part 2 55

367 20 2
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 2️⃣/ 55_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki, da suka bibiyeni a littafi na farko, Alhamdilillah yanzuma gani na dawo domin kawo muku kashi na biyu, nagode da kulawarku, ku biyoni domin jin yadda zata kaya a cikin wannan littafi naku me farin jini.
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Gmail @ www.humaira17@gmail.com Facebook @ real humaira
Follow the group of ABDUL JALAL NOVEL FANS through this link 👇
https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL
Follow me on watpad @Ayshercool7724

_MY FIRST NOVEL _

A hankali ta daga idonta, tasa a cikin nasa bata manta fuskarba dukda gani biyu ta taba yimasa, baban faruk ne, bako shakka shine, wani shu'umin murmushi yayi mata irin nasu na yan duniya "ko baki gane ni bane"? wani kallon rainin hankali tayi masa" sannan tace "dukda kasancewar kwakwalwata tana rike, tareda tuno abubuwa masu mahimmanci da suka shafeni ne, amma hakan besa na manta wannan fuskar ba"
"Kenan nima inada mahimmanci a gurinki tunda har kika tunoni? " "sosai makuwa kanada mahimmanci, shiyasa na iya tunaka" wani murmushi ya kumayi "Amma naji dadin zama daya daga cikin masu mahimmanci a gurin wannan kyakyawar halittar, amma meyasa nazama me mahimmanci a gurinki" Jalila a zuciyarta tace saboda ka shigo cikin suspect dina amma a zahiri tace
"saboda kasancewar ka uba nagari, me kokarin kare mutuncin dansa daga hulda da mutanen dabana kwarai ba" "kinji haushin abunda nayiwa Jalal kenan, amma inkika duba ya cancanci hakan, duba da yanayin wani irin mutum neshi" Jalila ta dan kuramasa ido, kai da ganin mutumin nan kaga rikakken dan duniya, tsabar iya barikine yasashi yake acting kaman mutumin kirki, "excuse me please komai nawa a ka'ida nakeyinsa ina da abubuwan yi yanzu se anjima" yai saurin dakatar da ita ta hanyar cewa "yi hakuri dan tsaya mana dan Allah, ina so mudinga haduwa muna gaisawa ne, in bazaki damuba ga complementary card dina seki kirani, dakuma adress dina, mutane na musamman nake bawa wannan adress din" hannu tasa ta karba ta kalli katin ta juyashi, ta dan kalleshi na wasu seconds, tsaf ta haddace lambarsa da adress din jiki, sakin katin tayi a kasa tai masa wani kallo da yakasa gane me take nufi, kawai ta juya tai tafiyarta, tsayawa yayi ya zuba mata ido, "gaskiya wannan yarinyar yar rainin hankali ce, amma kota halin yaya, seya gane wacece din Jalal, kuma se yayi yadda yakeso da ita
Itakam tana fitowa ta kalli manu tace " yi hakuri manu na dan dade, muje nagama"ta shiga mota suka tafi, ta dakko kudin tabawa manu tace gashi nan, aiwa maman sannu, kuma ita kyauta ta bashi ba rance ba" manu kaman ya yi kuka dan murna se godiya yake mata.
Jalila na zuwa gida, ta tarar gidan ba kowa dan haka ta tafi dakinsu ta haye gado ta sha baccinta, alhalin school ana can ana lectures, se bayan azahar ta tashi, tana tashi da baban faruk ta tashi a ranta, ras take kuma ganin katin daya bata a idonta, kabiru Idris, shine sunan dayake jikin katin, wayarta ta dakko tayi saving sunansa da lambar sa, da adress din dayabata a jiki, duk tayi saving a wayarta, sannan ta aje wayar a hankali, sannan tace kaima ban yadda da kai ba. Ta tashi ta tafi kitchen ta hado cornflakes dan tana jin yunwa, maimakon ta koma daki seta fito harabar gidan tai zamanta a kujerun harabar gidan, ta gefen Jawwad dayake gurin akwai bishiya, ta zauna tana shan cornflakes dinta, tanayi tana karanta qura'ani a hankali, tana dan kaďa kafarta, Jalal ne ya shigo yazo ya wuce ta gabanta bata kulashi ba be kulata ba, ya wuce part din Jawwad, yana zuwa ya dau laptop dinsa da yabari a dakin ya samu guri ya zauna ya fara video call da daddynsa
"My Man ka girma, naga hotuna na birthday kunyi kyau Allah yakaro tsawon rai da lafiya me inganci" "to Ameen amma ni fushi nake da kai"
Daddy yai dariya "to menayi?" "Kaje ka makale a England kaki dawowa, bakayi attending birthday na ba" daddy yai murmushi "to ai nace ka daga birthday din indawo kaki, kuma abubuwa sunyimin yawa anan gakuma aikin daka sani, koka manta ne?" "ban manta ba daddy, ina fatan ana samun cigaba" "eh anasamu Alhamdilillah" "to hakan yayi kyau, yaushe zaka dawo?"
