ABDUL JALAL (2020)

576 30 2
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 2
PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

_My first novel_

Kallonta Nana tayi, ta ce
"kaman ya se kin rabasu, ina ruwanki dasu? kinga Jalila ba ruwanki dasu, Maaama ma tayi ta Hakura, Jalal ba ze iya rabuwa da Jawwad ba, bayan abokansa na banza ina ga Yaya Jawwad ne kawai mutumin kirki, kika sani ko Allah ya shiryeshi a sanadin sa? kawai muyi musu addu' a."

Ajiyar zuciya Jalila tayi ta ce "Nana abotar Yaya Jalal da Ya Jawad sam bata dace ba,
barazana ne ga tarbiya da rayuwar Yaya Jalal mutumin dabe ji maganar Wanda suka kawoshi duniyaba ne kike zaton ze wani shiryu sanadin wan?i yau da gobe se Allah yasha giya ya kwana club yayi sa'insa da mahaifiyarsa shi kike tunanin ze shiryu sabodaa wani aboki Sam bashi da tarbiyya Nana ."

Jalila Allah shi yasan manufar hada abotarsu duk da banbancin halayensu, kawai muyi musu addua shine mafita mukuma muyi abinda ke gabanmu."

"Nana ni kam nacji amma ban gamsu da bayanan ki ba , zanyiwa Yaya Jawwad magana,"

" to Allah yatemaka inji Nana, amma kome zakiyi karki shiga harkar Jalal."

Ajiyar zuciya Jalila tayi ta ce "karki wani damu Yar uwata, ni dai fatana yafita shirgin yayana, bana so yazama irinsa ya lalatamin Dan uwana,
tunda shi lalataccene ma tayashi da addu a."

"To Allah ya baki Sa' a, nima da naso hakan".

********************************

Sanye yake da kananan kaya, wando 3quater fari da Riga T-shirt itama fara, yayi kyau sosai, yasa hannu ya dauki turare ya feshe jikinsa dashi, ya dauki wayoyinsa dake kan mudubi da mukullin motarsa yafito.
Kai tsaye ya nufin inda akayi parking motoci, sekuma ya juya ya nufi cikin gidan.

yanazuwa kofar parlour ya budee ya Shiga, ba sallama ba komai fuskanan tashi a daure tam babu alamar fara'a
parlour shiru se kamshin turaren wuta dana abinci da ya gauraye parlourn, gefe kuma Ilham ke kwance kan kujera 3seater tana kallon Tv.

"keee!!"
ya fada cike da gadara ,
a dan tsorace ta dago Dan batasan ya shigo ba, "Yaya Jal sannu da zuwa"

Ta fada tana kallon sa tare da yaba kyawun da yayi acikin ranta, be amsa ba yace

" Ina matar gidan nan take?"

"matar gidan nan kuma?"
ta maimaita tana dubansa
"ba kiji bane ko kuma tsabar rainin hankaline?"

Adan daburce ta ce "ai jinai kace matar gidan nan, wai mummy kake nufi?"

" Yaushe raini ya shiga tsakanina dake ne? har nake magana kina maimaitawa, akwai wata mata a gidan nan banda itane?"
Mamakinta ne yakasa boyuwa, lallai yaya Jalal abin nasa ya girmama, mummyn tasa ma bata tsiraba wai matar gidan nan? tabdijan, amma ta dake ta boye mamakinta ta bashi amsa da
"ta fitane, taje saloon"
"mtseww" ya Dan jaa tsaki , "inta dawo ki ce ta kirani a waya, ina da magana da ita."

Bai jira mezatace ba yasa kai yafita,
"ohh God ni Ilham, yaushe Yaya Jalal ze fara sakarmin fuska ne yana kulani? kullum mutum fuska a daure Yaya Jalal whyyyy?? "

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now