ABDUL JALAL (2020) 43

337 13 1
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 43
PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.
Ina me neman afuwarku masoyana, kwana biyu banyi typing ba wayata ta dan samu matsalane
Sannan ina kuma neman afuwarku bazan samu dinga yi muku posting kullum ba saboda zan koma lectures online, Nagode da kulawa

_My first novel_

Jalala ya karaso inda suke, ya kalli Jalila, "kina kuma marinta kema sena mareki, mara kunyar kawai, Ilham sa'arki ce?"
Wani banzan kallo Jalila tayi masa
"Ilham din banza Ilham din wofi, wallahi ta kuma zagina sena kuma wankamata mari dama Jakace kaima kasaba jibgarta, sha3 Karya banza
Mamakine ya cika Ilham wai ita yake tarewa fada, kallon Jalila tayi
" Kece babbar karya baniba"
Jalila tace "kinga karnuka nan" ta nuna Ilham da Jalal,
Ilham tace "Nida yaya Jalal dinne karnuka"
Tsaki Jalila tayi, ta shige ciki, ta hankado kofa, Ilham ta kalli Jalal
Zatayi magana kawai yai tafiyarsa, yabar gurin dama dan ya kuma kunna Jalila yayi, ba nufinsa ya shigarwa Ilham ba, suka batta a tsaye baki bude
"to me suke nufi da hakan?"
Babu me bata amasa dan haka ta juya ta koma gida, se bayan sallar isha'i sannan su Nana suka dawo, Nana tai tabawa Jalila hakuri akan sun tafi sun barta ita kadak, Jalila ta nuna mata bata damu ba, tun ranar da Yaya mairo tazo tayi wannan cin mutuncin Jalila bata kuma bari sun hadu da Jawwad ba, ya damu sosai ko wayarta inya kira bata dagawa, ko palourn ma ta dena fitowa se dai ta zauna a daki,

