ABDUL JALAL 81

348 21 1
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

              _ABDUL JALAL (2020)_

       _Story and written by_
      AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
        
   PART 2        
                          _PAGE  2️⃣8⃣81

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

     
          
         

   
          _MY FIRST NOVEL _

Gaba daya sukayi shiru suna sauraranta, tareda kallon mamaki, ta cigaba da cewa
"Sannan kuma zan tabattar maka da zarginka Nice  nasaka aka dauke Jalal ranar birthday dinsa" ta juya ta kalli Suleiman tace
"Yallabai gashi nan, ku tambayeshi"
Suleiman ya janyo kujera gaban gadon Jeje ya zauna, ya kalli Jeje yace

"Ya jikin naka dan uwa?" da kyar Jeje ya motsa baki yace
"Da sauki"
suleiman ya gyara zama yace

"Inbazaka damu ba, zamuyi maka tambayoyine gaskiya muke bukatar ka gayamana in kayi karya, zamu daukeka a haka mutafi da kai office ka warke a can, mecece Alakarka da mutumin daya yi maka wannan raunukan?"

Jeje yace "Ubangida nane, ni yaronsa ne"

"Ubangidanka kamar yaya? Aikin me kake masa, A ina kuka hadu? Yaushe kafara masa Aiki?" Jeje ya juya ya kalli Jalal ya sunkuyar da kai kasa, a fusace Suleiman yace
"magana fa nakeyi maka, kabani Amsa kuma in kayimin karya seka gane kuskuren ka" Jeje ya juya ya kalli Jalal yace

"Jalal ina fatan zakamin Afuwa jin abunda ze fito daga bakina, Asalina nidan garin Azare ne, a cikin wani kauye, mahifina ya dakkoni yakawoni Almajiranci lokacin inada kananun shekaru dabasu fi takwas ba, tunda aka kawoni bawanda yakuma zuwa inda nake, balle susan halin danake ciki, sedana shekara goma shahudu sannan naje gida, koda naje gida mahaifiyata ta rasu, nayi bakin ciki me tarin yawa nadawo kano, Rayuwar Almajiranci Rayuwace me matukar matsi da wahala, ba kula ba Abinci sabulun wanka wanki, balle magani komai kai zakayiwa kanka Rayuwa tayimin Zafi nafara shiga kasuwa domin neman na kaina, na gudu daga makaranta a haka na shiga makarantar boko, a kasuwar nan nasamu aiki a gidan karuwai nake musu aiki, a haka nakoyi shaye2, neman mata tunda kananun shekaruna, Jagaliya da bangar siyasa ba wadda ba'adamawa dani, mun hadu da Alhaji Kabiru a gurin campaign din wani ubangidansa, ninake jagorantar group din jagaliya da 'yan daba, Alhaji Kabiru ya gayyaceni gidansa da zummar yanaso inmasa wani Aiki zena biyana, na yadda na Amince, ya nunamin hoton Jalal yace akansa yakeso inmasa Aiki, nace kamar yaya, yace soyake Jalal yazama mugun dan shaye2 dan Jagaliya kamar ni, nace masa amma tayaya hakan ze faru yacemin inyi duk yadda zanyi zena biyana duk wata dubu Ashirin, idan har burinsa yacika Jalal ya lalace ze bani wasu kudi masu yawa, Na amince na karbi Adress din Jalal nafara zuwa unguwar su, na lura yanada saukin Kai dayawan kyauta, dukda na girmeshi haka na dinga kokari ina shiga jikinsa, ina turamasa Akidar shaye2, dabe amince ba har sabani muka samu, amma daga baya bansan ya akayi ba ya Amince da kansa, Abokinsa Jawwad yayi kokari yaga ya rabamu amma abu yaki, haka nakoya masa zuwa clubs daban2 kasancewar yanada kudi kayan maye se wanda mukeso zamu sha, Nayi kokarin in koyamasa bin mata amma yaki, sam hankalinsa baya kan wannan shidai kawai yayi shaye2 Alhaji Kabiru yacigaba da biyana makudan kudade kafin daga baya ya nunamin sana'ar da yake yi ta saida miyagun kwayoyi da makamai ta barauniyar Hanya, idan Jarinsa yai kasa senazo nasan yadda nayi na karbo masa kudi masu yawa a gurin Jalal seya raba yabani kasona, nazama babban Aminin Jalal, Alhaji Kabiru yasa nadinga Jan ra'ayin Jalal akan mutafi Dubai semunfi holewa acan bame samana ido, mussaman shi da mahaifiyarsa take takuramasa aikuwa ya yadda, shikuma Alhaji Kabiru yahada baki da wasu ma'aikata za'asaka kwayoyi a kayan Jalal, yadda semunje dubai za'a kamashi, idan mukaje dubai aka kamashi da wannan kayan hukuncin kisa ne, Amma abun mamaki se a Airport Jalal yace yafasa tafiyar nan, Saboda Jawwad.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now