ABDUL JALAL (2020)

279 19 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 37

PART 1
Share please

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
ABDUL JALAL NOVEL FANS
Love u all guys ❤❤❤❤❤

-MY FIRST NOVEL-

Karewa Jalila kallo tsaf Hannah tayi, ta tabbatar Jalila Sa ar kanwarta ce, badan kartayi karyaba setace kanwa ta biyu ma, bude motar tayi sannan ta fito ta kalli Jalila sama da kasa, ta danyi murmushi sannan tace
"Ni kike kora kike cewa in tafi in bar nan gurin"
"Au tambayata ma kike, lallai na fuskanci saboda irinku ake double period a class, saboda ba kwa dauka a daya"
Mamakine yacika Hannah, tace
"Bari in gaya miki wani abu dabaki saniba ni.....
Jalila ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu tareda fadin
" NO need saboda babu wani abu me amfani ko me mahimmanci Wanda ze amfaneni dazaki fada, as I said it before, kibar nan gurin in ba hakaba zan baki mamaki"
"Ni Hannah zaki bawa mamaki"
"Kwaraikuwa kedin"
Nuna Jalila tayi da Dan yatsa zatayi magana, batayi maganarba Jalila tasa hannu ta sauke yatsan Hannah
"Duk wata magana muyita amma ba a nunani da Dan yatsa, daga haka nagama magana dake, nabarki lafiya, inkin gadama kicigaba da tsayuwa"
Jalila na zuwa nan a zancenta ta shige gidansu Jalal tabar Hannah tsaye sororo tana mamaki
Jalila ta shiga cikin gidan da sallama, Ilham tana palourn tana danna waya tayi mata banza, Jalila ta kuma nanata sallama amma Ilham mirsisi taki amsa sallamar Jalila
Karasawa Jalila tayi tasa hannu ta fizge wayar hannun Nana
"Haba kekuwa, kome nayi miki a rayuwa be kyautu inyi sallama kimin banza ba"
A fusace Ilham ta kalleta
"Bani wayata malama"
"Kiramin mummy, seki karbi wayarki"
"Ke kin isa kisani aiki,"
"Ban isaba alfarma na nema"
Sannan ta bawa Ilham wayarta,
Ana haka mummy tafito da alama unguwa zata fita
Suka gaisa da Jalila, Jalila ta gayamata Aiken da akayi mata, mummy tace taje yanzu fita zatayi in ta dawo zata aiko,
Da haka Jalila ta fito ta tafi gida,.data fito ta tarar Hannah ta tafi, Jalila a ranta tace kin kyautawa kanki dakika tafi ai
Hannah tana barin gurin takira wayar Jeje ta tambayeshi ina zasu hadu yagaya mata, ta nufi gurin kai tsaye, tana zuwa ko tasameshi a can, yanayin fuskarta kawai ya nuna masa akwai matsala, saboda yadda take huci
"Me idon zinare, lafiya kuwa"?
" ina fa lafiya, gidansu Jalal naje, saboda yan kwanakin nan baya daga wayata, naje nasamu wata a kofar gidansu, wata yarinya taci min mutunci"
"Kamarya taci miki mutunci, miye hadinki da ita?"
"Ina kyautata zaton itace budurwar tasa, da Jawwad yake fada Ilham take kowa, hada cewa bazata bari ya fito ba, sedai injira muhadu inda mukasaba"
"Jalal din, to karya takeyi barazana ce kawai, uwar da ta haifeshi ma bata isa ta hanashi abinda yyi niyya ba, balle wata Ilham, gayen da soyayya bata gabansa, kema kinciri tuta ne da yake sauraronki, amma ya akayi kika San Ilham dince"?
"Na tambayeta amma ta rainamin hankal, Amma nayi mamaki, yanda nake zaton Ilham din na dauka wadda zanyi maganice a take amma naga itama a tsaye take Dan bata da kunya"
Dan shiru Jeje yayi sannan yace