Yau ta tashi da murnar ummi zatazo, amma haryanzu ba saki jikinta ba abunda su Yaya mairo sukayi mata yana taba mata zuciya, sannan idan ta tuna ummi tafiya zatayi ta barta a gidan, setaji ba dadi,
Nana da halima ne sukayi wa Jalila kara sukayi girki domin tarbar ummin Jalila, amma ita kam ko san fitowa batayi, seda Abba yasa aka kirata ya tambayeta ko akwai matsala kwana biyu baya ganin gilmawarta, amma tace masa ba komai, Jawwad ma yayi sintiri a cikin gidan amma baya samun ganin ta, gashi yana tsoron yaje dakinsu Jalilan, saboda Maama, in yakira Nana yace tabata wayar se taki karba, Jawwad ya damu sosai
Karfe sha biyun rana ummi ta iso gidan, Jalila kaman ta shige cikin ummi dan farin ciki, tayi murna matuka, Abba yana gidan saboda zuwanta, Maama dai ba yabo ba fallasa ta tarbeta saboda idon Abba, Jawwad ya shigo domin gaida ummi, se lokacin yaga Jalila, ta dan fada idonta yayi zuru2 tana manne a jikin ummi, tausayinsune yakama shi, suka gaisa da ummi, daga nan ya shantake akayi ta hira, ya tashi ze fita ya waigo ya kalli Jalila yace
"Jalila, dan Allah kawomin coffee"
Abba yace
"Yayana kafiye takura, tana zaune tana jin dumin ummin zaka sakata aiki, murmushi Jawwad yayi yana dan sosa keya, Maama kam wani mugun harara tayi masa, suna hada ido da Maama ya sunkuyar da kansa kasa, ummi kuma tace
" Ai ba wani takura dan yasata aiki, ai kanwarsa ce, tashi ki kaimasa"
Jalila ba dan tasoba ta mike taje ta hado masa, ta fita domin kai masa, Maama a ranta tace "lallai Yaron nan, wato beji maganar da mukayi masa ba kenan?, aikuwa sena saba masa"
Jalila tana kaimasa, ta ajiye ta juyo zata fice Jawwad ya kira sunanta
"Jalila" cak ta tsaya amma taki yadda ta kalleshi,
Tasowa yayi yazo gabanta ya tsaya, suna iya jin numfashin juna, muryarsa a sanyaye yace, "Baby menayi miki na cancanci wannan hukuncin? Kin kauracewa ganina, tsawon kwana biyu, kinki daga wayata, kinsani cikin damuwa, Baby why?"
Dan dagowa tayi ta kalleshi, idonta sun ciko taf da hawaye, ta sunkuyar da kai, kallonta yayi ya kuma sassauta muryarsa
"Ohhh no Baby, nagane, Jalila you are not suffering alone, i also feels what you feel, Baby dan Allah kiyi hakuri akan abunda akayi miki, kar hakan yasa ki kuma, kauracemin kwana biyun nan na shiga damuwa, sannan kidena zubar da hawayen nan, banaso, kuma in Ummi, taganki cikin damuwa bazata ji dadi ba"
Gaba daya jiknta yayi sanyi, duk yabata tausayi, ta gyada masa kai alamun ta gamsu da maganarsa
"Kindena kukan?"
Ta gyada masa kai, ya ciro handkechief a aljihunsa yabata, ta goge hawayen da yake idonta, ta mika masa, sannan ta fito, ta koma cikin gida,
Ta tarar ummi tana cin abinci, spoon ta dauka tazo ta zauna, suna ci da Ummi,
Zuciyar Ummi fal tausayin Jalila, akwai abunda yake damunta, amma taki fada mata,
Nana ta fito taga Jalila da ummi suna cin abinci tare, ta kalli Jalila
"Wato dan ummi tazo shine, yau bazaki ci abinci dani ba?"
Dan murmushi Jalila tayi, wanda iyakacinsa lebenta
"Ni na isa, Nana"
"gashi nan makuwa nagani"
Ummi ta kallesu tana murmushi
"kema dakko spoon dinki, kizo muci"
Haka kuwa akayi, suka zauna suna cin abincin tare
Ummi tagayawa Abba, kwana daya zatayi, ta wuce,
Maama ta shige daki ta kira Naana, ta hanata fiyowa, karshe ma ta aiketa tabar gidan, ta bar Ummi se Jalila da Halima, dakinsu Jalila taja Ummi, ta dinga mata magiya ta tafi da ita, amma Ummi tace mata baze yiwuba, Yanayin yadda taga Maama ta karbeta, tasan akwai matsala amma Jalila tace komai lafiya kalau suke zaune
Haka Jalila sukai ta hira da Ummi wanda hakan ya rage mata bacin ran da take ciki ,
Rabin hirarsu da Ummi, Nasiha ce take mata akan hakuri da karbar kaddara a duk lokacin datazo mata,
