ABDUL JALAL (2020) 46

356 24 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 46
PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske,
Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar
07063065680
Ina godiya matuka Allah yabar kauna

_My first novel_

Murmushi Jawwad yayi, "kasan ban zaci zaka zoba, na dauka dagaske bazaka zoba"
"nima na fada ne ai dan in tsokaneka, kuma kaji haushi"
"aikam dai naji haushin da farko amma yanzu na huce, ya me jiki?"
Jalal ya kalli Jalila, sannan ya kalli Jawwad "Nima bansaniba, yanzu aka fito da ita"
Jawwad yace "nayi mamaki da haryanzu bata farkaba,"
"hakane, amma zata tashi very soon, karkayi kuka, baban soyayya"
Murmushi Jawwad yayi tareda girgiza kai, "Jalal kafiye neman magana, nine baban soyayya ko?"
"eh mana nagani ne zakayi kuka"
Sukayi Murmushi gaba daya

Maama ta sha jinin jikinta yadda Abba ya rufe ido yake ta fada, yana da matukar hakuri, rabon da taga yana fada kaman haka harta manta, duk abunda zatayi masa yana dauke kai, amma yanzu ta inda ya shiga bata nan yake fita ba,
Duk yadda taso ya tsaya ya saurareta yaki, balle ta bashi hakuri, seda yayi mata wankin babban bargo sannan ya fice ya barmata palourn,
Yana fitowa palour yakira Nana, yace tazo suje asibiti, ko shi seya kwana da Jalila, tunda yayi waya da Jawwad yace masa anfito da ita kuma ana sa ran zata iya tashi a kowane lokaci, Nana ta fito suka tafi a Asibiti. Sukaje suka tarar da su Jalal, suka gaisa da Abba, Abba yaje kan Jalila ya tsaya yana mata addu a, ta rame kwarai, kuma har yanzu bata farkaba,
Abba yace "Jawwad ku koma gida, mu semu kwana anan, nida Nana"
Jalal yace " A a Abba, Jawwad da Nana dai su zauna kai ka koma gida, be kamata ace kai zakayi jinya ba bayan gasu"
Jawwad yace "hakane Abba kabar Nana anan ka koma gida kawai" haka suka lallaba Abba ya koma gida, bayan tafiyar Abba Jalal ma ya mike yace ze tafi,
Jawwad ya rakoshi waje, Jalal ya kalleshi sannan yace
"Jawwad meyasa mamanku bazatazo ta zauna da ita ba, be kamata ace Abba yazoba, har yana batun ze kwana a gurinta ba"
Jawwad yai ajiyar zuciya "Jalal kaima ka fada, Maama bata da wani dalili na kyamar baby, tunda ta kwanta batazo ko Asibitin nan bafa ina tsoron inyi magana ne"
"shikenan seda safenku, nina tafi"
"to Jalal nagode, Allah ya saukeka lafiya"
Jalal ya jinjina kai daga nan ya nufi motarsa, Jalal yana barin asibiti ya nufi club, dayaje be samu su Jeje ba dan haka shika dai ya sha giyarsa, seda dare ya raba sosai , sannan ya tafi gida,
Maama ta kira wayar yaya mairo ta sanar da ita abunda yafaru tsakaninta da Abba, da fadan da yaitayi, tsaki yaya mairo tayi
"to ba seyayitayi ba dalla ki rabu dashi, mezakije kimata, baiwarta ce ke, ai Allah be doramiki wahalar ta ba, in yagama fushin ma ze sakko"
"A a yaya mairo kinga kuwa yadda yaimin yau, yana ikrarin ze iya rabuwa da kowa akanta, haka kurum aurena ya mutu, gaskiya dai banda wannan shawarar, idan yasakeni ina na kama, baniba harku se mun shiga matsala"
"Kuma fa hakane, amma kurarine baze iya sakinkiba, to ki dai kula karki saki jiki sosai, suma su Jawwad din kisa ido akansu, dan bana son su fiye shige mata, in kin samu lokaci ki leka ki ganta ko yan mintuna ne, shima dan ki rufe bakinsa, amma baze iya sakinki ba"
Motsin dawowar Abba, Mama taji, dan haka tayiwa yaya mairo sallama ta tafi gurinsa, ta shiga dakinsa tana zaune Abba yaje yai wanka, yai salla yazo ya nemi guri ze kwanta,
" Abban Jawwad gurinka nazo"
Banza yayi mata ya nemi guri, ya kwanta,
"Dan Allah Abban Jawwad kayi hakuri"
"kinga tashi kibani guri bani da lokacin jin maganganunki, indai zaki guji Jalila nikika guda tunda jinin dan uwana ce, ki kyaleni"
"Dan Allah....
