ABDUL JALAL 103

1.6K 23 1
                                    

..🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣0️⃣ 103

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

_MY FIRST NOVEL _

Da Sauri Mummy ta sha gaban Daddy tace

"Wallahi Habib seka gayamin dan me zaka yiwa Jalal Aure ba tareda nasani ba? Sannan kuma 'yar ubanwa aka Aura masa? Wato kaje kun haďa kai da wannan munafukan' yan uwan naka aka Aurawa ďana yarinya ban sani ba, to wallahi baze yuwu ba, ďa dai nawane nina haifi abuna, dan haka ba'a isa a yanke masa hukunci game da rayuwarsa ba tareda sani na ba"

"sekuma kiyi, naga yadda zaki raba Auren ai, indai Jalal ne gaki nan gashi, dai dai yake dake, Akan kirabashi da yarinyar nan zaki kuma lalata alakarki da shine kawai, dan nagaya miki yana sonta"

"karyane Wallahi, Jalal bashi da wata yarinya da yake so, Yarinyar dana zaba masa, ita ze Aura"

Dama daddy yasan ze fuskanci wannan kalubalen daga matar tasa, dan haka ya ture ta daga gabansa yabar mata palourn.

Se magariba Su Jalila suka isa garin maiduguri, koda sukaje sun gaji sosai, musamman su Jalila, su da suka sha hidimar biki, basu huta ba akayo wannaan uwar tafiyar.

Gaba daya Jalila ji take jikinta kaman ba nata ba saboda gajiya, har suka je maiduguri kanta a kasa yake, se dai ta jingina da jikin Nana, ko mota tayi bacci, in aka jima ta shige cikin mayafinta tayi kuka, har sukaje Jalila bata kula kowa ba seda taji an tsaya ance sufito.

Gidan da akayi parking din motar ne yayi awon gaba da tunanin ta, sekace ba a duniya ba, kallo daya zakayiwa gidan kasan mamallaka gidan sunyi hannun riga da talauci, ko da suka fito daga motar Se guďa akeyi, Jalal idonsa gaba daya yana kan Jalila da take a takure, Suka nufi cikin gidan, tun daga harabar gidan wani irin sassanyan kamshi ke tashi, har zuwa cikin gidan, cikin gidan da'a akwai mutane a gidan da sukazo domin karbar Amaren.

Cikin gidan ma kamshin da yake na musamman ne, fiye da na harabar gidan.

Aka basu ďaki, suka gabatar da sallolin da suke kansu, Sannan aka kawo musu Abinci, Jalila da Nana ne kawai a dakin dan haka Nana tace

"Jalila ki daure kici Abincin mana"
Girgiza kai Jalila tayi tace

"Na koshi, ke dai kici kawai, ni kaina kemin ciwo"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now