Da dare yayi ma Maama cewa tayi Nana ta kwana a dakinta, tabar musu can, dan bazata kwana a gurinsuba bata san me za a koyamata ba.
Washegari tunda safe Ummi tafara shirin tafiya, tun wayewar garin Jalila take kuka, ko karyawa takiyi, karfe goma na safe, Ummi tagama shirinta tsaf ta fito, Jalila janye da trolley din Ummi tana share hawaye, Nana kuma ta dakko karamin jakar Ummu, hakan yayi dai2 da fitowar Abba wanda shi zeje yasa Ummj a motar garinsu, Abba yace a kirawo Maama suyi sallama da Ummi, Maama ba dan tasoba ta fito, sedan kar Abba yayi mata fada,
Abba ya kalli Jalila yace "Baby muje, asaka kayan a mota" Jalila tayi gaba ita da Nana, ya bisu a baya, suna zuwa harabar Gidan, suka tarar da Jawwad ya kunna motar ya bude kofofin, suna zuwa yaje ya karbi trolley din hannun Jalila yana kokarin bude boot
Ummi ta kalli Maama da take tayi mata kallon banza, ta danyi murmushi sannan tace
"Zainab har yanzu ina ganin kiyayyata a idonki, bansan dalilin hakan ba, amma ina rokonki ga Jalila nan amana, kar kiyayyata ta shafeta, ki dubi Allah ki dubi maraicinta, in kikaci amana Allah yana kallonki, badan wasiyyar mahaifinta ba Zainab, babu abunda zesa in bar yata a gidanki, tunda nasan ba kya kaunarta, keda danginki, da da ita zan tafi, ko ina ne" Maama ta katseta ta hanyar cewa
"kinga saurara, amanar yarki a hannun dan uwan mijinki take baniba, dan ba muhada dangin komai dake ba, ni ban hada jini da arna ba balle abani amanarsu in karba"
Murmushi Ummi tayi me ciwo sannan tace"shikenan Zainab ki fadi abunda kikeso, kema kin haifa, bazan fasa fada ba Jalila amana ce, zan iya yafe duk abunda zakiyi min amma banda cin amanar gudan jinin Aliyu, wato Jalila " Ummi na zuwa nan a zancenta tayi waje tana share hawaye, tareda tausayin tilon Babyn ta.
Harabar gidan ta fito, suka koma gefe, da Abba suna magana, Jalal ne ya shigo gidan, ya hangi Ummi yana ganinta ya karaso da sauri yana murmushi, yace
" Ummi saukar yaushe"?
"Abdul Jalal haka ka girma, Jalal ka yadani, ka manta dani"
Ya dan girgiza kai
"ummi wane ni in manta dake ni na isa, yanzu kikazo ne?"
"A a tafiya zanyi, tun jiya nazo"
Kallon Jawwad yayi, sannan ya kalli Ummi
"Ummi Jawwad be gayamin ba danazo mun gais, yaushe rabon da naganki"
Abba yace "Lallai Jawwad baka kyauta ba tunda baka gaya masa ba"
Jawwad yace "Abba ba laifina bane jiya throughout ban ganshiba, ban san inda ya tafiba"
"amma lambar wayata ma baka ganta ba itama ta tafi yawon"
Jawwad yayi dariya
"Allah yabaka hakuri"
Jalila mamaki takeyi yadda ya ke girmama Umminta haka, yasan Ummi kenan, amma ranan datayi mata zancen waye JALAL tace mata bata saniba
Ummi tace "Abdul Jalal ina Mummynka?"
"tana nan Ummi, yanzu nan ta fita", daddy kuma baya gari,"
Ummi tace Allah sarki, dan Allah a gaishesu
" zasuji Insha Allah Jmmi"
Jalal ya kalli Abba yace "Abba ka bari, semu rakata"
Abba yace masa "ai ba kano zata koma ba, tasha zasu kaita, zataje garinsu"
"Ba komai Abba, bari mu kaita"
"to shikenan yarona, karbi mukullin"
Jalal yasa hannu ya karba,
Seda Jalila ta zare ido, ko dai Abba besan irin tukin da Jalal yake ba, yabashi mukullin motarsa
Abba suka gama maganar dazasuyi da Ummi, Jalila da Nana suka shiga bayan motar, sannan Ummi ta shiga,
Jawwad kuma ya zauna a gaban mota, sekuma Jalal da zeyi tuki
Suna tafe Jalila tana kuka, Nana, da Jawwad suna rarrashinta yayinda Ummi ta maida hankalinta kan JALAL sunata hirarsu, bawai dan batajin kukan Jalila ba sedai kar garin rarrashinta itama tayi kukan,
Ummi tace "Jalal ya karatu fa?"
Yace"Ummi kicigaba da yimin addu'a, very soon zakiji labari me dadi"
"to Allah ya tabbatar da alkhairi, yabaku mataye nagari kuyi aure"
Dariya Jalal yayi "Aure kuma Ummi"
"Eh mana Jalal, aure ai shine cikat mutum"
"ko ba hakaba Jawwad"
"hakane Ummi"
Jalal yai murmushi, tareda dan girgiza kai,
