ABDUL JALAL 75

322 17 2
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

              _ABDUL JALAL (2020)_

       _Story and written by_
      AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
        
   PART 2        
                          _PAGE  2️⃣2️⃣75

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

     
          
         

              _MY FIRST NOVEL_

Akayi gagarumin shagalin suna, dangin Habib sunje Suna, hakama dangin Khadija da abokan Arziki, dangin Habib sunji dadin saka sunan mahaifin Salma da Habib yayi. Dangin Habib sunyi bajinta, inda suka dinga bawa ABDUL JALAL kyautuka, abunka da masu dukiya, aka dinga mallakawa ABDUL JALAL kadarori, kasancewar shine jika daga bamgaren namiji da aka fara Haifa.

bayan kowa ya watse da daddare Habib ya shigo amma tundaga harabar palourn khadija yake jiyo kukan ABDUL JALAL, da sauri ya shiga ya tarar da dattijuwar da'aka kawo dan kula da khadija rungume da jariri yanata kuka, ya karasa yasa hannu ya karbeshi yace

"lafiya kuwa Baba? Ina khadijan take?"
Cikina girmamawa tace "Yallabai tun dazu ta shige daki bata bude ba yanata kuka"
Dakin khadija ya nufa da sauri, yana zuwa yajita a rufe yai magana amma taimasa banza, ya dade yana bugawa taki budewa, dakinsa yaje ya dakko key yazo ya bude, amma abun mamaki ya tarar da khadija kwance akam gado tana dannan waya

"khadija meye hakane? Kinajina ina bugu kikaki budewa dan wulakanci, tun dazu Jalal yake kuka, amma kinshige daki kin rufe kofa me kike nufine?"
Mikewa tayi zaune tace "yawwa anzo gurin, tunda kuka yakeyi seka daukeshi kakaiwa Salma ta shayar dashi tunda sunan babanta kasamasa, akanme Zakasawa dana sunan baban Salma, nibani da ubane koban cancanci kamin karaba zaka sawa dana sunan uban wata"

"Ya isheki haka, mahaifin Salma mahaifinane, yamin komai a rayuwata, kuma da nawane basenayi shawara da kowaba zan saka masa sunan danakeso"

"kai yaiwa wahala baniba, kuma tunda dankane kana da ikon samasa sunan daka gadama haka kake da ikon shayar dashi, ai kaima akwai abun bashi a jikinka seka bashi ai" ta juya tai kwanciyar ta, mamakine yacika Habib be taba zaton khadija zatayi haka ba, yayi juyin duniya amma taki saurararsa shida dansa, Jalal ya dinga kuka, haka ya fita a daren yasamo madarar shanu me dumi yakawo aka bawa Jalal sannan yayi bacci koda gari ya waye bata canza zaniba dan kin shayar da Jalal tayi, abu yakici yaki cinyewa, yaje yagayawa yayanta, dan yasan mahifiyarta bazata sataba bazata hanata ba, yayanta yazo har gidan yaita mata fada yaci mutuncinta sannnan ta yadda tacigaba da shayar dashi.

Se lokaci2 inta ga dama take shayar da Jalal inkuwa Habib baya kasar seta wuni bata bashiba haka ze wuni yana kuka sedai wannan dattijuwar taita hada madara tana bashi ta goyashi taita rarrashinsa. Bayan kwana Arba'in dattijuwar nan ta tafi, khadija tace se a samo wata ta dinga rainon Jalal dan ita bazata iya da wannan yaron me kukan tsiya ba, haka akayi akasamo wata mata, take kulada Jalal, A haka Jalal yakai wata bakwai khadija tace yayeshi zatayi, Habib yace tabari ko shekara daya yayi seta yayeshi amma tace batasan zancen ba, a wata bakwai din nan zata yayeshi, haka kuwa tayi watan Jalal bakwai ta yayeshi, Jalal be wani shaku da itaba yafi shakuwa da wannan matar, me rainonsa wato Habi sekuma daddynsa, jefi2 in khadija ta dauki Jalal tana son yaron amma intatuna da yanzu tayi nisa a karatunta amma yakawo mata cikas ga sunan da aka samasa duk se haushi yakamata.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now