ABDUL JALAL 94

371 22 7
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*ABDUL JALAL*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


_*Story, &writing*_

_and edited_

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*P.W.A*✍️

PART 2️⃣
_PAGE 4️⃣1️⃣94

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

_MY FIRST NOVEL _

Jalila ta bugu sosai, ta rike hannunta tana rintse ido saboda azabar zafi, shikam yasa kai ya fice yabar dakin.
Ta dade a gurin a zaune, sannan ta mike ta koma cikin gida tana yamutsa fuska.

Su Jawwad kam har la'asar sannan suka isa Bauchi, Abba yakira daddyn Hanan a waya yagaya masa sun karaso, aka turo wasu sojoji sukazo suka tafi dasu har estate din, Ba Jawwad ba har Abba seda yayi mamaki irin tsaruwar da estate din yayi sekace barrack duk inda ka juya sojoji ke shawagi a ciki, akai musu Jagora zuwa gidan daya kasance nan ne center.

A dankareren dakin Daddy akayi musu iso, da murna daddyn Hanan ya tarbi su Abba, suka gaisa yai musu barka da zuwa, seda suka fara gabatar da salla sannan daddy yai umarnin akawo musu Abinci.

Wasu matasan 'yan matane dabasu wuce sa' anin su Hanan ba su uku suka kawo Abincin suka ajiye, tareda gaida Abba da Jawwad, ďaya daga cikinsu wadda da gani kasan hutu da jin dadi ya ratsata tace

"daddy wannan yana matukar kama da Yaya Yusuf, ko shine sirikin naka?" Jawwad ya sunkuyar da kai saboda kunya
Daddy yace
"kaniyarki yusra, sarkin surutu, tunda kunkawo Abincin kukoma, ki gayawa Inna bakin sun iso zasu shigo anjima su gaisheta"
Murmushi Yusra tayi tace

"Yadda kace haka za'ayi daddy"
Abba yace "General wannan ma 'yar wajenka ce?, tana kama da Hanan"

"' yar wana ce, gaba dayansu yaran 'yan uwanane, Aini Hanan da Abdallah kadai Allah yabani, sekuma diyata Autar mata Jalila, Zuma kenan ga zaki ga harbi"

Gaba daya sukayi dariya, daddy yace su ci Abinci, Amma gaba daya Jawwad yakasa sakewa yaci Abincin nan saboda kunya "Sekace wani mace🙄, (ya kuke gani in goga Jalal ne? 😂 yaseen cin abunsa zeyi)
"
Daddy yace "Jawwad baka cin Abincin nan fa, nifa banason fulatanci, ka saki jiki kaci Abinci"
Jawwad murmushi kawai yayi yakuma sunkuyar da kai.

Bayan sun kammala, Abba ya gyara zama sannan yace

"to Captain ni dai da farko Jawwad be gayamin yana soyayya da Hanan ba, har nayi masa zabin matar Aure nida mahaifiyarsa, Amma yanzu nagane akwai matsala a dangane da zabin da mukayi masa, kuma Kanwarsa Jalila da Dan uwansa suka sanar dani halin da'ake ciki har kaima ka kirani a waya kazomin da wannan zance na Jawwad ya fito in dagaske yake"
Daddy yace "Hakane, nima mahaifiyar Hanan dince ta sanar dani halin da'ake ciki, kuma gaskiya yarinyar tanada manema dayawa kuma ta nuna shi Jawwad din takeso, shiyasa nima nayi maka magana"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now