ABDUL JALAL 85

346 26 2
                                    

.🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 3️⃣2️⃣85

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com


_MY FIRST NOVEL _

Jalila tace "Yasalam, Nana kiname Ilham zata shigo har cikin gidan nan ta daukarmin abu natane? Meya kai hannunta kayanmu harta daukarmin abu"

"Jalila Al'qurani fa ba Novel bane ko littafin hausa da zan kamata da kokawa in karba, gyaran daki nakemana tashigo ta ganshi ta dauka"

"Nana kingama dani dakika bari ta tafi dashi, amma tunda tace idan na dawo na je karba ki gayamata ta saurari dawowarta wa, tasan karona da ita ba dadi, zanzo in karba idan bata bayar dan Allah ba zata bayar dan dole, karma kikuma tada maganar tabaki zan dawo in karba, banda Jahilace me zatayi da Al'qurani metasani aciki? Inma tasani bashida amfani a gurinta ai"

"To nidai Allah yabaki hakuri, ni bayan haka wasu maganganu tazomin dasu dasam ban gane inda ta dosa ba?"

"Kamar yaya?" Jalila ta fada a kagauce

"Nikam Baby meye hadinki da Jalal ne?"

"Wane irin tambaya ne wannan Nana?"

"Jalila inkinga rashin mutuncin da Ilham ta dingayi a dakinmu sekinsha mamaki, tana gayamin wai na hada kai da ke zaki kwace mata Jalal, wai taga abunda ban ganiba, Kina son Jalal ne, Naja tazo suka hadu sukayi tayi, ni abun yabani mamaki iya sanina ko shiri bakwayi dashi amma maganganunta sun ban mamaki "

Jalila tayi ajiyar zuciya tace

"Nana kyale ta aikinyi ne bata dashi, kinsan tun asalina yarinyar nan batayi min ba, shiyasa take neman masifa, nime zanyi da wani Jalal, ai Jalal se ita makakkiya itama din ba Auren ta zeyiba, ki manta da ita zan dawo ai daidai nake da ita ai"

Nana tace "Hmm Jalila kenan, inaji kaman kina boyemin wani abune, amma inba rami meyakawo rami? Shikenan dai sekin dawo din, ki gaida min Hanan dan Allah 🙏"
Nana ta kashe wayarta, Jalila ta kalli Hanan a salube,
"me Nana take nufi?" dan daga mata gira Hanan tayi tace
"Queen kenan, naga kin damu da abunda Ilham tayi, amma keda bakyasonsa meyasa kike son abunda yafito daga hannunsa haka har kikejin babu dadi?"

"Hanan bansan mezan gaya miki ki yadda dani ba wallahi, Hanan Al'qurani abune me girma, sannan inason sanin meye Jalal ya ajiye tsawon lokaci ni banganiba, sannan muddin ina raye Wallahi sena nunawa Ilham iyakar ta"

"to meye na wannan tada jijiyoyin wuya haka easy queen i know you can do it, amma meye next plan dinki akan Jalal, kina ganin tafiyarsa Dubai akwai Alkhairi kuwa?"

"To yatafi uwar Dubai mana, daga nan yatafi bangon duniya idan yanaso? Ke nagama abunda zan iya akansa kowa tasa ta fishsheshi, dama yace ina takura masa kinga se yaje yayi abunda ya gadama, nima takaina nake, yatafi bayan duniyama yaje ya bude gidan giya in yanaso"

takarasa fadin haka tana kokarin kwanciya
Hanan tace
"karya kike tawajena, nasan halinki kaf Jalila yanzu kina jin wani abu ze sameshi zaki kuma tashin hankalinki, kya gama zagaye zagayenki ne"
Banza Jalila tai mata ta ja bargo ta shige, Hanan tai murmushi itama ta kwanta.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now