"Tabbas Ilham ma masifaffiya ce amma bana tunanin ta kai yadda kike fada haka"
"Hmm, bakaga wulakancin datayi minba kuma na girmeta, sena raina rashin kunyata Dan fafur hanani magana tayi, mamaki da takaici suka cikani"
"Gaskiya Hannah kin bani kunya duk bakin naki, kinsan a duniya Jalal ya tsani mace ta dinga juyashi"
"Ba a nan takeba Jeje hausawa kance yaki Dan zamba ne Dan haka, zan nuna mata duk Wanda yarigaka kwana ze rigaka tashi, idan takamarta rashin kunya, nikuma takamata bariki, zan daga shi har ita zan basu mamaki"
Jalila ta sanar da Abba zuwan captain Rasheed da yayansa domin kawo musu ziyara, Yaya farinciki sosai da jin haka, Jalila ji take kamar ta janyo ranar Saturday su Hanan suzo, se murna takeyi
Daren yau dai Jalal yasaci jiki ya tafi gurin shan giyarsa, yaje babu dadewa be fara shaba, mayyar tasa tazo wato Hannah, tazo ta nemi guri ta zauna tai shiru batace komaiba
Ya Dan kalleta, yanayin fuskarta ya nuna tana cikin damuwa,
"Ya akayine sarkin matsala, mekuma ya faru?"
Ta dago ta kalleshi, tayi kalar tausayi sannan tace
"Jalal kwana nawa ina kiranka kaki ka daga wayata, naturomaka messages kaki reply haba Jalal, gashi aka cimin mutunci saboda kai, yakamata ka tausayamin"
"Ya akayi aka cimiki mutunci sabodani?"
"Kanwarka mana"
"Wake nan?"
"Wace kanwar kake da ita, banda wadda Jawwad yacemin tana Sonka?"
Shiru ya danyi yana kallon Hannah, tacigaba da magana
"Ranar nakiraka baka dagaba, ita ta daga ta min rashin mutunci ni kana cemin Mara kamun kai amma me kanwarka take a gurinka shabiyun dare, har tana gayamin bacci kake ta zageni hadda cemin mayya"
Shikam Jalal kasa cewa komai yayi se ido da ya zuba mata,
"Har yanzu ni banga cin mutuncin dakike fada tayi miki ba"
Kallonshi tayi
"Au hakama zakace? Metakeyi a gurinka shabiyun dare harta daga wayarka?"
"Meye kuma na bin diddgi ina ruwanki dame take a gurina shabiyun dare?"
" haba Jalal,Yauma nakasa jurewa da rashin ganinka Dan haka naje gidanku, na hadu da ita a kofar Gida daga tambayar kana ina ta dinga zagina
Harda cewa baka isa tahanaka abu kayi ba Dan haka bazata bari ka fitoba, saboda baka tsallake maganarta, tana juyaka yadda taga dama, haka ta dinga fadar maganganu, abun ya dauremin kai"
Dan dagowa yayi da sauri
"Inji Ilham din?"
"Eh mana, ni babban bakin cikina yadda ta dinga gayamin miyagun maganganu saboda kai, wallahi Jalal ba Dan kanwarka bace senasa ankoyamata iya magana, harni zata cewa mutuniyar banza? Ita ma ai ta banzarce tunda zata iya zuwa dakinka shabiyun.......
" Enough malama, karki kuskura ki zagi kanwata, kuma wallahi duk abunda yasameta a kwanan nan kikuka da kanki, Ilham ba mutuniyar banza bace, ni shedane, ki kiyaye baki isa ki zageta a gabana ba, and then zanje gidan in sameta, zatayi bayani"
Yana zuwa nan ya tashi ya tafi yabar Hannah baki a bude, saboda mamaki se yanzu takuma tabbatarwa kanta tsawon wannan lokacin, har yanzu Jalal be fada tarkon sonta ba kenan tunda har ya fifita Yar uwarsa akanta kenan ya fara son Ilham, amma ko ba komai tasan abunda ta fada din nan ze tunzirashi, gaba dayanku, sena nuna muku ni gogaggiyace a bariki

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now