"ina nan tafe next week Insha Allah"
"To dan Allah ka dawo haka, inaso indinga ganinka" daddy ya dan girgiza kai "Allah sarki yarona, karka damu, nace kazo nan mu zauna tare kaki" Jalal cikin damuwa yace "Haba daddy, in taho nan in bar aminina dan uwana, kasan bazan iyaba" "Hakane Jalal, ina Dan nawane, ko yau bakwa tare?" "Yana makaranta" "that's good, Allah ya nunamin ranar da zaka koma makaranta, yanzu ka zama mutum Jalal ina fatan Allah ya shiryamin kai inmaka aure" ya mutsa fuska yayi ya kalli system din "Aure kuma? Habaa daddy yaushe aka haifeni, ni banason gayyatowa kaina matsala, mata matsalane daddy kaima kasani" ya karashe maganar kaman zeyu kuka,
"ABDUL JALAL, bakowace mace ce matsala ba, in har kayi dace da samun mace ta gari, kaga hotunan birthday dinka danagani, dana ganka tareda Takwararka abun yamin daďi, senaji dama matarka ce, yarinyar tanada nutsuwa ga tarbiyya " wani mugun hade rai Jalal yayi "What matata kuma, Allah ya kiyaye, wannan kwailar, mara kunyar, na auri wannaan sedai kuzo ku tarar na kakkaryata"
A gigice Ilham ta tashi zaune, ganin hotunan da aka turomata ta what's app, ba tareda tasan waye ya turoba, hotunan dasu Jalila sukayine, a kasa aka rubutamata "Yakika gansu, perfect match, ina musu fatan Alkhairi, da fatan kasancewa tare har abada, wannan itace matar data dace da Jalal bake ba" mikewa tsaye tayi akan gadon, "What ni za ayiwa wannan rashin hankalin, lallai Jalila tayi bal'in rainamin hankali. Ba tunanin komai, taja gyalenta tai waje, Mummy tana yimata magana amma taimata banza, ta fita se gidansu Jawwad, tana zuwa taga mutuniyar tata a hakimce a farfajiyar gidan, kusada part din Jawwad, a inuwa se kada kafa take, tana ciye2 hankali kwance, bazar2 Ilham ta tunkari Jalila taje kanta ta tsaya tana huci, Jalila kam kaman ba kowa a gurin, tacigaba da abunda take. Cikin masifa Ilham tace
"Wato gargadin danayi miki bakiji ba ko? Saboda kin rainamin hankali, abunda kukayi keda JALAL a gurin birthday dinsa be isheki ba ko? Hakan be miki ba seda kika hadani da wannan tsinanniyar yarinyar Hannah a gurin nan, Shine duk be miki ba sekin hada da turomin hotunanku, sau nawa ina gaya miki kifita harkata, ina tausayawa rayuwarki idan na tashi hukunta ki" Ita Jalila abun mamaki yake bata wai wace jarabar hotuna na ake damunta haka akai, ba tareda ta kalli Ilham ba tace
" tunda kekika halicceni dole ki tausayawa hukuncin dazaki yimin mana, ki kasheni ki huta mana, seki tabattarmin dake kanwar Jalal ce, hakan se ya tabbatar da cewar bashi kadai yake shan giya ba"
Takarasa maganar cikin ko in kula, tacigaba da watsa cornflakes dinta a baki, Ilham ta kawo iya wuya, wato Jalila takai karshe gurin raina mata hankali, idonta taf hawaye tace "Wallahi Jalila in baki fita hanyata data Jalal ba, kina daf da fadawa rijiyar sharrina, idan nasakoki gaba ruwa seya gagareki sha, Inakuma yimiki kashedi kinfara kaini bango, idan turn dina yazo bazaki ji dadi ba, ki kiyaye.
