ABDUL JALAL

332 21 1
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

              _ABDUL JALAL (2020)_

       _Story and written by_
      AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
        
   PART 2        
                          _PAGE  1️⃣8️⃣71

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

     
                _MY FIRST NOVEL_

Haka khadija tacigaba da wasa da hankalin Saudat ba tareda ita Saudat din tasan me khadija take shiryawa ba.

Khadija ta karbi kudade dayawa agurin Kabir da sauran kudaden data damfara a gurin samarinta tafara business na atamfofi da kayan sawa, gurin manyan masu kudi, saboda tace in Allah yasa lokacin bikinta kece raini zatayi bazata barima azo ayi wani abu  a wannan gidan nasuba, biki za'ayi kaman na diyar sarakuna, dan jikinta yana bata zatayi galaba akan Habib saboda alamun sun nuna yanada saukin kai da tausayi.

Ranar da habib yadawo Nigeria me gadinsa yakira khadija a waya yasanar mata, taimasa godiya take ta turamasa katin 5k saboda albishir din dayayi mata, shi habib har yamanta da batun me turomasa messages, se bayan kwana biyu yamaida layinsa na Nigeria messages din khadija yafara cin karodasu ba adadi, tsaki yayi ya aje wayar yashiga sabgoginsa.

kwanan sa uku da dawowa yakoma gurin aikinsa, yana zaune a office aka kirashi a waya, bakuwar lamba ne dan haka beyi tunanin komai ba ya daga wayar, tana sallama ya gane wacece, amma yarasa meyasa duk lokacin dazata kirashi baya iyayi mata rashin mutunci.
Yana cikin wannan tunanin yaji muryarta tana cewa "Rayuwata, barka da dawowa kasa Nigeria, ina maka barka da zuwa nayi kewarka matuka, nayi rashin lafiya sosai bayan tafiyarka, ina fatan kundawo lafiya?" Abun mamaki taji yace
"ya jikin naki?" seda tayi murmushi ta wani lumshe ido "Jiki ina samun sauki Alhamdilillah"
"me yake damunki?" takuma kashe murya

"hayatee komaima yana damuna, nikaina narasa meke damuna, amma jigon rashin lafiyata soyayya ce, at least zansamu relief tunda ka dawo, bari in barka ka huta, I love you hayatee"

ta kashe wayarta, tunda habib ya dawo Nigeria tafara shawo kansa saboda koyace katta kara kiransa bata fushi, kullum cikin nuna masa soyayya take, ta lura ya dan damu akan maganar rashin lafiyarta, hakan yasa tafara ji ajikinta burinta yana daf da cika. Tacigaba da kokari tana dauke hankalin Saudat daga kokarin zuwa gidan habib.

Seda khadija ta lura habib yafara bata kulawa, seta dena tura masa message ta kashe wayar da take kiransa da ita domin ta tabattar da ko yafara sonta, haka ta danne zuciyarta tsawon sati biyu bata kirashi ba kuma bata turamasa message ba.

Ranar da sati biyu ta cika khadija ta kunna wayarta, messages ne suka shigo wayarta, data bude duk na habib ne sekuma na kamfanin layi, dayake shikadai take kira da layin, duk messages din yana tambayarta ina tashigane layinta baya shiga Allah yasa lafiya, bata san lokacin datayi wani tsalle ba tayi ihu a daki, mamanta ta shigo dakin da sauri "ke lafiya meyasameki?"

"bakomai mama bansan nayibane"

"to Allah ya shiryeki auta" mama ta fice khadija ta mike tsaye hada rawa a cikin daki.

Bayan sallar magariba kabir ya tura yaro yace yayi masa sallama da khadija, tace yaron yace tana zuwa, ta shirya zata fita gurin kabir sega kiran Habib.
Nan da nan ta tashi ta kulle kofa tazo tanemi guri ta zauna akan gadonta ta daga wayar cikin sanyin murya tai masa sallama, kafin ya amsa sallamar yace
"ina kikashiga haka tsayin wannan lokacin?"
"hayatee bani da lafiya ne fa" ta faɗa cikin sigar shagwaba
Cikin sauri yace "subhanallah jikinne har yanzu? Yanzu kina inane?"
"ina gida naji sauki"
"dagaske kinji sauki kokuma wasa kike?"
"Am serious, yau naci Abinci sosai nayi wanka nayi kwalliya, i wish kaga kwalliya nan hayatee" murmushi yayi yace "dagaske?" "Eh mana nayi kyau sosai, sedai ciwon so duk ya ramar dani"
"yaushe zan ganki?"
"Duk sanda kakeso, a shiryenake"
"kiyi fixing time, seki gayamin zanzo mugaisa"
"masha Allah, hayateee harnaji na warke gaba daya"
"to Allah yakara afuwa, bari zan shiga gida" cikin sauri cikin shagwaba khadija tace
"haba hayatee ni wallahi bangaji dajin muryarka ba, kalli tsayin lokacin daka dauka bana jin muryarka fa" haka khadija ta dinga hilartasa suka shantake suna waya, tana masa hira me dadi har gurin goma da rabi na dare sannan sukayi sallama.
Kabir yagaji da jira gashi lokacin sanyi amma khadija taki fitowa maganar duniya tayi banza taki bude kofa tacigaba da wayarta, daga baya tace ace masa yacigaba da jira inyaga ze iya tana da abunyi me mahimmanci datakeyi.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now