" Zainab fita kibani guri, koni in fita in baki guri"
Haka Maama ta fita ta bar dakin, lallai yayi fushi, abune mawuyaci kaga fushinsa, bashi da hayaniya sam amma wannan karon ransa ya gama baci.
Dare yayi Nana ta samu guri ta kwanta, Jawwad kuma ya zauna akan kujerar dakin a haka bacci ya daukesu, cikin dare Jalila tafara motsawa tana atishawa, da sauri Jawwad ya tashi yana kiran sunan ta, tana gama atishawar tacigaba da baccinta, ba tareda ta tashiba, tunda ga wannan farkawar da tayi, Jawwad be kuma komawa bacci ba har gari ya waye,
Da safe Abba ya shirya ba tareda ya kula Maama ba, a palour ya tarar da halima da hijjabinta, ta gaishe da Abba ya amsa, tace
"dan Allah sonake in bika inga jikin Jalila, tunda aka kaita Asibiti ban dubata ba"
Ta karashe maganar kaman zatayi kuka, Abba yace ta taho su tafi, da sauri Halima taje kitchen ta dakko, kayan tea data dafa ta bi Abba, Abba a ransa yace "Baby ko bayan raina, nasan bazata rasa mutanen kirki dazasu kula da itaba, kodan saboda kyawawan halayenta, Halima me aiki duk ta damu, hada dawainiya haka, amma matarsa dayake tareda ita yake kyautata mata da danginta amma takasa yimasa alfarma akan yar dan uwansa saboda wani dalilinta mara tushe"
Haka Halima ta shiga bayan motar suka tafi Asibiti, koda suka isa Asibitin, Halima taga Jalila da yadda ta rame seta fashe da kuka, Abba yace tayi shiru ta dinga yimata addu a, bayan Abba ya duba Jalila ya tafi gurin aikinsa,
Hawaye halima ta cigaba da sharewa,
Jawwad yace "Halima kidena kuka cikin dare tayi atishawa akwai yuwuwar, ta farka a kowane lokaci, daga yanzu, kidena kuka, kimata addu a" gyada kai Halima tayi sannan
Jawwad yace tunda ga Halima tazo, bari ya kai Nana gida tayi wanka taci Abinci, Nana ta tashi suka tafi, aka bar Halima a gurin Jalila,
halima ta mike ta koma kujerar gaban gadon Jalila, ta kifa kanta a gefen Jalila tana share hawaye,
"Allah yabaki lafiya, Jalila, Allah ya dubi maraicinki, ya baki lafiya"
Doctor salis da kansa ya shigo yayiwa Jalila allurai, ya samata wani ruwan, yauma tsayawa yayi yana karewa Jalila kallo, Halima ta dan kalleshi,
"Likita wai yaushe zata farkane? kwananta biyu a haka fa" doctor salis ya kalli Halima, "karki damu muna sa ran zata tashi ba dadewa,"
Halima tace "Allah yasa"
Daga haka doctor ya fita,
Yayi awa daya da tafiyar su Jawwad, Halima taji an turo kofar dakin, dan dago kai tayi ta waiwayo, da mamakinta taga Jalal ne, seda gabanta ya dan fadi, dan batayi zaton ganinsa ba, ran nan nasa a hade ba fara a, babu alamarta, mikewa halima tayi daga kan kujerar da take, ta koma gefe
Ta dan risina sannan tace "Ina kwana" be amsaba yace mata
"Ina Jawwad?"
