ABDUL JALAL (2020) 44

328 22 2
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 44
PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.
Ina me neman afuwarku masoyana, kwana biyu banyi typing ba wayata ta dan samu matsalane
Sannan ina kuma neman afuwarku bazan samu dinga yi muku posting kullum ba saboda zan koma lectures online, Nagode da kulawa

_My first novel_

Sosai Jalila take kuka, tareda surutai,
"Haba Ummi dan Allah ki daga wayata mana, hankalina ya tashi"
Sam bacci ya gagari Jalila, tayi trying lambar Ummi bata san adadi ba amma a kashe, Nana kam tuni tayi bacci, yadda Jalila taga rana haka taga dare, bacci ko barawo be dauketa ba, ta kagu gari ya waye,
Da asuba Nana tashi tayi taga Jalila akan dadduma, ta sunkuyar da kai, bata san Jalila batayi bacci ba ta dauka dai ta tashi da wurine, Kamar kullum Nana tayi sallar asuba ta koma baccinta, mikewa Jalila tayi ta fita daga dakinsu idonta ya kumbura, yayi jawur, ga rashin bacci ga kuma kuka da tasha, kai tsaye kofar part din Abba ta nufa, a hankali tafara knocking, tayi ya kai sau hudu, sannan taga an bude, Maama ce ta bude, ta kalleta a wulakance
"Ke! Meye haka zakizo kinamana knocking da safiyar nan"
Jiki a sanyaye Jalila tace "Kiyi hakuri gurin Abba nazo"
"ikon Allah yaushe kika zama matar gidan nan dazakizo gurinsa da sassafe haka"
"A a Maama dama wayar Ummi ne tun jiya da yamma ya dena shiga shine...
" Shine Me? Fitowa zeyi ya tafi nemo miki ita, Allah ka dai yasan gidan uban data tafi, dalla matsa kibani guri"
Maama ta maida kofa ta rufe, silalewa Jalila tayi a gurin, tacigaba da kuka kuka
"Kingani ko Ummi dakin tafi dani da koma mene ze faru ina tareda ke"
Se karfe tara na safe Abba ya fito, yaga Jalila a kofar part dinsa a zaune, tana kuka, "Subhanallah Jalila me yasameki haka,?"
Kuka takuma fashewa dashi
"Abba, Ummi tun jiya da yamma, lambarta ta dena shiga,"
Tabbas dan shima ya kirata amma taki shiga, cikin sigar lallashi yace
"Kiyi hakuri kinji diyata, yanzu kije kiyi breakfast, zan cigaba da trying lambarta, in be shiga ba zanje tashar motar da kaina inji me ake ciki"
Gyada masa kai tayi ta mike ta koma palour ta zauna tayi shiru, se hawaye dayake bin fuskarta
Wasa2 har azahar babu labarin lambar Ummi, taki shiga, Jalila fa tafara fita hayyacinta, babu cin, Abinci takasa nutsuwa, Jawwad da Abba suka tafi har tashar da akasaka Ummi a mota, amma aka tabbatar musu da cewa motar taje har garin sun juyo, sedai sunyi tsaye2 sun sauke fasinjojii, amma lafiya sukaje suka dawo,
Se dare su Abba suka dawo, amma ba wani labarin samun Ummi, Wunin ranar babu batun nutsuwa a tareda Jalila, kuka kam idon harya kafe, babu hawaye se ajiyar zuciya kawai da take yi, Maama ko kallon Jalila ba tayi ba balle wani magana me dadi ta fito daga bakinta, Nana da Halima ne kawai suke rarrashinta,
Su Abba suna dawowa Jalila ta mike, tana tambayarsu, ya akayi? "
Abba yakama hannunta ya zaunar da ita, sannan yace
" ki kwantar da hankalinki, kinji, munje tashar motar, sunce mana motocinsu sunje lafiya, sun sauke fasinjojin su lafiya sun dawo, dan haka muna da tabbacin Ummi ta sauka lafiya, watakila wayarta ce tasamu matsala amma sunje lafiya, zuwa gobe Insha Allah nida Jawwad zamu kuma komawa, in takama mu bibiya har can garin nasu zamuje, amma muna fatan komai lafiya " hankalin Jalila ya dan kwanta kadan,
