ABDUL JALAL (2020) 16

303 24 0
                                    

.🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

    _ABDUL  JALAL_
           (2020)

      _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
    (Daddy's girl)

               PAGE-  16&17

PART 1

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢
Your comments give me courage

Aimin afuwa the page is not edited
         -my first Novel-

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un shine abinda Jalila ta fada jikinta a sanyaye
A hankali ta sauke wayar daga kunnenta ta kashe wayar
Takalli siyama
"Aminiya ya tafi"
Yasalam shine abinda siyama ta furta

"Kwantar da hankalinki har yanzu da sauran lokaci ai"
"Kwanciyar hankalifa babu shi Aminiya dan bakiji yadda zuciyata take min bane
Bari in tafi Gida uumi tace kar in dade kuma kinga nabata lokaci bari in tafi kawai"
Har gate Siyama ta rakota tana bata kwarin gwiwa, tare da bata shawarar cigaba da addu'oi
Sannan ta mata alkawarin zatazo har gidan taji yadda akayi
Haka Jalila ta tafi Gida jikinta a mace
Yanayin fuskar Ummi ya nuna mata tayi fushi da ita
Dan se basar da ita take Jalila ta rasa meyake mata dadi

Jeje ne a tare da wani mutum a cikin mota me tint glass yasaka wando three quarter da wata Yar Riga Mara hannu suman nan tayi tsage²
Kai daka ganshi ka ga dan iska

"Katabbatar kayi abinda yakamata in kukaje kasan abinda ya dace kayi shima wannan aikin naka akwai kaso me tsoka ka tabattar da aikin nan ya tafi dai² "
Mutumin yayiwa jeje maganar

"Considered it done my boss zan tabbatar da aikin nan ya tabbatat"
Jeje yafada yana dan risinar da kai
"Good"
mutumin yafada cikin Isa
Sannan jeje ya bude kofar motar ya fita ya dauki akwatinsa
Inda sukayi zasu hadu da Jalal yaje ya tsaya ya kirashi a waya yan mintuna kadan sega Jalal ya karaso
Shima
"hmm yau kayi abun arziki ka cika alkawari"
Murmushi Jeje yayi
"ba dole ba my boss ina ciki farin ciki"
"Good yanzu se mu tafi ko"
Gaban Jalal ne yai mummunar faduwa
Meyake damuna ne haka, menake shirin yine"
Jalal yake maganar a zuciyarta

"Yanaga kana tafiya kuma a hankali yanzu ko akwai abunda yake damunka" Jeje ya tambayeshi
Girgiza kai Jalal yayi
Jeje ne yafara mika passport dinsa aka duba aka bashi ya danyi gaba yana jiran a duba na Jalal,
Jiki a sanyaye Jalal ya mika passport dinsa

(Karka kara kirana dan uwanka Jalal niba dan uwanka bane, tunda zaka iya manta soyayya da shakuwar dake tsakaninmu ka tsallake ka barni,
Tun tasowata bani da dan uwa namiji ban budi ido da kowa ba a matsayin aboki dan uwa sekai,!!!!!)

Maganganun Jawwad ne suke dawo masa dakuma tsantsar damuwa da hawaye da ya gani kwance a idon Jawwad su yake tunowa se yaji zuciyarsa ta cunkushe bakin ciki ya ziyarci zuciyarsa, gaskiya ba karamin kauna Jawwa yake masa ba in ya tafi beyiwa kansa adalci ba Jawwad wani bangarene me mahimmanci a rayuwarsa ga kuma mahaifinsa, anya inyayi tafiyar nan yayiwa kansa adalci
jikinsa ne yayi matukar yin sanyi, hannu yasa ya karbi passport dinsa ya juya dabaya yafara tafiya
"Jalal ya haka lokaci fa inazaka jene"
Jeje ya tambayeshi
Bebashi amsa ba yacigaba da tafiya da gudu Jeje ya taho ya sha gabansa
"Man wai meyafaru ne ?
Ina zakaje yanzu fa jirginmu ze ta shi"
  "Zaka iya tafiya nikam na fasa"
Zaro ido Jeje yayi "why meyasa zaka fasa"
"Saboda haka naga dama nace in zaka ka tafi ni na fasa"
Ya bashi amsa
JALAL yayi maganar a tsawace

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now