Jalal ne yake tajin hayaniya, har ya basar ze kwanta seyaji hayaniyar yana kara yawa, dan haka ya yanke shawarar fitowa dan ganin meke faruwa, yana fitowa ya tsaya a kofar part din Jawwad yana kallon dramar da ake.
Ilham tacigaba da cewa
"waike wace irin mayyace? Mara zuciya, meye hadinki da mune, baki da alaka ta kusa ta nesa damu why do you involve yourself in our family matters, nagaya miki nakuma gaya miki Jalal nawane, wace irin mara zuciya ce ke, kishiga hankalinki harni zaki turawa hotuna, kina kece kika dace da Jalal, zakiga wacece Ilham, na daga miki kafa amma baki ganeba, zakiga me zanyi" Kamshin turaren JALAL Jalila taji, hakan ya tabbatar mata da fitowa yayi, dan haka bata kula Ilham ba ta mike tsaye, ta taka a hankali, cikin takunta na isa, kunsan fa Ummi jinin sarauta ce dan haka akwai abun a jinin Jalila, taje gaban Jalal ta tsaya, ta kalli Jalal sannan ta kalli Ilham, ta nuna Jalal sannan tace "Wannan shine mara zuciya, mara tarbiyya shiyakamata, kigayawa bakaken maganganu bani Jalila ba, shi duk abunda yake meyasa baki ja kunnensa ba dan kina tsoronsa, kokuwa dan abunda yake ranki wanda kike boyewa, to ni bana tsoron kowa se mahalicci na, aike karamar mara kunya ce, ni idan zanyi sedai aga na aikata, bana fada, idan akabari nafadi abunda zanyi komaj muninsa sena aikata, ke alwashi nawa kika dauka kika kasa cika ko daya, Tunda ABDUL JALAL yashiga rayuwar Yaya Jawwad to a cikin rayuwata yake, shi zaki Jawa kunne ya rabu da Jawwad, in har ya rabu da Jawwad, ba ruwana da shi, bari kiji in gaya miki za ayi dayan biyune ko Jalal ya fita daga rayuwar Jawwad kokuma kudirina.... Sekuma tai murmushi ta kalli Jalal
"Kagayawa wannan sokuwar yarinyar, niba abunda zanyi da kai, baka da abunda ze birgeni insoka bana cikin jerin banzayen matan da zasu zubar kimarsu da ajinsu akan namiji mara daraja irinka, wanda besan ciwon kansa ba balle yasan na wani, namijin da besan darajar iyayensa ba, namijin dabaya girmama alaka, dan da kanayi da zuwa yanzu ka tausayawa Jawwad kadena abunda kake, namijin dabe maida sabon Allah komai ba, baya kunyar sabawa mahaliccinsa agaban kowa, shikike tunanin ya cika siffa da kamalar dazan soshi a matsayin uban y'ay'a na, shi kike tunanin zan zubar da kimata ina hayagaga dake akansa "ta nuna Jalal sama da kasa da hannunta
" Ilham ki canza tunani, Jalila ba irin sauran matan da kike tunani bane, duk abunda kikaga inayi i have a mission, kawai ina kokarin rama Alkhairi ne da Alkhairi, karki manta da maganar dana yimiki abaya muddin kudirina yaci karo da na wani zan rusa kudirin ko uban waye dan cikar burina" ta waiga ta kalli Jalal, da idonsa tuni yayi ja, gashi ya kasa matsawa daga inda yake kaman an dasa shi, Ilham rasa bakin magana tayi, Jalila ta kalleshi a wulakance, kaikuma ka gayamata ta kiyayeni dan muddin takuma cin mutuncina saboda kai akanka zan rama, har sena gamsar da ita cewa bawata alaka me ma'ana tsakanina da kai" tana gama fadin haka takoma ta dau Cup dinta tai cikin gida ta barsu nan a tsaye.