Abba ya mike, ya koma part dinsa, Jawwad yasa halima ta zubo Abinci ta hado da tea, ya zauna yasaka Jalila a gaba, ya takura mata, amma ta tsakuri kadan tace ta koshi, karbar Abincin yayi, ya dan hade rai, sannan yafara bata a baki, karba take tana ya tsuna fuska, "Yanaga kina bata raine, kiyi hakuri kici Abincin mana" ta yamutsa fuska, muryarta kasa2 tace
"kaina fa ciwo yake"
"to yi hakuri, ci Abincin, se in kawomiki magani" ta gyada kai
Yana cikin bata Abincin ne, Maama ta fito, wani mugun kallo tai musu
"Kai Jawwad meye haka, ban isa in gaya maka kaji bako?, meye nawani zama kana bata Abinci, tashi kabar nan malam, tashi kafita sha3 kawai, jiki a sanyaye ya mike yana waiwayen Jalila, yayinda ita kuma ta sunkuyar da kai, Maama ta kalli Jalila sannan tace" Mayya kawai, Mara zuciya" dagowa Jalila tayi ta kalli Maama, ta mike ta bar mata palourn, takoma dakinsu,
Jawwad ya koma dakinsa abun duniya ya dameshi, yayi wanka yayi sallar isha'i ya dawo ya zauna a palour, yayi shiru yana tunani,
Jalal ne ya shigo, yazo ya tarar da shi a palour ya samu guri, ya zauna ya kalleshi
"Ina kashigane nazo baka nan, ina ka tafine?"
Ajiyar zuciya Jawwad yayi sannan yace
"Akwai matsalane Jalal"
"matsalar mene?"
"jiya bayan mun kai Ummi tashar mota, tun bayan la asar har yanzu danake maka magana ankasa samunta a waya, lambobinta basa shiga, har tashar motar mukaje nida Abba, amma sun tabbatar mana motocinsu sun isa lafiya sun dawo,"
"To ya akayi haka tafaru?"
Jawwad yace "nima ban saniba Jalal, gashi Jalila ta daga hankalinta fiye da yadda kake tunani, ko abinci taki ci, yanzu na tursasata ina bata, Maama ta koreni, kuma hada gayamata munanan magana, Jalal narasa me zanyi, a halin Yanzu Jalila na bukatar me kwantar mata da hankali, ta damu kwarai"
Ajiyar zuciya Jalal yayi sannan yace
"to yanzu wani mataki aka dauka amma da mamaki ace wayarta bata shiga kuma by now, dai nasan ta isa, kwara state, kuma nasan bazata kasa kiran wayaba"
"Koni jiyan da azahar munyi waya da ita, Gobe in Allah ya kaimu zamu koma tashar, in takama mutafi can garin nasu se muje, ina tausayin Jalila,"
"Allah yasa komai lafiya"
Jawwad yace "Ameen" Jalal ya dafa kafadar Jawwad
"Ka kwantar da hankalinka, karkasa damuwa a ranka, komai zezo da sauki, bana son ka damu"
Dan murmushi Jawwad yayi sannan yace "to naji"
Daga haka Jalal ya tashi ya tafi gida, yunwa duk ta ishi Jalal dan ba wani Abincin kirki a cikinsa, saboda Jawwad baya nan, gashi baya son shiga cikin gidansu, dan yasan inya shiga kafin ya fito se an bata masa rai, har ya kwanta, ya tashi ya nufi cikin gida bakowa a palourn, dan haka ya wuce kitchen zuwa yayi yaita bude2, ji yayi kaman da mutum a tsaye a bayansa yana waigowa yaga Ilham a tsaye, da wata yar riga a jikinta, iya gwiwarta, dauke kansa yayi, yacigaba da abunda yake, a hankali ta tako ta karaso cikin kitchen din, ta dan kalleshi
"My star, me kake nema ne?"
Be amsamata ba balle ya kalleta,
"Ko kanajin yunwa ne?" shiru yayi mata, ya nufi fridge, bayansa ta kuma bi
"haba star, ka kalleni mana, ka amsamin"
A fusace ya juyo