"dazu suka koma gida, amma zasu dawo"
Gyada kai yayi ya jawo wata kujerar ya zauna ya harde kafa, yana karkadawa sekace wani basarake, ya zaro sigarinsa ya kunna, Halima ji tayi duk ta tsargu, ga mara lafiya a kwance amma taba yake sha, ji tayi duk ta takura, dan haka ta mike ta fita ta bar dakin,
Yana nan zaune yana shan tabarsa, yaga kafar Jalila tana motsawa, a hankali ta fara motsawa, tana kokarin bude idonta, a hankali ta cigaba da motsawa, ta bude idonta, dishi2 take gani kafin daga baya kuma ta bude idonta fes akan Jalal zaune kan kujera da taba a hannunsa, kallon dakin dake ciki tayi, tana kokarin gane mafarki takeyi kokuma a gaske ne, yunkurawa tayi zata tashi zaune amma taji cikinta ya kulle, ta kasa tashi, Jalal yana kallon ta amma be cemata uffan ba,
Yunkurawa tayi zata kuma tashi zaune, ga drip da yake shiga jikinta, tana nema tasa ya goce, Jalal ya kalleta,
"Malama kikoma ki kwanta, idan ruwan ya goce kuma fa, wayace ki tashi zaune daga farkawarki," ya fada a dan tsawace se yanzu Jalila ta tabbatar da ba mafarki take ba, tashi yayi yaje ya zare ruwan da ke shiga jikinta,
Yai waje, office din doctor salis yaje ya gaya masa Jalila ta tashi, da sauri salis ya Mike yana fadi" Alhamdilillah, gani nan zuwa " Jalal yakoma ya tarar Jalila ta lumshe ido, tanajin motsin Jalal ta dan bude ido tana kallonsa, ko ta kanta be kuma biba yasamu guri ya zauna, doctor salis ya shigo, yai sallama, ya kalli Jalila, ya kira sunanta a hankali ta bude ido ta kalleshi,
" sannu ya jikin naki" gyada masa kai kawai tayi, doctor salis yace
"Yanzu me yake miki ciwo" cikin muryar marasa lafiya, tareda shagwaba tace "Ni sonake in tashi in zauna, cikina kuma ciwo yakemin, nagaji da kwanciya amma nakasa tashi" ba karamin jin dadin muryarta doctor salis yaiba
"Ok zaki iya tashi zaunen"?
"A a nakasa tashin"
"Ok let me help you, sit up" ya kai hannu yana kokarin tabata, da sauri tace "A a nika kyaleni zan tashi da kaina"
"Bazaki iya tashiba, ki bari in temakamiki"
Yamutsa fuska tayi, "Nace maka ka kyaleni"
Jalal dake gefe yace "to ka kyaleta mana dolene, tunda tace bata so, base tayi ta kwanciyar ba,"
Kallon Jalal tayi ta dauke kai, salis yana jin tsoron Jalal, saboda yanada matukar kwarjini, dan haka yabar maganar temakamata ta tashi zaune, yace, "in Jawwad yazo, akwai magani daze siyo abata, amma a tabbatar taci abinci, dan zata bukaci abinci, asamu abu me dan ruwa2 abata ta sha,"
Jalal bece komai ba, doctor yai waje, Jalila trying ta kumayi ta tashi amma gefen cikinta a kulle, taji kamar an soka mata wani abu a cikinta zuwa zuciyarta, a hankali ta danyi kara, ta koma ta kwanta, kukanta ne ya karu yanzu hada sauti, da sheshsheka, takeyi, Jalal ya kalleta yai tsaki
"Malama kimin shiru kincikamin kunne,"
Banza tayi masa ta cigaba da kukanta
"Ni wallahi nagaji da wannan kwanciyar bayana ciwo yakemin"
Shiru Jalal yai mata, yacigaba da danna wayarsa, ita mamaki ma takeyi, me take a asibiti ita da Jalal ina yan gidansu, tanaga dai mafarki takeyi, kukanta tacigaba hawayene na bin gefen idonta,
tashi Jalal yayi ze fita, har yaje bakin kofa, ya dawo ya kalli Jalila yasa hannu ya dago Jalila daga kwanciyar da take, ya jinginar da ita, ji tayi gefen cikinta ya kara kullewa, saboda ba a hankali ya dagata ba
Ihu tayi ta rike hannunsa da karfi tana fadin
