ABDUL JALAL (2020)

287 19 1
                                    

.[8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

    _ABDUL  JALAL_
           (2020)

      _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
    (Daddy's girl)

               PAGE-  13

PART 1

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Domin joining group dina follow this link
What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Is a free book

Ina yinku AbdulJalal novel fans irin💯💯💯 da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all ❤❤❤

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢
Your comments give me courage

    Ina amfani da wannan damar gurin mika sakon barka da sallar layya ga dukkan al ummar musulmi
Ubangiji Allah ya maimai tamana

         -my first Novel-

Da sauri maryam takarasa bakin gadon da Aliyu yake kwance yana ta fidda jini ta hanci tabaki ga wani wahalallen numfashi da yake saukewa da kyar, da gudu take ta zube a gabansa
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Aliyu meya sameka haka"
Shine abinda maryam tafada cikin kuka
Jalila ma da gudu ta tafi gurin abbanta cikin karfin hali ya rungume Jalila tareda janyo maryam kirjinsa
  "Noor kiyi hakuri na taho kano ban gayamiki ba Usman ne yakirani jikin innarmu yayi tsanani shine na taho muka samu accident a hanya"

"Sannu abu Jalila Dan Allah ka warke ka tashi mucigaba da rayuwa u are my life habibi"
  "Is not complicated dear kawai internal injury ne kuma likitoci zasuyimin aiki zan warke insha Allah
Dama haka kike matukar sona noor irin wannan rikicewa haka I love u too my dear u mean a lot to me maryam"

Yafada cikin karfin hali da son kawar wa da maryam damuwa
  "Abu Jalila is not time for joke lafiyarka tafiyemin komai nikam, inaso mu rayu tare kacigaba dabani farin ciki nida baby Kaine garkuwarmu kai ka dai ka ragemin "
Tafada tana zubda hawaye

"I love u too ummu Jalila, kije kuduba inna se ki turomin Dan uwana zamuyi magana"

Harta yunkura zata tashi
"Maryaman Aliyu"
Ya kira sunanta dawowa tayi ta zauna ta kuma riko hannunsa

"Dan Allah ko bayan raina kar abinda matar usaman take miki yasa ki raba zumuncin dake tsakanin yayanmu"
Gyada masa kai tayi sannaan
Ta mike jiki a sanyaye ta nufi kofar fita,
Usman yana waje a bakin kofa yanajin duk hirarsu gwanin ban tausayi, haka usman ya dinga share hawaye kaman karamin yaro
Jiki a sanyaye Tafito daga dakin Usman ya nuna mata dakin da aka kwantar da inna
Usman ya koma dakin da Aliyu yake yaje gaban gadon Aliyu ya zauna ya riko hannunsa
 
"Dan uwana ya jikin naka ya kake ji yanzu"
"Yayana mutuwa zanyi bazan rayuba inaso in barmaka amana ne da duk duniya bame rikemin se kai"
Aliyu ya fada yana Jan numfashi da kyar
Yacigaba da cewa

"Dan Allah karkabari babyna tai kukan maraici, ko aure maryam tayi ban yadda ta tafi da yata agolanci ba, inason baby tayi karatu me zurfi, na addini Dana zamani
idan ta isa Shiga Jami a inaso takoma hannunka kasan tarbiyar ya mace seda tsayayyen namiji,"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now