suka cigaba da hira, Jawwad ne ya fito ze wuce su Jalila ya tsaya suka kuma gaisawa da Ahmad dayake dazu sun gaisa, Jawwad yace "to sirikina zan iya ce maka se anjima, ni zan tafi kai Jalal airport ne"

Da sauri Jalila tace "Ina zashi?"
Jawwad yayi murmushi yace "Aiki mana, an tura shi Lagos, se lokacin biki inaga ze dawo, bari inje karyai ta jirana, kin san baya son jira, se anjimanku" Sukayi sallama da Ahmad ya fita.

Ahmad ya maida idonsa kan Jalila yace "Gimbiya naso a haďa bikin nan hada namu, na kagu in mallakeki"
Murmushi kawai tayi amma hankalinta baya kansa, tanata zancen zuci ne, dayaga haka yace

"queen naga kaman Akwai abunda yake damunki, bari in tafi semunyi waya"
Ta mike ta rakashi har bakin gate sannan ta dawo ta zauna akan kujerun tana nazari

"At least yakamata ace sunyi sallama da Jalal, tayi masa nasiha, Amma bata tunanin zata iya kuma rabarsa ba saboda mahaifiyarsa.

Jawwad ya ga sam fuskar Jalal a daure take, babu alamar walwala ko fara'a, Jawwad yai masa magana yafi a kirga, amma ko daya be bashi amsa ba, dan haka ya kyleshi suka cigaba da tafiya a haka kaman kurame.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now