"Wayyo Allah cikina, ni cewa nayi ka dagani, saboda mugunta, bakasan me nakejiba, zaka dagoni a haka wayace ka tabani" ta fada tana hawaye, dan tsuramata ido yayi, ita dai bazata canzaba da kyar take magana, kai dakaji muryarta kasan tanajin jiki, amma bazatayi shiruba
"yimin shiru ko in maidake inda kika taso" dauke kanta tayi, kamshin turaren Jalal da warin sigarin dayakene Yasa Jalila taji tana yinkurin amai, dama gashi kwanakin nan cikinta ba komai, shi ya haddasa mata kullewar cikin,
Daga haka Jalal yai waje ya barta, Halima tana reception taga wucewar Jalal dan haka ta mike ta nufi dakin da Jalila take, tana zuwa ta tarar da Jalila a zaune, zare ido Halima tayi, ganin Jalila a zaune "Jalila kin tashi sannu"
Murmushi Jalila tayi, kafin tayi magana, Jawwad yai sallama, shima da mamaki yaga Jalila a zaune, da sauri ya karasa gaban gadon "Baby kin tashi sannu, ya jikin"
"Da sauki yaya Jawwad, ina kuka tafi kuka barni, anan ni kadai, waima me nakeyi anan"
"Bakida lafiya ne muka kawoki nan, yanzu me ke damunki"
"Cikina ne yakemin ciwo, da kirjina,"
"Ok Sannu bari inkira salis"
Halima tace "likitan yazo dazu yace abata abume ruwa2 ya mata allurai"
"Ok temakamata tayi brush, ina zuwa"
Jawwad na fita Jalila tace "Halima wai meyasameni ne, aka kawoni Asibiti"
"Bakida lafiyane kawai"
Halima ta dakko toothpaste da brush amma Jalila takasa sakkowa daga kan gadon, dan data motsa ko ina ciwo yake mata, bama ya cikinta,
Haka ta hakura, ta zauna akan gadon tayi brush tai alwala, ta kalli Halima
"Halima yaushe aka kawoni nakasa tuna komai, bansan sallan me zanyiba yanzu"
Dan shiru Halima tayi, dan bata san mezatace mata ba,
Jawwad ya shigo da leda a hannunsa, "sannu halima tayi brush dinne?"
"Eh tayi,"
Tea yasa halima ta hada, yazo gaban gadon Jalila ya zauna, yace "Baby karbi kisha se kisha magani"
Ta kalleshi "Yaya Jawwad salla zanyi, amma meyasameni aka kawoni asibiti"
"kinga kiyi hakuri, fara sha tukuna zamuyi magana"
Karba tayi ta dan sha kadan, yana shiga cikinta, taji ya murda ajiyewa tayi, idonta ya ciko da hawaye, zeyi magana wayarsa tafara ringing,
Yana dakko wayar yaga Abdallah ne yake kiransa
Dagawa yai yasaka a kunnensa tareda yin sallama, suka gaisa da Abdallah,
"Aliyu meyasamu wayan Jalilane? Hanan ta kirata tagaji bata shiga"
"Eyya batada lafiyane, kwananta biyu tana asibiti"
"Subhanallah me yasameta haka?" seda Jawwad ya kalli Jalila sannan yace
"ba ta jin dadine, amma taji sauki Alhamdilillah"
"Allah sarki, amata sannu dan Allah, zan gaya ma Hanan din insha Allah"
"to shikenan a gaida mutanen gidan"
Jawwad ya maida hankalinsa kan Jalila, hawaye ya gani shabe2 a fuskarta
"meya farune, Dan Allah baby kisha kinji"
"Yaya Jawwad ni na koshi, cikina ciwo yakemin"
Ana haka Jalal ya dawo, "Jawwad kana nan". "eh Jalal nakoma gida na maida Nana ne, sannu da zuwa dan uwa"
"Yawwa yanemi guri ya zauna"
Jawwad ya maida hankalinsa kan Jalila, suka cigaba da fafatawa da Jalila taki cin Abincin, Jawwad se wani lallabata yake tana wani shagwaba, taki cin Abincin balle ta sha maganin, Jalal ransa yabaci ya dan kalli Jawwad
"Namanta ban gaya maka ba, dazu kafin inshigo doctor Salis yace kaje, yana son ganinka"
"Ok bari ta ci Abincin se inje"
"No kaje kaji kowani abunne mana"
Jawwad ya mike " to Bari inje," ya juya ya kalli Jalila"baby dan Allah kisha tea din nan kinji, yanzu zan dawo" Jawwad ya juya ya fita, yana fita ya rage daga Jalila, Halima se Jalal,
