ABDUL JALAL 64

348 19 1
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 1️⃣1️⃣64_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com


_MY FIRST NOVEL _

Kallo daya tayi musu ta dauke kanta ta wuce cikin dakinsu, itakanta Maama seda tasha jinin jikinta dan gani take kaman Jalila taji abunda tace, tashi Jawwad yayi ya fice, yayinda Nana da sauri itama ta mike da nufin bin bayan Jalila amma Maama ta hanata ta hanyar cewa "Ina zaki? Karki sake Kibi ta mayya"

haka Nana ta hakura tafasa bin Jalila. Jalila tana shiga dakin tai jifa da jakarta da hijabinta akan gado ta zauna ta fashe da kuka me tsuma zuciya, dama tsanar da Maama take mata harta kai taci mutuncin mahaifinta haka shida baya doron kasar tsawon shekaru, ga kazafi datakeyi wa uwata, menayiwa wannan matar hakane meyasa ta tsaneni?, banda albarkacin Abba dasu Nana da matar nan itada zuri'arta suka ganni se sun canza hanya "zamana a gidan nan baze yuwu ba, bazan cigaba da jure cin zarafin iyayena ba musamman uwata ba dan kawai tubabbiya ce gara inshiga duniya, to amma inna tafi Jalal fa?
Tayi shiru tana tunani Tabdijan wallahi matar nan tahana Jawwad aurena bata isa ya auri wata Naja ba, in ita Maaman bata san wacece Najaba to nina sani, Jawwad kuma dan uwana ne, intace baze aureniba baze auri Naja ba wallahi, bazan zauna a kasheni da bakin ciki ba, ta karkashin kasa zan fara ramawa nagaji" "Enough!!!!" Jalila tafada da karfi idonta duk hawaye, guri ta nema ta kwanta hawaye na cigaba da bin gefen idonta to Jalal dinme ma? Nagaji tafiya zanyi sena bar gidan nan wallahi nagaji da wannan abun da akemin, hijab dinta tasaka ta mike tsaye.

Nasihar ummi ta dinga tunowa wanda take yawan yi mata akan hakuri da rayuwa dakuma karbar kaddara a duk yadda tazo mata, komawa tayi ta zauna ta fashe da kuka me ban tausayi.

Jiki a sanyaye Jawwad yayi sallar magariba, gaba daya yarasa abunda yake masa dadi, Jalal ne ya shigo dakin da sallama, amma sam Jawwad bejiba hankalinsa baya jikinsa, dafa shi Jalal yayi cikin damuwa yace

"Jawwad lafiya kuwa? Meyake damunka kake tunani haka?"

Ajiyar zuciya Jawwad yayi, ya danyi shiru na wani lokaci sannan yace "Jalal ina cikin damuwa, narasa me yakamata inyi"

"gayamin meya farune?"

Nan Jawwad yagaya masa komai sanna ya dora da cewa

"Jalal babban damuwana shine cin zarafin da Maama tayiwa iyayen Jalila ina kyautata zaton Jalila taji abunda Maama tace, amma ban tabbatar ba, data shigo ba wanda ta kula a cikinmu, wallahi bana zaton zan iya auren Naja bazan iyaba wallahi"

Shiruu Jalal yayi, "Jawwad a duk lokacin da aka ci zarafin Ummi, har cikin zuciyata nakeji, raina yana baci, bana manta Alkhairi Jawwad, idan har a matsayinmu na hausawa zamu cigaba da aibata wanda suka karbi Addinin musulinci daga baya to tabbas wanda ba musulmi ba zasu dinga kyamatarmu da addininmu, Jawwad kayi hakuri, amma mahaifiyarka da yan uwanta basa kyautatawa, dukda ina gefe ina fadar rashin kunyar yarinyar nan bazan mata sharri ba tanada matukar biyayya, wanda dayawa aka haifa a musulincin basuda ita, kuma itama ai a musulinci aka haifeta, Ummi mace ce me karamci da ilimi riko da Addininta yasa ta baro iyayenta gidan jin dadi ta dau shekaru ba tareda ta waiwayesu ba, soyayyar datakewa mijinta da 'yan uwansa ce tasa nima naci Albarkacinku, Jawwad mahaifiyarka bata kyauta ba, kuma zigata akeyi amma kasani gara wanda ya tuba daga baya akan abunda yayar mahaifiyarka take aikatawa"
da sauri Jawwad ya kalleshi yana kokarin yayi magana, Jalal yace

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now