A hankali ya lumshe ido, ya tako a hankali ya nufi hanyar fita, Ilham tai sauri tace "Yaya Jalal dan Allah... Daga mata hannu yayi alamar baya son jin mezata ce, yai gaba abunsa, maganganun Jalila na cigaba da tafarfasa zuciyar sa. Yana shiga gida ya nufi part dinsa ya samu guri ya zauna ya dafe kai yai shiru, Ilham ta biyo shi tazo ta zauna a kusa dashi, "Dan Allah yay Jalal kayi hakuri, nibani da laifi anan, kawai ina kokarin kare alakar dake tsakanina da kaine, meyasa bazaka yadda dani a in zama wani bangare na rayuwarka ba"? Tashi tsaye yayi ya tafi bedroom dinsa ya kulle kofa ya barta a palour.
Jalila koda ta koma dakinsu, kwanciyarta tayi ta dakko wayarta, tafara chatting, ta bude pages da take advertising kayan da Maama dakuma Mummy Jalal suke siyarwa, tana kawo musu customers sosai, daga gurare daban2, wasu suzo da kansu, wasu kuma a aika musu har garin da suke, gashi Jalila ma tana harkar catering ta iya girke2, wani lokacin ta kanyi snacks ta siyar, gashi duk karshen wata Abba yana basu kudi, wani lokacin dubu Ashirin zuwa talatin, inda me bukata tayi amfani dasu, Jalila bata da wata matsala se na kewar Ummi da har yanzu yake damunta, dan har yanzu takan kulle kanta tayi kuka me isarta, tana naan tanawa Ummi Addu"ar Inda rabo Allah ya kuma hadasu.
Chats dinsu da siyama ta bude taga ta turomata hotuna tana dubawa taga hotunanta ne da Jalal, wani dogon tsaki taja yanzu watakila saboda wannan hotunan Ilham tazo kanta tanamata hauka, har zata rufe data dinta taga wani sako ya shigo, tana budewa taga an mata sallama, ta duba profile din taga basuda group in Common dame maganar, amma an rubuta unique zarah, batayi reply ba ta rufe data. Da Nana ta dawo tayi mamakin ganin Jalila a gida, Manu yagaya mata ai tun goma da rabi ya dawo da Jalila gida, Nana ta kalli Jalila
"Jalila ya akayi naganki a gida, manu yacemin tun safe kika dawo, kobaki da lafiya ne?" "lafiyata kalau zaman makarantar ne ya isheni, na dawo gida" dan zare ido Nana tayi to lectures dinfa? "
" Kinga ki manta kawai"
"Bangane in manta ba kefa al amuranki se a hankali" "A a nagaya miki gaskiya to meye na tuhumata" Nana tace "tabdijan, A haka zakiyi karatun sekin gadama zakiyi attending class in kika fadi fa" "Nana kidenamin fatan faduwa, ba abunda zekadani Insha Allah" "to Allah ya yadda amma dai banga ta yadda za aci jarrabawa a haka ba" Jalila ta dan tabe baki tace "ke kika ga haka"
Tunda Ilham takoma gida takewa Mummy kuka, "Mummy dan Allah ki gaggauta auramin Jalal, wallahi zuciyata daf take datayi bindiga in har ban mallakeshi ba, Mummy nagaji da wulakancin Yaya" Mummy ta dafata
"Kiyi hakuri mana Ilham kefa macece yakamata kija ajinki, kuma ni namiki alkawarin auren Jalal" "Mummy babu wani batun aji a fagen soyayya, Mummy dan Allah kiyi wani abu"
"Haba Ilham wai meye hakane, kibari daddynsa ze dawo next week Insha Allah, in ya dawo semu san yadda za'yi, tashi ki tafi dakinki ki dena wannan kukan" mikewa Ilham tayi ta tafi dakinta, tana zuwa ta rufo kofa, sannan tai kwafa "Mummy kicigaba da jamin rai akan auren danki, koki sabaki ya aureni ko karkiyi sena aureshi, sena cika burin mahaifiya ta, sekin wulakanta kin dandani bakin cikin da uwata tayi, ko zan tafi tsirara bazan bari A banza Jalal ya auri wataba bayan ni, wasan ze fara nakusa kawo karshen wannan dramar, indai na haifu se nasa bakin cikin ABDUL JALAL ya kusa kasheki, sekuma ya aureni dan zan iya halaka duk wadda tai nufin aurensa ko wacece!!!!!

Share please
More Comments More typing..............................

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now