ABDUL JALAL 61

345 20 4
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 8️⃣/61_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

_MY FIRST NOVEL _

Wani irin Kallo Mum tayiwa Hanan

"I don't think you are in your senses, Hanan, kawartaki dukda yarinyar ba wani yimin tayiba, amma son da kike mata yasa na kyaleku tare, amma hakan bazesa inkasa gayamiki gaskiya ba, Hanan inkikayi haka baki kyautaba, hakan ba daidai bane, Jalila taana kaunarki meyasa zakiyi mata haka"
kwalla ce ta taru a idon Hanan

"Mummy ki fuskanceni banyi haka dan cin amanar Jalila ba, Mum wallahi makauniyar soyayya nakewa Jawwad, Mummy he is very nice and gentle, gashi salihi, Mum soyayyata da Jawwad mafita ce kuma ceton Jalila ne, inajinta a zuciyata kamar yar uwata ta jini, dan haka bazan iya cutar da itaba all i know is that inason Jawwad "
"Kamar yaya kenan, tayaya kike son maida karya gaskiya"
Labarin abunda ke tsakanin Jalal da Jalila tabawa Mummy, ta nisa tace

"Mum ko bankuma cewa komai ba kinsan Jalal is her e destiny, ita kadaice zata iya sadaukarwa domin ceton sa, Mum mahimmanci Jalal a rayuwarta ne yasa ake mata nuni da halin dayake ciki a mafarki, Mum kibani karfin gwiwa, zanyi meyuwuwa in dauke hankalinta daga kan Jawwad, sannan zan temaketa akan rayuwar Jalal" Jikin Mum ba karamin sanyi yayiba dajin labarin da Hanan tabata,
"Shikenan Auta, zancigaba dayimuku Addu'a Allah ya zaba abunda yafi Alkhairi".

Jalal cikin gida ya tafi domin samun yin hira da daddy, yana zuwa ya tarar da Ilham a babban palour da waya a hanunta tana waya, kota kanta bebi ba yanufi part din daddy, bayansa Ilham tabi da kallo

"muje zuwa Jalal zakaga tsiya" Jalal yana zuwa ya tarar da daddy a palour dinsa suna hira da mummy, daddy na ganinsa yai murmushi "dan halak kaki ambato, zancenka nakeyi a a raina karaso Dama inason ganinka dan gidan daddy"

"to gani mezaka bani, Jalal yafada yana zama akan kusa da daddy"

"Jalal magana nakeso muyi da kai, Mum dinka tazomin da magana nayi murna da jin hakan shine nakeson ji bakinka" Mummy tai farat tace
"Ba dai maganar da mukayi dazu bane, ai mungama magana dakai, meye kuma na tada wannan zancen, kayi abunda yakamata kawai" daddy yace
"A a Madam karmuyi gaggawa, dole mubi komai a sannu sannan inji ta bakin kowannensu" "A'a fa ai mungama magana wannan kawai maida hannun agogo baya zakayi"
Jalila da sallama ta shigo palourn, Ilham na palourn amma tai mirsisi taki amsawa, "Aminiya Ilham amsa sallamar ma seyazamo miki aiki, amsa sallama dabi ace ta kyakkyawan musulmi, karki zama irin yayanki nan mana" tsaki Ilham tayi tareda fadin
"meye hakane wai? Ke kullum in baki shiga sabgata ba bakyajin dadi ko? Ina ruwanki da nida danuwanane mayya"
"Aini indai a irin sha'anin nan ne to nafi uwar mayya naci, mayya in akayi magani ana samun nasara nikuwa babu abunda zakiyi kiyi nasara akaina, sannan duk abunda ba'aso ni shinakeyi dan aji haushi, and the most craziest part of me is that bana riko, yanzu zamuyi fada yanzu zan manta, duk abunda na rike a zuciyata nake fushi akansa to yanada mahimmanci a gurina, dan haka nibana gaba dake Ilham dan bakikai inyi hakan ba dake, sannan kuma bazan fasa bata miki raiba in har kikayi abunda yaci karo da Ra'ayina sedai kiyi hakuri "
Lallai Jalila tacika yar rainin hankali, wulakanci goma da ashirin.
Duk yada Mummy tayi a wayance kar Jalal yaji zancen nemamasa auren Ilham daddy yaki, karshe a fusace Jalal yace" waini meye hakane daddy, afadamin komene mana, inbaza ayiba meye na dakko maganar agabana, nibanason irin haka fa"
"Ohh ka kwantar da hankalinka yaron kirki, aiba abun tashin hankali bane, maganane me dadi akanka, maganane nacika maka burin rayuwarka, Mummy dinka tagama yimin bayani akan komai, nagame da abunda ke tsakaninka da Kanwarka Ilham, dan haka zanje muyi magana da mahaifinta asa rana, nayi farinciki da har kafara tunanin aure Jalal, cigaba yafara zuwa a rayuwarka kaga......

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now