ABDUL JALAL 66

347 21 4
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 1️⃣3️⃣ 66_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com


_MY FIRST NOVEL _

Jalal bai fita daga motar ba, dayake motar tint glass ne, da mamakin Jalila motar data sha gaban tasu, Jeje ne a ciki da wasu manyan karti suka fito, suka tinkaro inda tasu motar take, knocking sukayi a side din direba, a hankali Jalal ya sauke glass sukayi ido hudu da Jeje, rikicewa Jeje yayi, cikin inda inda da mamaki yace
"J man kaine da kanka? huh ya gida amm...
"shut up please" Jalal ya katseshi cikin tsawa

"nasan za'ayi haka ai, shiyasa na shirya hakan, Jeje baka da amana, baka da mutunci, ko bataci darajar kowaba taci darajar yayanta amininane, amma saboda baka da mutunci shine ka shirya cutar da ita, kuma duk abubuwan data fada akanka karyane? Ba karya bane ba, Jeje inaso in maka kashedi, koda makamancin wasa ba kai babu ita, idan nakuma fuskantar ka shirya wani abu akanta na cutarwa, you know what am capable of doing, ka kiyaye"
Cikin marairaicewa Jeje yace

" haba Jalal kai ka dauki abun a haka amma ni banyi niyyar yimata wani abuba...

"Enough malam, kayimin blocking way, ku janye motarku zan wuce"

cike da bakinciki Jeje yasa aka janye motar, ya shirya ya dauke Jalila yaketa mata haddi, saboda abunda tayi masa, ya dauki fansa akan abubuwan datayi masa, ya akayi Jalal ya gane shirina haka, dukan motarsa yayi da karfi, yayiwa kartin umarnin su shiga mota.

Jalal ya kalli Jalila yace "kinga Abunda shishshiginki ya nemi ya janyomiki ko? Da kin bari kin taho ke kadai da wani zancen ake ba wannan ba" ya karasa maganar cikin fada, kallon Jalal tayi, ta dauke kanta cikin ko in kula tace

"waman yatawwakallu alallahi fahuwa hasbuh, dan haka be isa yayi min wani abu ba, kuma kaima baka isa ka kareni daga komai ba, ba gudu ba ja da baya wallahi koze kasheni seyayi nadamar niyyar dayayi akaina, kar ya fasa, zan nuna masa wacece ni duk Abunda nasa gaba Allah yana bani sa'a kansa, bana alwashi in kasa cikawa, duk wanda ya takaleni da sharri senaga bayansa, kodame yake takama, dan haka ba kaika kareni ba Allah ne, kuma ka gaya masa zamu gauraya dashi dan haka kadenamin tsawa"

Jalal yakara jinjinawa Jalila akan taurin kai, betaba ganin mace me taurin kai kamanta ba, bata da tsoro bata son raini, kuma abun mamakin she has a luck, kota gangamo rigima se Allah ya kwaceta.

Kallonta kawai yayi yai shiru bekuma cewa komai ba yacigaba da tukinsa, suna zuwa kofar gate ɗin makarantar yayi parking yace
"Fita"

"aiko bakace in fitaba zan fita, komeye nayimin gadara aiba motarka bace, kuma bani nace ka kawoni ba dan haka karka kara yimin tsawa" harzata bude motar, setaga wannan lecturer da Sir Hafiz ya kaita gurinsa wato Sir sagir yazo wucewa, da sauri ta kalli Jalal
"Yawwa kasan wancan mutumin?"
Kallo daya yayiwa sagir yagane shi, cousin din baban Ilham ne, shikuma meye hadinsa da ita oho, amma yace "ban saniba kifita nace"

"to kayiwa kanka dama sako yabani in baka, tunda kace haka shikenan" ta fice abunta Jalal ya girgiza kai yatafi.

Karfe tara na safe Ilham tana kofar gidansu Yaseera ta kirata awaya ta fito suka tafi gidan malamin nan. Suna zaune agabansa kaman masu neman gafara, ya kalli Ilham yace "kunyi sake gaskiya, saboda aikin baya tasiri akansa yanzu sosai kaman a baya, amma yanzu mekikeso ayi" Ilham kaman ta fashe da kuka tace "Malam har za'ayi maganar aure bawan Allah nan yaki yaita min wulakanci, amma katsam naganshi da wannan yarinyar da nake gayamaka rungume a kirjinsa, hankalina ya tashi matuka"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now