ABDUL JALAL 67

321 22 1
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 1️⃣4️⃣66_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com


_MY FIRST NOVEL _

Koda Saleema ta dago tai ido hudu da mahaifinta a gigice ta mike daga cinyar wanda take zaune, tana zazzare ido, gaba daya sukayi cirko2 suna kallonsa. koda ya duba yaga waye Saleema take kan cinyarsa ba kowabane illa Jeje, a gigice Alhaji Kabir yace

"Saleema abunda kike aikatawa kenan, kin cuceni kin cuci kanki Allah ya isa tsakanina da ke" ya maida idonsa kan Jeje yace
"nizaka ciwa amana, karasa da wadda zakayi lalata se yar cikina, duk halaccin danayi maka a rayuwa wallahi seka ga karshenka sekaga abunda zanyi maka, sena dau mummunan mataki akanka"

Jeje rasa mezece yayi gaba daya ya rude, daga gefe wani tsageran matashi yace

"wai dan Allah meyakawo ka nan gurin, kake wannan maganganun ne? nina dauka harka kazo, kaima fa ana kaimaka matan nan guest house dinka to meye dan anyiwa yarka? abunda kakewa yayan wasu nefa"

seda Alhaji Kabiru ya duba sosai sannan ya gane matashin, tabass suna kaimasa karuwai yana biyansu kudi. A fusace Alhaji Kabiru ya dau wata kwalba ya nufi inda matashin yake, Saleema se kuka takeyi, jin ance itama ga abunda mahaifinta yakeyi. yana zuwa ya bugawa matashin a ka, sauran matasan sukayo kansa, duk wanda yazo seya kaimasa suka da fashashiyar kwalba.
Itako Jalila koda taga Alhaji Kabiru ya shiga cikin gidan nan ta kuma kiran yan jarida, tana gama wayar sega motar

"yan hisba, tareda yan sanda, sukayiwa gidan dirar mikiya, suka kewaye shi, sannan wasu suka shiga cikin gidan, babban abun kunya da asara shine kama uba da 'ya a gidan karuwai, nan aka tarkata kansu tsaf, Alhaji Kabiru se rantse2 yake, ga wadanda yajiwa ciwo da kwalba, Saleema banda aikin kuka ba abunda takeyi, kan Jeje se zubarda jini yakeyi,'yan sanda suka caje gidan inda akasamu miyagun kwayoyi, da kayan shaye2 kala2, kafin a tafi dasu yan jarida suma suka karaso, suka rufawa motar yansanda baya dan zuwa daukar rahoto, ba karamin farinciki Jalila tayiba, rasa inda zatasa kanta tayi dan murna, batasan lokacin dataji hawaye farinciki nabin fuskarta ba "Allah kai kabani wannan dama, Allah kaikabani nasara ba dabarata da wayona ba, Allah nagode maka, nagode da ni'imarka da kariyarka, Allah kasa sanadiyar shiryuwar bawanka ce tazo" hanyar titi ta nufo tana sauri, yamma tayi sosai, ta tafi gida gida cike da murna da farinciki.

Takoma gida tanata murna, tana zuwa ta tarar da sa'ada tazo itada Naja wai a gidan zasu kwana biyu, Jalila ko takansu bata biba, murnarta kawai takeyi,
Nana tace "Baby meye sirrin wannan fara'ar da murmushinne haka?"
"Nana nima ban saniba ina murna ne kawai"

"Hmm kyama fadi gaskiya" "gaskiyar kenan Nana"
sukayi dariya gaba daya. Kan kace me Labari yafara yada duniya cewar an kai sumame gidan karuwai, inda aka kamo hada wani uba da 'yarsa tareda yaronsa a gidan" nan da nan zance yafara zaga social media, da sauran kafafan watsa labarai, inda ake ta tir da Allah wadaran akan Alhaji Kabiru.
Nana takira Jalila a waya "Jalila Allah yasaki a Aljannah, kinceci rayuwata da sauran rayukan dasu Saleema sukaso lalatawa, Allah yabiyaki da mafificin Alkhairi, Allah yabaki miji nagari me kaunarki" "ba komai Zahra, Nagode sosai nima Allah ya amsa mana bukatunmu"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now