"Ohhh God, haba wai meye hakane? Kinyimin magana nayi miki shiru, base ki kyaleniba, kalleki kalli Jikinki, ya dace kizo inda nake a haka, get out from my side"
Ita a tunaninta shekaranjiya da ya shigar mata fada ko yafara sakkowane, amma yanzu setaga abun bahakaba, shi har yawani san abunda ya dace, ko be daceba, bayan giya yake sha, ga sauran lefuka, amma ta maze ta matso inda yake
"Yaya Jalal kenan, nasan yunwa kakeji, kawo in dafa maka wani abun kaci"
"No need" shine abunda yace mata kawai, kuma matsawa tayi daf dashi, yana juyowa suka hade, zuciyarsa ta buga da karfi,
Ta dan tsura masa ido,
"Meyasa kullum baka da burin daya wuce azabtar da zuciyata ne, kasan ko yadda nakeji? Please Yaya na, love me too"
Shiru yayi mata yasa hannunsa biyu, ya tureta gefe, yakama hanyar waje, sauri takumayi tasha gabansa, tana kallonsa, Ajiyar zuciya yayi sannan yace
"bana son yi miki wulakanci, u are pushing me to the wall, meye haka ne? Meyasa bakida kamun kai Ilham, a hakan kikeso in aureki,? Kalli yadda kikemin ba kya tunanin haramcin hakan, kina tunanin ko na aureki zan yadda dake"
Ta dan nisa
"Yaya Jalal kome nayi kaine sila, meye laifina dan Nace inasonka, da soyayyarka na budi ido why Yaya Jalal? Msyasa baka sona"
Hade rai yakuma yi "Ana so dolene? Tun farko nagaya miki, niba na
ra ayinki, kije kisamu wani, ni bani da niyyar aure yanzu, ki hakura mana, nagaya miki gaskiya bazan aureki ba, "
"Yaya Jalal agaban idona kake gayamin bazaka aureniba, to bari ingaya maka, kayiwa duk wadda zaka aura Albishir din, ta tari bala'in dabata san karshensa ba, wallahi kowa ka aura, sena hana muku farinciki baka isa ka auri wata baniba indai ina raye a doron kasa, kuma ko bana raye fatalwata seta hanaku sukuni,"
Murmushi yayi kawai yai waje, ya fasa daukar abunda yayi niyya, a ransa yace" lallai yarinyar nan bata da hankali"
Ilham takoma dakin tana jujjuya maganganun Jalal "Wallahi karya kakeyi Jalal, kozan tafi tsirara se nacikawa Mamina burinta, zakaga tsiya, senayiwa Jalila abunda se ta mutu da bakinciki, dan na lura itake kara, batamin aiki, da raina wallahi bazakayi aure ba da wata mace inba niba, if not inyi abinda zan karya asirin kowa ya huta, haka Ilham taita surutai marasa kan gado,
Shikam Jalal, Ya fita harabar gidan ya tsaya, yana nazari, ya Kalli agogon hannunsa daga baya ya dau motarsa ya fita, Club ya tafi abunsa yaje aka cashe aka sha giya, yai manksa abunsa, yana tangadi se kawoshi gida akayi.
Dare yaraba, Jalila se nafila takeyi, tana addu a Allah ya bayyana mata Umminta yasa tana lafiya, se gefin asuba bacci yasaceta akan daddumar datayi salla, a cikin baccinnata maimakon tayi mafarkin Ummi tunda itace a ranta, setayi mugun mafarkin data saba yi akan Jalal, a firgice ta farka, tana ambatar sunan Allah gaban ta na faduwa, Nana ta taso tazo inda take, ta dafata "Jalila lafiya kuwa?" rirrike Nana tayi ta fashe da kuka
"is ok dear, yi hakuri, Insha Allah komai zezo da sauki, a yau za a ga Ummi Insha Allah" gyadawa Nana kai kawai tayi, seda ta dan samu, nutsuwa sannan ta mike tayo alwala tazo ta tayar da sallar asuba,
Da sassafe karfe shida Jalal ya tashi yai wanka yai salla, ya dau motarsa ya fita ba tareda wani yasan inda ze tafiba, dan ko Jawwad be gaya masaba.

