ABDUL JALAL (2020) 15

282 21 0
                                    

_ABDUL  JALAL_
           (2020)

      _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
    (Daddy's girl)

               PAGE-  15

PART 1

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢
Your comments give me courage

Aimin afuwa the page is not edited
         -my first Novel-

Ni bazan iyaba wallahi, idan suka kashe nifa, niba abunda zan iya yatafi ina ruwana

"Ke Jalila wai meye hakane
Ba magana nake miki ba"
Tashi Ummi tayi taje ta jijjigata a firgice ta tashi tana rarraba ido
"Wai meyake damunki a yan kwanakin nan kusan kullum sekin tayar min da hankali in dare yayi ko dai gamo kikayi da Aljanu"?

"Niba wasu aljanu kawai tsorata nake"
Jalila tafada tana ya mutsa fuska

"Au tsoratanne kawai, to tunda kawai ne kika kuma min kuka a cikin bacci bulala zan saka in zaneki ta shi kije kiyo alwala kiyi salla ki dau Qurani ki karanta Allah yasa kina Azkar"
"Ummi bana salla"
"To jekiyo Alwala kibiya Wanda kika haddace"
Ba musu taje tayo alwala tazo taita bitar Qurani da ka bacci kam gagararta yayi se dai juye²

  Yauma kamar kullum haka ta tashi jikinta kaman Mara lafiya ko abincin kirki takasa ci ga idonta daya kumbura saboda rashin bacci Ummi kallonta kawai take dakinta ta koma ta nemi guri ta kwanta tayi shiru

(Karki bari Jalal yayi tafiyar nan in har yayi tafiyar nan rayuwarsa zata lalace fiye da da burinsu ze cika, Wanda abun ze iya shafar rayuwar Jawwad , ze lalace fiye da baya kiyi wani abu a kai Jalila kar ki bari Jalal ya tafi!!!)
Tas kalaman da akayi mata a mafarki suke dawo mata kwakwalwarta Wanda yayi dai² da wani mugun bugawa da zuciyarta tayi da karfi, kanta ya Sara
"Nashiga uku ni Jalila wannan wani irin bala'i ne meye hadina da wannan mutumin ake tsoratani akanshi wani tsautsayin ne ya kaini kano wanannan wani irin jarabane ana nema a haukatani why?"
Tafada tareda yin jifa da pillows din kan katifar ta yage bedsheet din kan gadon ta kifa kanta akan katifar

"Dan Allah ji abinda nake kamar mahaukaciya Ta Yaya zan hanashi tafiya ina nan yana can how? Be duba amincinsu da Yaya Jawwad yafasa tafiyar ba se ni da bama shiri to ni ya zanyi?
Kawai shirmen mafarkine kimanta kicigaba da harkokinki
Wani bangare na zuciyarta ya gayamata,
aikam ta yadda da abinda zuciyarta ta gayamata na ta manta shirmen mafarkine
Ga bacci a idonta kanta har ciwo yake amma bazata iya ba saboda fargabar inta kwanta me zata gani
Duk yadda taso ta manta takasa zuciyarta se bugawa take da sauri² hankalinta yaki kwanciya
" Nashiga uku ni Jalila meke shirin faruwa dani haka ya zanyine?
Ko ingaya Ummi me
Karki kuskura hakan be dace ba mussaman intaji abinda yayi miki bazataji dadi ba, wani sashi na zuciyarta ya gargadeta

Siyama ce ta faɗo mata a rai, dan haka da sauri ta mike taje ta wanke fuskarta tasaka hijjabi ta fito, ta tarar da Ummi tana saka a dakinta
"Ummi inaso zanje gurin siyama"
"Adawo lafiya kigaidamin da ummanta saura ki dade inkika dade kin kori gaba kinsan halina"
Gyada kai Jalila tayi ta fita ta nufi hanyar gidansu siyama

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now