ABDUL JALAL 112

991 26 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣8️⃣111

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

_MY FIRST NOVEL _

Ummi ta rungume Jalila sosai a jikinta, Jawwad ya dakko ruwa me
Sanyi a fridge aka shafawa Jalila ruwan a fuska, a hankali Jalila ta bude ido tareda jero ajiyar zuciya ta sauke idonta akan Ummi, kara kankame Ummi tayi tareda sake fashewa da kuka.

Maama tace

"Jalila ba kuka zakiyi ba, kamata yayi ki godewa Allah ganin mahaifiyarki da kikayi"

Abba yace

"hakane yakamata ki godewa Allah sannan ki godewa mijinki da danginsa"

Kallon Abba tayi cike da rashin fahimtar abunda yake nufi

Daddyn Hanan yace

"gaskiya kam, mijinki ya cancanci yabo, da shi da danginsa, kuma kafa da kafa zamuje domin nuna godiyar mu da farincikin abunda sukayi"

Sam Jalila bata san inda zancen nasu ya dosa ba.

Ummi ta share hawayen fuskarta tace

"tabbas bayan godiya ga Allah daya nuna muku naku ahalin, zanyi godiya ta musamman bisa Jajircewarku da kulawa da tarbiyya yarinya ta, nagode Allah yasa ku dauka a gidan Aljanna, Jalila bata taɓa kukan rashin mahaifi ba sanadiyar tarasa wani abu ba nagode kwarai.

Tabbas Jalal yasan inda nake, lokacin dana bar ku nayi sallama domin zuwa garinmu, motar mu ta tsaya domin musulmin cinkinmu su gabatar da salla, bayan nayi salla ne na tsallaka wani restaurant na sai Abinci, na fito zan tsallaka titi mota ta bigeni, mutane suka fara taruwa a gurin, wanda ya bigeni dan sanda ne, dan haka ya nuna musu id card dinsa ya daukeni ya tafi dani.

Ya kaini wani Asibiti na kudi, inda aka tabattar masa dana samu matsala a kashin bayana, sannan nasamu internal injury akaina, lokacin da labarin bata na ya iskeku Jalal ya shiga zuwa offisoshin yan sanda domin an gaya masa dan sanda ne ya bigeni, Allah ya temake shi yasamo wanda ya bigeni yaje har Asibitin da nake, koda yaje yaga halin da nake ciki, yai magana da mahaifin sa akayimin visa zuwa Dubai a wani Asibiti, na dade ina jinya saboda aikin da'akayimin Kashi- kashi a bayana saboda matsalar dana samu.
Dana fara samun sauki Jalal yai magana da Hajiya Salma aka maidani Can England gurinta take jiyyata aka cigaba da bani kulawa a can.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now