ABDUL JALAL 107

1.1K 24 5
                                    

.. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣4️⃣107

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

_MY FIRST NOVEL _

Jalal be san inda kansa yake ba, dan a buge yake sosai ga jikinsa yayi zafi, sakkowa tayi daga kan gadon ta debo ruwa da towel, ta dinga shafa masa a hankali ya dinga sauke numfashi, ta tattare kwalaben giyar da yasha, da sauran sigarin da yabari ta fita dasu, ta dawo ta dauki bargo ta rufeshi, sannan ta kashe fitlar dakin ta fita.

Koda ta koma dakinta bacci kauracewa idonta yayi, dan haka ta dauro Alwala tazo ta tayar da salla, taita nafilfili tana kai kukanta ga Allah tare da yiwa Jalal fatan shiriya, ta dade tana Addu'a sannan ta shafa, ta dauki Al'qur'ani ta koma kan gadon dan ta karanta, ta ciro qur'anin daga cover, se cover din ya fadi kasa da sauri tace "bismillah" ta mika hannu ta dakko, dan abun da'aka shimfida a kasan cover ne taga ya Dan daga, kokarin gyarawa tayi amma taji kaman da tudun abu a kasan, nan tatattara hankalinta gurin gano menene a gurin, a hankali ta gano wata 'yar takadda a gurin, a hankali taita kokari harta janyo takaddar, tana mamakin takaddar mene wannan?
A hankali ta warware takarda tareda kosawa taga meye a jiki, tana budewa taci karo da kyakykyawan handwriting din mijinta wato ABDUL JALAL, mamaki ne yakamata, tafara karanta abunda ke jiki.

Am so happy my flower is growing, dukda na dade ban ganki ba, kuma banji dadin yadda wannan haduwar ta mu ta kasance ba, nayi farincikin ganinki Baby, kiyi hakuri da halin da nakeyi banji dadin yadda kika sameni a wannan halin ba, Amma ga Alqu'arni da nafi so, tunda bana iya karantawa, idan kin karanta kidinga min Addu'a, i need your prayers, kidena min shouting please bana so, it touches my heart when ever you shouted at me, my regards to Ummi
I love you my heart ♥
ABDUL JALAL

Se signing din Jalal da date din daya rubuta, gaba daya Jalila jikinta yayi sanyi, dama wannan ce ajiyar da yake tambayarta, to ai lokacin da yayi rubutun ma lokacin da ta fara zuwa kano da wayonta lokacin tana kwailarta se rashin kunya, kenan tun lokacin yake sonta kokuma yaya?
Jalila ta juya takar dan nan ta karanta tata yafi sau Ashirin.
Tuno abubuwan da ta dinga yimasa tayi, tabbas ta masa maganganu na bata rai, Amma sedai yaita mata warning, ko kuma barazanar ze mata wani abun,
Indai tun a wancan lokacin yake sona ya akayi ban saniba? A lokacin ma bata da wani abu daza'a sota danshi, sedai kyan fuskarta amma a lokacin tana kwaila.
Tunani ta dingayi reaction din Jalal duk lokacin daya ga tana kuka, kokuma ranta a bace, yadda yake kasa boye damuwarsa in ya ganta a haka.
Meyasa be gayamin yana sona ba tun wancan lokacin?
"kina masa wulakancin da rashin kunya ta ya ze Gaya miki?" wata zuciyar ta gaya mata.
"amma banga alamar Jalal yana sona a wancan lokacin ba, ko ganina fa baya son yi"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now