ABDUL JALAL (2020) 19

284 18 0
                                    

.🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 19

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢
Your comments give me courage


-My First Novel-

Malamai ne suka jeru suna shirin janyowa Jalila inda zata karanta
Itakam tayi shiru ta kurawa camera ido haka nan taji gabanta na faduwa dukda tasaba zuwa musabuka amma takejinta wani iri

Jalal ne ya kurawa TV ido gani yake kaman shi Jalila take kallo so yake ya tabbatar itace kuwa a jikin allon TV kokuwa kamrun dayasha ce tafara gaya masa karya(giya)
Ita kam Ilham kara shige masa take tana kuma zuba masa Wayne tana mika masa
"Ilham ki kyaleni please"
"Yaya J why?"

Tayi maganar tana kuma kwanciya a jikinsa
Shikam yakoma kaman wani karamin yaro
"Bana so Ilham ki kyaleni kwanciya zanyi kaina ciwo yake"
Dan dagashi tayi ya koma ya kwanta akan kujerar yana kallon TV kasa²
A hankali Ilaham ta mika hannunta tana shafa sajensa
"Sannu Yaya J"
Gyada mata kai yayi

"Ilham karki kuma saka turaren nan inzakizo inda nake banaso"
Yai maganar a hankali
"To na dena"
Tv ya kuma kalla Jalilan ce dai sedai wannan karon annurin fuskarta ya gushe ta dai²ta nutsuwarta aka janyomata inda zata biya
A hankali tayi bismillah tafara karanto Qur'ani cikin sauti me dadi
Ture Ilham yayi daga Jikinsa ya lumshe idonsa jin sautin karatun nata yake yana ratsa ko ina na jikinsa yana saukar masa da nutsuwa Ji yayi kasalar tana sakinsa duk yayinda ya bude Ido seyaga kaman Jalila shi take kallo jinsa yake kaman ba Shiva
Ilham hannu ta kuma mikawa zata taba shi ya daka mata tsawa
"Ke wace irin banzar yarinya ce waima tukuna me kikemin anan gurin ne tashi kibar min daki kafin in zaneki banza kawai"
"Haba Yaya amma
" bazaki fitan ba kenan kalli Tv duk rawar kanta kalli yadda take karatun Qur'ani gwanin burgewa keko sha³ baki iya komaiba se hauka get out from my room"
Idonta ta kai duba kan Tv Jalila tagani tana zuba kira'a kaman ba itace me shegen surutu da Neman magana ba, wani abu taji yazo ya tokaremata zuciya wato tun dazu da ya kurawa Tv ido ita yake kallo kenan
Wani mugun kallo taimasa
"To ai gara ni inazuwa Islamiyyar kai...........
Bata rufe bakiba yasaka kafafuwansa ya take nata kafar wani irin ihu tayi da karfi kuma yaki dagawa
" Dan girman Allah kayi hakuri, wallahi bazan kuma ba"
Kara takesu yayi
"Dan ina daga miki kafa ina nan a Jalal dina da kikasani, yanzuma Sa a kikaci da wallahi sena zaneki da belt, tashi kifita wawiya kalli rigar jikinki sokuwa kawai"
Da kyar taja kafa ta fita kafarta se zugi takeyi ta koma dakinta ta hau gado ta kama kuka
Wani uban tsaki ya ja yanemi guri ya zauna
Tashar da suke haska musabakar su Jalika sun tafi talla dan haka
ya dauki cup din giyarsa ya cigaba da sha yakuma zubawa ze sha aka kuma hasko Jalila haka nan se ya aje giyar hannunsa shima ya kuramata ido, yanayin Jalila ne ya nuna kaman bata da nutsuwa
Aka kuma janyomata karatu amma tayi shiru ta tafi tunani kowa ita yake kallo
Jikinta ne yayi sanyi jitake kaman wani abune ke shirin faruwa, mafarkanta datakeyi yan kwanakin nan ne suke fado mata a rai taji gabanta yacigaba da faduwa.
a hankali tayi ajiyar zuciya ta Dora inda aka janyomata da karatun ta cikin birgewa

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now