ABDUL JALAL (2020) 7

339 22 0
                                    

..🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

    _ABDUL  JALAL_

      _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
    (Daddy's girl)

               PAGE-  7

PART 1

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680

Is a free book

I want comments not stickers😢😢😢😢
Comments dinku  shine kwarin gwiwata

       _My first novel_

Aimin afuwa
Today's page isNot Edited

"To wai Yaya mairo me kikeso inyine  yaje ya taho da ita yace anan zatayi Hutu to korarta kikeso inyi ko kuma yazanyi
Kinsan halin Abban su Jawwad yanason Dan uwansa akan yarinyar nan beki yamin wulakanci ba"
Maama tayi maganar cike da damuwa

"Seki hade mata fuska yadda nan gaba in ance tazo miki Gida bazata zo ba akan me azo akoyawa yaranki dabi'un arna kinsan ba kunyace dasu ba har kibarta da danki su kwana daki daya da yarinyarki"

Jikin Jalila a sanyaye ta saki handle din kofar ta koma da baya idanunta na zubda hawaye bazata iya cigaba da jin wannan miyagun maganganun da cin fuskar ba

Wai itace dangin arna ababen kyama to shikenan su arna ba mutane bane

Kaman wadda kwai ya fashewa a ciki haka taja kafarta ta nufi dakinsu ta shiga ta tarar Nana da wata budurwa wadda batafi sa'arsu ba (wadda sukazo da yaya mairo)
sallama tayi a hankali

Nana na ganinta ta mike ta rungumeta
"Oyo yo Jalilana sannu ya jikin"

Murmushin dole Jalila tayiwa Nana Wanda iyakarsa bakinta "
da sauki Nana nasaku wahala sannuku Nagode"

" shhhh meye kuma wahala anan bana son irin wannan zancen gaskiya babu haka a tsakaninmu"

"To na dena Ashe bakuwa kikayi"?
" baki ganeta ba Sa'ada cefa Yar gidan Anty mero"

"Eyya banganeta bane sannunki"
Jalila tafada
Sa'ada ta Dan dubeta a yatsine "yawwa sannu"

"Nana bari in Dan watsa ruwa"

"To a fito lafiya kiyi a hankali inda wani abu daba zaki iya ba kimin magana " Nana tafada cike da kulawa

"Karki damu zan iya komai da kaina"

Towel ta dauka ta shiga toilet dayake toilet din a cikin daki yake

Tana shiga bandakin Sa'ada ta gyara zama cike da gulma

"Ke Nana yanzu Dan Allah wannan danginsu arna ne?kuma kike zaune tare da ita ko kyamarta ba kyayi?"
A fusace Nana ta kalleta
"Mene haka Sa ada ina ruwanki?
Waima tukuna ubanwa yagaya miki haka karki karamin irin wannan maganar bana so" Nana tai maganar a fusace

"Daga fadan gaskiya se ki kama min jaraba, ai dai kinsan mamanmu bazatayi karya ba ke Yar uwata ce bazanso kishiga wani hali ba ni warin arna ma naji tanayi"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now