ABDUL JALAL 99

359 28 1
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 4️⃣6️⃣99

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

_MY FIRST NOVEL _

Hannah gaba daya kanta ya kwance bata taba tsammanin abubuwa zasu kwabe mata haka ba, wai me yakawo Jalila a gabar da takeso kulla wannan gadar Zaren, da komai ya tafi dai2, Jalal baze taba tsallake shirinta ba, wayarta ce ta fara ringing amma Hannah tayi biris da ita, an kirata ya kai sau shida sannan ta dauka a fusace tace

"dalla waye haka?"

"ke dalla zizo ne, za'a miki abun Arziki amma kina wa mutane hauka, ki tattara kayanki tun wuri kisan inda dare yayi miki wallahi"

"kamar yaya? Saboda me?"

"Allah ne yake sonki da rahama, Wallahi Jiya na raka wani me gidana Unguwa, ya tsaya gurin wani me gidansa dan sanda ne babba, naji me gidannan sa yana waya, bayan ya gama yake gayawa maigidana, wai wani yabada izinin a kamo masa wata yarinya a ajiye masa ita har seta haihu, ta yaye yaron ya shekara biyar sannan a saketa, idan kuma ba tada ciki aita ajiye ta kar a saketa, kuma yadda mutumin nan yake kwatantawa na gano kaman kece, ban gasgata hakan ba se jiya da naje palace, wallahi cikin dare 'yan sada sukazo nemanki, dan haka in kin san da wata cakwakiyar da kika kulla tun wuri ki kama gabanki wallahi "

Hannah ta hadiyi wani mugun miyau ta ce
"Shikenan nagode sosai zizo"

Ta katse wayarta ta mike tsaye tareda fadin
"kan bala'i banga ta zama ba, ni Jalal zewa haka? Wallahi yadda ya fada din nan aka kamani kashina ya bushe, Amma wallahi in yasan besan wata besan wata ba, ni zesa akama, nizewa hauka? Banga ta zama ba"

Ta mike da sauri ta janyo Akwati tafara zuba kayanta tanayi tanayin surutai.

Jalila ta tattara komai ta ajiye a gefe ta maida hankali akan karatunta, dan yadda takeji in bata dena yawan damuwar nan ba zuciyarta zata iya bugawa, sosai Maama ta rage wannan gabar da takeyi da Jalila, tana dan sakewa da Jalila har suyi hira, suna shirye shiryen yadda biki ze kasance, Jalila bata taba nuna mata tana fushi da ita akan abubuwan da tayi mata a baya ba, Maama har mamaki takeyi, wani lokacin yanayin halinta daya da Jawwad, ka musu laifi amma su nuna basu san kanayi ba, ita kanta Nana tayi mamakin yadda Maama tayi saurin karaya da Al'amarin da yafaru.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now