ABDUL JALAL 96

395 21 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 4️⃣3️⃣96

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

_MY FIRST NOVEL _

Juyawa tayi ta fice da sauri tana goge hawaye, Ilham dataga duk abunda yafaru tayi wani tsallen farinciki, amma da tuna irin tonon sililin da Jalal yayi mata dazu se taji jikinta yayi sanyi ta juya da sauri ta koma gida.

Jalal bashida zabi da ya wuce ya bar gurin shima kamar wanda kwai ya fashewa a ciki yakoma part dinsa, zuciyarsa kaman an kunna masa wuta saboda bacin rai, side bed dinsa ya kalla yaga Alqur'anin nan da kuma teddyn Jalila a gurin, a hankali yace

"do she really mean what she said, zata barni gaba daya, bani ba ita? Jalila why? karkimin haka mana, nasan ba'a kyauta miki ba, Amma kar laifin Mummy ya shafeni"

ya zauna a gefen gadon sa ya rintse ido, ya dinga tuno moments dinsu tare, da fitar da sukayi dazu, ji yayi kansa yana juyawa zuciyarsa ta masa nauyi, ya kunna sigari yafara sha, ya sha takai kara biyar amma beji yadda yakeso ba seda ya dakko merlot red wine ya sha ya fita daga hayyacinsa sannan ya yada kwalbar a gurin shima ya zube.

Ita kuwa Jalila seda ta samu guri a cikin flowers tayi kukanta ta gode Allah sannan ta nufi palourn gidan, tunda ta shiga ita dai taji Abba yana bayani yayinda Yaya mairo keta haya gaga, sam Jalila bata gane me suke fada danji take kaman zata fadi ta wucesu ta shige daki ba tareda ta kula kowa ba, tana zuwa ta haye gado ta ja blanket ta cigaba da kuka da kuma tunani, shikenan yanzu kuma kallon mazinaciya mahaifiyar Jalal take mata? Gaskiya tsakanin ta da Ilham se Allah yasaka mata, amma ba komai zata rama ne, zatayi wa Ilham daurin da bata isa ta kwance ba"

Jawwad ya farka daga baccin dayake cike da farinciki ya tashi yayi salla, sannan ya nufi cikin gida dan ganin Maama dakuma 'yan kannensa dan yasan zuwa yanzu sun dawo daga school.

Yana fitowa manu direba ya shigo harabar gidan da mota, ya jira manu yayi parking Nana ta fito daga motar kallo daya zakayi mata kasan a gajiye take, se jefa kafa take kawai tana ganin Yaya Jawwad ta yalwata murmushinta tareda fadin

"Oyoyo mutan Bauchi, Ashe kun dawo?"

"Mun dawo Nana, ya school din?

Naganki ke kadai ina Jalila?"
"Yaya Jawwad kasan Jalila manyan kwarine, yau bataje school ba, amma ancemin angan ta dazu ta shiga zasuyi test"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now