ABDUL JALAL 98

330 21 3
                                    

. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 4️⃣5️⃣98

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

_MY FIRST NOVEL _

A hankali Jalila ta cigaba da bin bayan Hannah, ba tareda ita Hannah ta sani ba, Hannah ta bude kofar babban palourn ta shiga, Jalila ta biyo bayanta amma ta tsaya a corridor yadda ba wanda ze ganta, Hannah ba karamin mamakin kyau da tsaruwar gidansu Jalal tayi ba, an kashe masa dukiya matuka, tun daga harabar gidan zaka gane mzauna gidan na cikin ni'imar ubangiji ta dukiya da yake bada ita ga wanda yaso a lokacin da yaga dama.

Koda ta shiga palourn ba kowa, seda ta tsaya ta karewa tangamemen palourn kallo, sannan ta jinjina kai tareda yin ajiyar zuciya, ta fara sallama, Mummy dake kitchen ta amsa tareda fitowa da jug a hannunta, suka gaisa da Hannah, Mummy na mata kallon rashin sani,
Mummy tace
"bari in kira miki Ilham din, dan a zatonta kawarta ce" Hannah tace "A'a ba gurinta nazo ba, Mummy dan Allah Jalal fa?"

Mamakine yakama Mummy amma ta dake tace
"Ai kusan watansa guda baya gari, yana lagos"
Hannah tace "Ai dole ya lallaba ya gudu lagos mana, Ina fatan mahaifinsa yana nan"

Mummy tace "lafiya kuwa?"

"Ina fa lafiya, ina son ganin mahaifinsa tunda shi baya nan"

"me mahaifinsa ze miki ne? Ki gayamin menene?" hakan yayi daidai da fitowar Ilham da alama fita zatayi, kawai taga Hannah, take gabanta yayi mummunar faduwa, kirjinta yafara dukan goma2, ta wani hade rai, ta karaso palourn cikin kasaita kaman gidan father dinta, tazo ta tsaya tareda kama kugu tanawa Hannah kallon da wacce kika zo?.

Kallo daya Hannah tayi mata ta dauke kai, tareda yin murmushi a ranta ta kalli Mummy tace

"Gara in gayawa mahaifin Sa abunda ake ciki, na gaya masa wancan karon be dau mataki ba, shi namjine ke ba lallai ki iya daukar abunda zan fada ba"

"ki Fadamin bakomai ni mahaifiyarsa ce ai"
Hannah ta gyara zama, sannan ta kalli Mummy tace

"wancan karon da nazo nayiwa mahaifinsa magana, nace yayi yadda zeyi a hadu mu rufawa juna asiri amma ba'ace min komai ba, nikuma asirina yana daf da tonuwa, Ina dauke da cikin Jalal na watanni uku a yanzu"

Da sauri Jalila tasa hannu ta toshe bakinta tana zare ido, gaba daya taji kafafuwanta suna rawa.

Hannah ta cigaba da cewa "muna haduwa da Jalal a hotels, kokuma idan yake night clubs, yasaba yimin ciki yace in zubar, wannan karon likita yace rayuwata na shirin fadawa hatsari muddin na zubar da cikin nan, ga iyayena na kokarin ganewa, soyayyar Jalal ce tasa na bashi kaina, wallahi koya aureni ko nayi kararsa ya kula dani da dansa"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now