Jalal ya kalli halima yace "hada wani tea din a katon cup" ba musu Halima ta hada, yasa hannu ya dauka ya mike ya nufo gadon Jalila, yana zuwa ya dire cup din a gefenta, ya hade rai
"dauki ki shanye"
Zunbura baki tayi "nina koshi, tayaya zan iya shan wannan uban shayin" tsawa ya dakamata "Ki dauka nace, se wani shirme kikeyi shikuma yana biye miki, inkin ki sha, wa kikayiwa inba kankiba, ki dauka ki shanye nace, kokuma wallahi in danneki se kinsha katon cup din nan biyu, danni ba Jawwad bane"
Kallon cup din tayi, ta kalleshi yanayin fuskarsa ya tabbatar mata he mean what he said, fuskarsa babu alamar annuri, Halima kam tana gefe tana kallon ikon Allah, hannunta na rawa ta dau cup din, tana fara sha seda taji kaman ana kuma nannade mata hanji, yamutsa fuska tayi, tana dan sha a hankali, shikuma ya kakkafeta da jajayen idanunsa duk ya takurata, dire kofin tayi "ni gaskiya na koshi"
Bece mata komai ba, ya cigaba da kallonta, itama kallonsa tayi, "to waini bana koshi ba" wani mugun kallo yacigaba dayi mata, ba shiri takuma daukan kofin tana sha tana haawaye ga wani amai dayake tasomata,
"Wallahi kikayimin amai sekinsha cup uku"
Da kyar da nishi Jalila ta shanye tea din nan tana zare ido tana kuka, seda ta shanye shi tas, sannan ya koma inda ya tashi ya zauna,
Jawwad ya dawo da magani a hannunsa, ya duba cup din tea yaga ba komai a ciki yace "Yawwa baby ashe kinsha saura magani kuma" shima maganin da kyar tasha, taji dadin jikinta sosai, har tasamu tafara rama sallolin da suke kanta
Jawwad ya kira Abba yagaya masa Jalila ta tashi, Abba yayi murna yace Insha Allah yana dawowa zezo ya dubata,
anci sa a Maama tazo ta dubata, bisa shawarar yaya mairo, amma ta tsorata dataga Jalila dan ba karamar rama tayi ba,
Jalila tace "Maama ina Nana"
"anan ta kwana, shiyasa yanzu nahanata zuwa, gara ta zauna ta huta" daga nan Jalila bata kuma cewa uffan ba, Mama batafi minti goma da zuwaba ta tafi abunta,
Bayan tafiyar Mama, Jalila ta kalli Halima tace "Halima wai kwana na nawa a asibitin nan ne? Ni dai nasan lafiya ta kalau"
"Kwananki biyu cif"
"Kwana biyu kuma"?
Jalila tayi shiru tana tunani kaman an tsinkuleta ta fashe da kuka ta kalli Jawwd
"Yaya Jawwad ina Ummi ba a ganta ba ko? Wai dama duk abun nan ba mafarki nakeba, Jawwad ina Ummi, ta mutu ko?"
Jawwad yace "A a Baby Ummi bata mutu ba har yanzu ana nemanta"
"Yaya Jawwad kacemin ta mutu kawai, shikenan nikam ita kadai taragemin dama, nasan ta mutu, haba Ummi, meyasa kika tafi kika barni, dan Allah Ummi ki dawo"
"Ke dalla kiyi mana shiru, daga farkawarki kina ma mutane kururuwa a asibiti, wayace miki mutuwa tayi,? Zaki dinga yimana ihu, kowa ba gatansa Allah ba"
"Ba ruwanka dani nayi kukan, ko dan kai bakasan darajar uwaba kake gani kowama haka ne agurinsa, dole inyi kuka, bansan halin da uwata ke cikiba, dakasan soyayyar da da uwa dabakamin tsawa ba, ita kadaice dani, ba uwa ba uba ba dangin uwa, " tana maganar tana hawaye numfashinta na fita da sauri
Jalal zuba mata ido yayi, wani abu na sukarsa a zuciyarsa, tabbas besan soyayyar tsakanin da da uwaba,
" Jalila meye haka, sa ankine shi, kike gaya masa haka"

Jawwad ya dakawa Jalila tsawa abunda be tabayiba

Share please
More comments more typing.............................

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now