Karfe takwas na safe Abba da Jawwad suka hadu a palour zasu kuma fita, Maama ta Kalli Abba
"wai Dan Allah yanzu fita zaku kumayi, ko karya bakuyiba, nasan wallahi wani gurin tai tafiyarta amma duk ka daga hankalinka"
Abba ya kalleta
"kina tunanin, zata iya tafiya wani gurin batareda sanin yarta ba, bari in tunamiki abunda kika manta, Maryam da Jalila amanar dan uwana Aliyu ce dasu Inna, idan naci wannan amanar Allah baze barniba, dolena innemo abunda yasamu Maryam dan na tabbatar, da taje lafiya, da komai lafiya nasan, komae ake ciki, zata gayamin"
"kai kake ganin hakan amma a gurin su aikata irin wannan ai ba wani abun damuwa bane, ai abun kunyane ta koma garinsu da yarinya bayan basu san tayi aureba, kodayake su ina suka san wata kunya"
"Ya isheki haka Zainab, Wallahi zan bata miki rai fiye da yadda kike tunani, akan cin zarafin matar Dan uwana, babu bawan da ya isa ya kuskurewa kaddararsa,"
Jawwad ganin sa' insa na neman barkewa tsakanin iyayennasa, se ya kewaye ya tafi dakinsu Nana, ya tarar da Jalila ta dora kanta akan cinyar Nana, tana zubda hawaye, yayinda Nana take bata hakuri, karasowa yayi ya tsuguna
"Baby baki dena kukan bako? Dagowa tayi ta kalleshi, sannan ta sunkuyar da kai, kiyi hakuri yanzuma fita zamu kumayi da Abba Insha Allah zamu gano inda take, ki dena kukan nan kinji, ze iya kawo miki matsala"
Ta dan Jinjina masa kai, ya Kalli Nana yace "Nana dan Allah ki tabbatar taci Abinci"
"to Yaya Insha Allah" daga haka ya mike yafita cike da tausayin Jalila,
Yana fitowa palour yaga ba kowa dan haka ya fita harabar gidan ya tarar da Abba a zaune a cikin motar yana Jiransa, Jawwad ya shiga motar ya kunna suka fita,
Har la'asar babu wani kyakykyawan labari, dasu Jawwad suka samu game da Ummi, kuma har yanzu wayarta bata shiga, haka suka gaji suka dawo gida, koda Jalila taga sun dawo, da sauri ta tashi, ta fita domin sanin me ake ciki, Abba yasa aka kiramasa Jalila, Jalila tazo, ta durkusa a gabansa
Koda taji Abba yafara dayi mata nasiha ta karaya ta kuma fashewa da kuka
"Shikenan na rasa Ummina, Ummi dama haka zakiyimin, kikayimin wayo kika tafi kika barni, yanzu ba Abee ba Ummi"
Jawwad yace "haba Jalila duk bagamuba, kuma Ummi fa bacewa akayi ta mutuba tana nan da ranta, kuma mun bada cigiyarta gurin" 'yansanda, insha Allah za a sameta, kidena kuka"
Daga Abban har Jawwad din Jinsu kawai take, dan bata san me suke fada ba, hankalinta sam baya kansu, dan wani abune yazo saitin zuciyarta ya tsaya, shibe fitaba, shi be komaba,
har magariba, Jalila kaman wata mara hankali, batun Abinci dama babu shi, dan ko ruwa bata zubawa cikinta ba danba Yadda Nana batayi da itaba amma taki cin komai, banda aikin kuka ba abunda take, ga gefe cikinta da ya kulle saboda rashin Abinci,
Bayan sallar Isha'i kaman me tabun hankali ta mike ta nufi part din Abba, ta tarar dashi da Jawwad da Maama a palourn sa, tsayawa tayi tana tunanin to intaje mezatace masa,
Wayar Abba aka kira, yasa hannu yadaga, yayi sallama sannan yadanyi shiru
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya furta" Jawwad ya kalleshi a kidime "Abba lafiya kuwa?"
"Jawwad, wai Ummin Jalila wai motace ta bigeta kafin sukarasa garinsu, ta sauka yin salla, kuma wanda ya bigetan yasata a mota ya tafi da ita"
Da jin haka Jalila ta kwalla kara, sekuma ta kame a tsaye, gaba daya suka juyo suka kalli inda take tsaye, idonta a kafe a kansu, mikewa Jawwad yayi da sauri ya nufi Inda take amma ko motsawa batayi ba, kuma ko kyafta idon batayiba, Yana tabata ta tafi zata fadi, da sauri Jawwad ya rikota, Abba ya taso da hanzari "lafiya kuwa, meyasameta?"
Idonta a bude kar, amma bata mosti bata numfashi
"Innalillahi wa inna ilaihi raji un Abba Jalila ta mutu"
Maama na jin haka ta taso da sauri
"kamarya ta mutu?"

Share please
More Comments More typing........................................

Love u all my fans ina godiya, da adduo'inku, da kaunarku, Allah yabar kauna
🌹🌹🌹❤️❤️❤️❤️
Team Jalila su ummu Hanif kuzo jana'iza 😂😂😂😂💃💃💃 queen ta wula

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now