ABDUL JALAL 84

347 20 3
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 3️⃣1️⃣84

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com




_MY FIRST NOVEL _

Kallonsa Jalila take kaman wata sokuwa, ya daga kai yaga su Jawwad da Abba suna tahowa, yakuma durkusowa yace mata
"Allah ya kaiku lafiya"
Hanan tana kallon abunda yake faruwa harsuka karaso inda motar take, Abba yayi musu nasiha tareda fatan suje lafiya, Abdallah ya shiga ya kunna mota, yafito da ita daga cikin gidan, Nana tace
"Jalila dan Allah inkin tafi karki dade, zanyi missing dinki sosai"
"Bazan dadeba Nana, nima zanyi missing dinki" suka rungume juna sannan Jalila ta karbi jakarta a hannun Nana.

Hanan tazo bayan Jawwad ta wajen kunnensa tace "I love you Haidar, i wish to see you soon" ta juya ta shiga mota, murmushi kawai Jawwad yayi, Jalila ta bude mota ta shiga amma hankalin ta yana kan Maganganun Jalal.
Jalal yazaga sukayi musabiha da Abdallah yace
"Allah ya saukeku lafiya, ya kiyaye hanya"
Suka amsa da Ameen banda Jalila da taketa zancen zuci.

Abdallah ya kunna mota yafara ja a hankali Jalila tanata waigawa tana kallon Jalal harsuka bar layin, Hanan ta daki cinyarta tace
"To ai seki dena kallon nasa haka"
dan hade rai Jalila tai tace
"kamarya indena kallonsa? Wakenan?"
"Jalal mana, aishi kike kallo tukuna ma meya gaya miki ne naga jikinki yayi sanyi?"

"Bansaniba, niba shinake kallo ba"

Hanan tai dariya tace
"Queen ba dai taurin kai ba, bakyason gazgata zuciyarki, ga abu a zahiri amma kinata wani basarwa"

"Ke dan Allah ki kyaleni Hanan"
Hanan tace
"Na kyaleki"
Abdallah yana jinsu yai murmushi yace
"Jalila kokece sirikar tamu ne? Keda Jalal kuke boyewa"
"Tab Allah ya kiyaye, bawani sirika, wadda ze Aura tana gidansu cousin dinsa ce Ilham"

Hanan tace

"karya kikeyi, kefa kikace bazaki bari ya Auri Ilham ba"

"to dan ban bari ya auri Ilham ba kuma ni seya Aureni?.

Abunnasu na nema yakoma fada dan haka Abdallah ya shiga yimusu hira aka manta da wannan zancen, Jalila ta rarraba hankalinta me Jalal ya ajiye mata a cikin Al'qur'ani tsawon wannan lokacin bata taba ganiba? Sannan mezesa yace ze bar kasar nan haka taita zancen zuci, Hanan ta fuskanci Jalila nacikin damuwa, Amma taurin kai ya hanata yadda.

Nana taji babu dadi sosai da Jalila ta tafi jinta take kaman marainiya, Naja taje ta samu Maama ta gayamata abunda yafaru, Maama taimata alkawarin tasan matakin dazata dauka, zata kawo dukkan karshen wannan yaran, zatayi wa Abbansu Jawwad magana.

Jalila se kusan takwas na dare suka isa garin bauchi, wani irin katon estate ne, dake dauke da gidaje dayawa a ciki, kuma kusan duk irinsu daya, tundaga farkon estate din suke cin karo da sojoji, da sunzo wucewa Abdallah yake daga musu Hannu, wani gida suka nufa, duk gidajen da Jalila ta gani a estate din wannan gidan yafi shi girma, shima akwai sojoji abakin gate din, bude musu akai Abdallah yashiga sunata daga masa hannu, Abdallah ya tsaya suna gaisawa, suna masa sannu da hanya, daya sojan cikin gurbatacciyar hausar sa yacewa Hanan

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now