ABDUL JALAL

335 23 6
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

              _ABDUL JALAL (2020)_

       _Story and written by_
      AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
        
   PART 2        
                          _PAGE  3️⃣4️⃣87

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

     
          
         

   
          _MY FIRST NOVEL _


Tsaki Jalila tayi, taje ta dakko trolley tafara zuba kayanta, A daren Jalila taje tasamu dadyn Hanan tace masa zata koma gida jibi saboda sun koma makaranta, daddy beji dadi ba yacewa Jalila da kansa ze maida ita gida.

'yan gidansu Hanan sunji babu dadi batun tafiyar Jalila, sun mata Alheri sosai, Inna ma taji babu dadi, tace itama wataran zatasa akaita kano gurin Jalila.

ranar da Jalila zata koma tun safe tagama shirinta tsaf, karfe goma na safe daddyn Hanan da kansa yasa Jalila a mota ya tafi kai Jalila gida, suna tafe suna hira.

Jawwad yayi duk yadda zeyi ya hana Jalal tafiya amma wannan karon Jalal ya dage, yayi rantsuwa yace seya tafi sannan yaki gayawa Jawwad hakikanin abunda akayi masa a gida, Jawwad ya tafi gidansu Jalal yasamu daddy bayan sun gaisa yace

"daddy me akayiwa Jalal ne yace in yatafi baze sake dawowa ba, bansan me akayi masa ba?"

Nan daddy ya gayawa Jawwad abunda yafaru Jawwad yace

"Amma daddy meyasa kake zargin Jalal akan wannan, daddy zan iya rantsuwa da Alqur'ani Jalal baya neman mata, koma wacece sharri take masa daddy"

"Jawwad se daga baya naga  nima ban kyauta masa ba, ka bashi hakuri, yadena fushi da daddyn sa, amma kokana da masaniyar dalilin dayasa Jalal ya tsani Ilham, ko tayi masa wani abun ne?"

Jawwad yayi Jim sannan yace "A'a daddy nima bansaniba, ban san metayi masa ba"

"Anya kuwa Jawwad zan yadda bakasan komai ba?"

"daddy dagaske nake bansan komai ba"

"to shikenan, amma Jawwad dan Allah ka hana Jalal tafiyar nan, nasan yana fushi dani, amma karya tafi ya bar daddyn sa"

"Insha Allah daddy zanyi kokarin yin hakan"

Jawwad ya tashi ya fita, tun lokacin da Abba yayiwa Jawwad zancen kai kudin Auren Naja yake rashin lafiya amma be gayawa kowa ba, ga kuma tension din Jalal, yakoma daki ya tarar Jalal yana ta hada kaya, ya zura masa ido, yarasa mema zece masa, kansa ne yake sarawa sosai ya kwanta akan doguwar kujera ya lumshe ido, yanata sakawa yana kwancewa.

Nana tasan da dawowar Jalila dan haka tanata murna, tana shirye2 itakuma Naja so take Jalila ta dawo ta kuntata mata rai.

Karfe biyu na rana Su Jalila suka iso kano, Nana ta fito ta taresu ta rungume Jalila suka dinga murna, Abba baya gari, ya tafi da Maama lagos, kwanansu uku da tafiya, dan haka Jalila ta budewa daddy sitting room ya zauna.

Nana ta dauki kayan Jalila ta shiga dasu cikin gida, ta kawo wa daddy ruwa da lemo da Abinci.

Duk abun nan, Jawwad besan su Jalila sun dawo ba, Jalila da kanta ta tafi part din Jawwad tana shiga palourn sa ta tarar da Jawwad a kwance akan kujera ya lumshe ido Jalal kuma yasa TV a gaba amma sam ba tv yake kallo ba tunani yakeyi.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now