ABDUL JALAL (2020) 8

315 19 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 8

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Is a free book

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢
Your comments give me courage

I dedicated this page to you sister like no other
Saddika Adam (baby)
can't love u less
But stop asking silly questions if not zan hadaki da JALAL lolz

_My first novel_

Aimin afuwa
Today's page is
Not Edited

Gadan² yanufi inda Jalila take,
Kasa kwakwakwaran motsi Jalila tayi, ta kuramasa ido jira kawai take taga hukuncin daze mata
kawai se ya canza shawara ya koma ya fice daga palourn

Ajiyar zuciya Jalila tayi dataga be mata komai ba

Ilham ta kalli Jalila cike da bacin rai
"Waike Dan Allah meyasa kika fiye shishshigine ina ruwanki da shi wannan fa sabgar family ce meye naki a ciki 'Yar karere"?

Jalila ta kalleta tai maganar kasa²
"Hmm so hana ganin laifi"

Daddyn Jalal ne yayi gyaran murya yace
"A'a Ilham abinda yayanki yake baya kyautawa abinda takwararsa tafada gaskiyane se dai muyi masa fatan Allah ya shiryeshi"

Wani dam kirjin Ilham yayi takwararsa kuma?
Tai maganar a zuciyar ta

Jalila ta karasa cikin palourn ta durkusa har kasa ta gaishe da daddyn Jalal

Mummy kuwa tuni tabar palourn ranta yana daci game da abubuwan da Jalal yakeyi Sam baya ganin kimarta a matsayinsa na Dan da ta haifa

Fuskarsa a sake ya amsa mata gaisuwar
"Jiya ake gayamin baki da lafiya har an kaiki Asibiti, dazu mummyn su zata je dubaki da safe akace Baku dawo ba,
"Yanzu ya jikin naki"?

" ai naji sauki daddy "
Tayi maganar kanta a kasa

"To dama kiran kenan in miki sannu
Ya gurin mamanki ?"
"Tana nan lafiya"
"Masha Allah kin dawo nan ne gaba daya"?

"A'a zuwa nayi nakusa komawa"
"Allah sarki in kin tashi tafiya kizo muyi sallama kafin kitafi"

"To daddy nagode"
"Yawwa Allah yabaki lafiya"
"Ameen"
Ta amsa
"To daddy seda safe"

"Allah ya tashemu lafiya daddy nagode"
"Ameen Yar albarka
Allah yayi miki Albarka"
"Ameen ta mike ta nufi hanyar fita"

"Daddy dama kasanta ne?"
Ilham tafada tana ya mutsa fuska

"Nasanta Ilham amma tun tana Karama nasan mahaifinta kanin Alhaji Mahmud ne (baban su Jawwad) mutumin kirkine sosai"

Dan tabe baki kawai Ilham tayi

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now