ABDUL JALAL (2020)

321 23 0
                                    

 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

    _ABDUL  JALAL_
           (2020)

      _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
    (Daddy's girl)

               PAGE-  14

PART 1

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢
Your comments give me courage

         -my first Novel-

"Karki caka masa, dan Allah
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!!"

Shine abinda Jalila tafada da karfi ta farka daga mummunan mafarkin da take Wanda ya kasance tsakiyar dare
Da gudu Ummi ta yanke sallar da take ta taho kan gadon ta dago Jalila
"Lafiya me yasameki Jalila,?"
"Bakomai Ummi mafarki nayi"
  "Kinyi adduar kwanciya bacci?"
  Gyada kai Jalila tayi alamar eh
"Alwala fa"
"Itama nayi Ummi"
"Jeki sake alwalar sekizo ki kwanta"
Mikewa Jalila tayi taje ta yo alwala ta dawo ta kwanta tayi shiru tana kuma tunanin mafarkin da tayi
A hankali Ummi ta zo ta rungume Jalila tana mata
addu a, amma har yanzu kirjin Jalila bugawa yakeyi da sauri²
  Washe gari da safe suna karyawa, amma hankalin Jalila yana kan mafarkin da tayi jiya Ummi ta lura da ita dan haka, ta yanke shawarar  tambayar Jalila mafarkin da tayi take ihu cikin dare

"Jalila mafarkin me yasaki ihu cikin dare jiya"?
"Ba komai"
Jalila tabata amsa

"Kaman ya ba komai kin firgitani"
"Ummi ni dai nasan nayi mafarkin tsoro amma na manta me nagani"
Kallonta Ummi ta yi
"Baby kenan adinga addu'a dai"
"Inayi ai Ummi amma zan kara insha Allah"
"Yayi kyau kici abinci kidena wannan tunanin"
Gyada kai Jalila tayi ta Dan cakali abincin ta bari
Uniform din islamiyyarta ta dakko tana gogewa, amma duk kokarin ta, ta cigaba da harkokinta tana tuna mafarkin nan se gabanta yayi mummunar faduwa
"Subhanallah"
Shine abinda Jalila take fada in ta tuna mafarkin, haka ta karasa gugar tasaka uniform din islamiyya tana zaman jiran siyama ta karaso su tafi islamiyya
Qur'anin da Daddyn Jalal yabata ta je ta dakko tasamu guri tazauna tana kallonsa tana shafawa se jujjuya shi take a hannunta
Sallamar Siyama ta ji amma bats motsa daga inda take ba Siyama suka gaisa da Ummi a tsakar gida
"Ummi ina Jalilan take?"

"Tana cikin dakinta yau narasa meyake damunta yau tun safe tana daki"
"To Ummi bari ingani kinsan ta wani lokacin se a hankali"
"Aikam halin Jalila ai se hakuri"

Dakin Jalila ta shiga ta tarar da ita tana ta jujjuya Qur'ani a hannunta
"Aminiya lafiya dai yau kuwa,wannan Qur'anin fa me kyau, kice har babban guzuri kika taho mana da shi"

Ita dai Jalila ba tace mata komai ba ta mika mata
"Masha Allah gaskiya yayi kyau box din da yake ciki ma gwanin sha awa bari in sashi a Jaka mutafi da shi Islamiyya munyi sabon Al Qur'ani

"Bani"
Jalila tasaka hannu ta karbe Al Qur'anin daga hannunta Jalila

"wannan ba na zuwa islamiyya bane kallonsa kawai zan dinga yi"
"Kamar ya "?
" kamar yadda nagaya miki"
"Allah yabaki hakuri naga yau tambotsai kikeji"
Jalila bata kuma kulata ba ta dauki hijjabinta ta saka ta maida Qur'anin cikin cover dinsa ta adana shi
  Suka fito
"Ummi zamu tafi"
Siyama tayi maganar tana risinawa
"To adawo lafiya Allah yayi Albarka"
"Ameen Ummi"
duk wannan maganar da ake Jalila batace uffan ba
Har sunkusa fita Ummi tace
"Ke madiga ina taki Jakar makarantar?"
"Ban gan taba sena dawo zan duba"
Tafada tana sunkuyar da kai
Girgiza kai kawai Ummi tayi sukuma suka tafi

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now