ABDUL JALAL

320 20 3
                                    

. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

              _ABDUL JALAL (2020)_

       _Story and written by_
      AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
        
   PART 2        
                          _PAGE  3️⃣3️⃣86

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

     
          
         

   
          _MY FIRST NOVEL _

Kara hade rai yayi ya shiga palourn ya zauna becewa kowa komai ba ya zauna, daddy ya kalleshi yace
"son ka tashi lafiya"
"Alhamdilillah" daddy yai murmushi yace
"Masha Allah, kayi breakfast ne?"
"A'a ina jiran Jawwad ne kuma bezoba"

"bari a hada maka anan kaci" daddy ya kalli Ilham yace
"Ilham hadawa yayanki Abinci mana"
Jiki na rawa ta mike ta nufi dining din daddy ta hado masa kayan breakfast ta kawo ta ajiye, shidai be kulata ba ya zauna yafara cin Abincin sa, daddy suka cigaba da hirarsu shidasu Mummy, shidai Jalal bece musu uffan ba, yana kammala cin Abincin sa ya mike ze fita, daddy ya dakatar dashi ta hanyar cewa
"Ina kuma zakaje? Zamuyi magana ne ai"
Dawowa yayi ya zauna yana kallon daddy, daddy yace

"Jalal kaga zamanka haka baze yuwu ba, tunda ansamu degree daya da kyar, kaga shekarunka sun fara Ja daga kai har Jawwad zuwa yanzu yakamata ace ansama maka abokiyar rayuwa a matsayinka na namiji, amma bantaba jin kacemin ga budurwarka ba, ko akwai wata bansaniba "

Wani irin kallo Jalal yayiwa daddy sannan yace
" dan Allah adena wannan zancen, in lokacin Auren yazo za'ayi, amma dan Allah for now a kyaleni"

"A'a Jalal babu batun a kyaleka, banason cigaba da ganinka a haka ba Aure, bakasan Aure shine cikar mutum ba, inma baka da budurwa ne ga Ilham tace taji ta gani tana sonka a haka, meye laifin Ilham? Dan haka nakiraka tunda kaida Ilham duk dayane"

"A zato na a baya munyi wannan Maganar ta wuce? Wannan tamkar maida hannun agogo bayane, nace bana sonta, bana sonta akan me za'a takuramin, kuma ai naga Aure ba wajibi bane, balle ace in banyiba nayi laifi, dan haka a kyaleni bana sonta bazan Aureta ba"

A fusace Mummy tace

"Baka isa ba wallahi, da abun kunyar da kake shirin jawomana gara aimaka Aure, kokana so ko ba kaso Aure se anyi shi"

Jalal yace "Abun kunya na nawa kuma? Koke har yanzu abubuwan da nakeyi basu isheki kunya ba? Nagama magana ba wanda ya isa yamin Auren dole wallahi, duk duniya natasani wannan yarinyar natsani duk wani abu da yashafeta, Aurene bazan Aureta ba"

Ilham ta rushe da kuka tace "Nashiga uku Mummy, menayiwa Yaya Jalal haka?"
Mummy tace
"rabu dashi, Aurene babu fashi, tunda yasan yafara biye biyen mata, har karuwai sufara biyoshi gida, rashin mutuncin sa ya wuce yaje ya samesu a can, se yafara kawosu gida, ai dole a dau mataki akansa"
daddyn Jalal yaso ya hana Mummy karasa maganar amma seda ta karasa, Jalal dake shirin fita ya tsaya cak ya juyo

"Niza kiyiwa sharri dan nace bana son wannan shashashar, Nine nake bin mata, kirasa dame zaki alakanta ni se wannan mummunan Aiki, to wallahi da in Auri Ilham gara a dauramin Aure da Akuya, Nagode da sharrin da kika yimin a matsayinki na uwata"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now