Haka suka cigaba da tafiya, har suka je tasha, Jalal hira suke da Ummi, aka samawa Ummi mota, suka saimata ticket, Rirriketa Jalila tayi tana kuka,
"Ummi dan Allah kidawo da wuri, karki tafi ki zauna Ummi"
Ummi ta dan goge kwalla tana dan dukan bayan Jalila, alamun rarrashi, sannan ta kalli su Jawwad
"ga sister dinku nan, asaka ido akanta, kuyi hakuri da halayenta, dan Allah,"
Nana tai saurin cewa "Ummi karki damu, Jalila bata da wani damuwa, lafiya kalau muke zaune"
Jawwad ma yace "ummi karki damu shagwaba nsme kawai takeji, shiyasa take kuka, amma ba wani damuwa," murmushi Ummi tayi sannan ta dago Jalila tace
"Baby na is ok, bazan dadeba zan dawo insha Allah, zamu dinga waya, Baby kiyi hakuri da rayuwa, sannan kizama me hakuri da kaddararki, kizama me yafiya da kauda kai, akan al amuran rayuwa, banda tsokana da neman magana duk abunda yasameki kiyi tawwakali ga Allah kinji baby"
Gyada mata kai Jalila tayi
"Yawwa Allah yayi muku albarka, ya hada kanku gaba daya"
Jawwad yace "Insha Allah Ummi" Ummi ta kalli Jalal "Abdul Jalal ni zan tafi, Allah ya jishemu alkhairi, in ka koma makaranta, a ko bikin yazo kar a manta dani"
Dariya yayi yace "Hajiya ummi, kidena batun auren nan fa, zan karbi lambarki gurin Jawwad mudinga gaisawa"
"to shikenan ku koma haka nagode sosai,"
Ta dan rungume Jalila tai kissing dinta a goshi
"kidena kuka, addu a zakiyimin"
Daga haka Ummi ta shige motar
Jikin Jalila a sanyaye, suka koma motarsu suka dau hanyar gida,
Jawwad se bawa Jalila baki, yake kan tayi hakuri amma kaman yana zigata, ta kwanta akan cinyar Nana, se kuka take,
Kukan Jalila ne yacikawa Jalal kunne, ya samu guri, yayi parking, sannan cikin tsawa yace "dallah Malama ki rufewa mutane baki, se wani lallabaki ake kina cigaba da kukan, Wani abunne yasamu, Ummin dazaki dinga yiwa mutane kuka haka, in baki rufemin bakiba sena makeki wallahi"
Yadda yayi maganar seda hantar cikin Jalila ta kada, saboda cikin tsawa yayi maganar, Jawwad yace wa Jalal "dan Allah kayi hakuri ka kyaleta
" Bazan kyaleta dinba Wallahi ta cigaba damin kuka seta sauka, bana son shirme"
Nana tace "Yaya Jalal dan Allah kayi hakuri, tadena, Jalila dan Allah kiyi shiru"
Banza Jalila tayi musu, amma ta rage sautin kukan, da kyar Jawwad ya lallabashi, yaja motar suka tafi,
Bayan sun koma gida Jalila kaman wata marainiya, abun duniya duk ya dameta.
Halima ta lura da damuwar da Jalila take ciki, dan haka Halima taita rarrashinta
"sayyada Jalila dan Allah ki saki ranki, gidan ba dadi in bakya walwala, Ummi zata dawo fa"
Jalila ta danyi yake
"leemart baki san yanake Jiba, wallahi zuciyata ba dadi"
"Nasani Jalila, amma kiyi hakuri, damuwa ba shine mafita ba"
"hakane nagode"
"yawwa kisaki ranki"
Jalila taita kiran Ummi tana tambayarta ko ta karasa, Ummi tace mata in taje zata kirata,
Hakanan Jalila taji hankalinta yaki kwanciya, bayan la'asar ta kuma kiran wayar Ummi amma taki shiga, da farko tayi tunanin ko network ne amma wasa2 har karfe tara na dare wayar Ummi a kashe, hankalinta ya tashi matuka,
Nana tace "dan Allah Jalila ki nutsu ki kwantar da hankalinki, maybe bata da cajine"
"Nana cewa kike in kwantar da hankalina, ta yaya? Dazu fa muka gama waya amma ace yanzu wayar bata shiga"
"To kika sani ko network ne, kinsan hanyar, akwai dazuka, dan haka ba lallai asamu Network ba" da haka hankalin Jalila ya dan kwanta,
Amma har gurin karfe sha biyun dare, Jalila takasa hakuri trying lambar Ummi ta kumayi, amma still switch off
Jifa Jalila tayi da wayar ta fashe da kuka

Share please
More Comments More typing...............................

Aimin afuwa rashin samun posting da wuri, ina busy ne sosai
Amma ina godiya da addu"oinku

🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now