ABDUL JALAL 109

1K 30 4
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣5️⃣108

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

_MY FIRST NOVEL _


Jalila kaman zatayi kuka tace

"please Jalal, kome sukayi maka kayi hakuri kasa a kyalesu, karka karamin bakin jini a gurin mutane.

Jalal yayi kasa da muryarsa sosai ya kai bakinsa kunenta yace

"ko kowa ya ki ki, ni ina tareda ke kuma ina sonki, duk me kinki Bashi da gaskiya, duk wanda yake adawa dake wanda baya son cigaba nane, kinyi yaki da mutane da dama saboda ni, ina sonki Jalila,"

Gaba daya jikinta yayi sanyi taji tsigar jikinta na tashi, a hankali tace" Amma Jalal.....

"karki kuma yimin magana akan su, akwai dalilin da yasani yin hakan, karki damu kinji my wife"


Yaya mairo ta kira wayar su Naja babu adadi amma sunki dagawa, sun saba da gantalinsu bata damuwa amma haka nan taji yau takasa nutsuwa, har maghariba bata gansu, se wajen Isha'i Naja ta dawo a wahalce, ko Abinci bata ci ba ga yunwa da kishirwa.

Yaya mairo tace

"ke lafiya kuwa? Ina sa'adah take?"

Naja tace

"ina fa lafiya, sa'adah ta jamu gidan wannan Yarinyar mijinta yasa aka kamamu, wai ko seta fadi inda wata take, nima da kyar yayi waya aka sakeni"

Yaya mairo tace

"ke kimin bayani wai ina kukaje akayi muku hakan? Bangane me kike nufi ba"
A fusace Naja tace "Wai meyasa ba kya ganewa ne, nace miki gidan Jalal ta ja mu, yasa 'yan sanda suka kamamu, ni sun sakeni ita tana can"

"A' ahh to me kukayi masa? Wani station dinne?"

"dan Allah ki barni in huta, Allah kadai yasan azabar dana sha ta yunwa amma kin uzzuramun da tambayoyi, niki kyaleni da banyi niyyar zuwa gidan nan ba amma ta jani ta janyomin masifa"

Hankalin yaya mairo ya tashi sosai, gashi Naja taki ta tsaya tayi mata bayani yadda yakamata .

Jalila ta kira Hanan suna ta waya tace

"gaskiya Hanan kina wahalar da bawan Allah, yau kice wannan gobe wancan haka akeyi"

Hanan tace

"Jalila duk yadda zan Gaya miki bazaki gane ba seyazo kanki tukuna"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum