ABDUL JALAL (2020) 27

295 22 4
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

    _ABDUL  JALAL_
           (2020)

      _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
    (Daddy's girl)

               PAGE-  27

PART 1

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

07063065680

Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum
Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa

   
       -MY FIRST NOVEL-

A hankali ya bude idonsa da sukayi jawur, saboda buguwa ya mayar ya lumshe sannan ya fara magana a cikin maye

"Ni wannan yarinyar bana sonta, narasa meyasa Jawwad yayi min hakane, nace masa bana so amma shi......se wani"
Sekuma yayi shiru, Ajiyar zuciya Ilham tayi tace"munafukan banza daga Jawwad har kanwar tasa, zasu gane kurensu
Matsawa takuma yi ta kwanta a jikinsa sannan ta Dan dago ta kalleshi tace

"Meyasa baka sonta?"

"Mtseww nifa bana son tambaya, bana sonta kawai bata da hankali," ya Dan girgiza kai ya yamusta fuska warin turaren nan yaji da yabaya so

Ta kuma cewa "Ita kuma Ilham meyasa baka sonta?"
Dan bude ido yayi ya mayar ya lumshe yace
"wannan fa kanwata ce, meyasa zanyi wani soyayya da ita, kanwata ce kawai"
Shigewa jikinsa ta kumayi sosai
"But I love you, karkayi soyayya da wata bayan ni, Ilham ce kawai take sonka, sauran duk bamasu kaunarka bane, Ilham tana sonka kaima kasota kaman yadda take sonka mana"

Dukda yana cikin maye setaga yayi murmush i"ka yadda zakaso Ilham?"

"Bacci nakeji ki kyaleni da wannan mafarkin"

"Mafarki kake?"
Ya gyda mata kai
Tace  "ya kusa faruwa a zahiri"
Tai maganar tana shafa gashin kirjinsa ya mutsa fuska yayi ya rike mata hannu"kidena bana so"
"Meyasa bakaso?"
Shiru yayi be ce mata komai ba
"Shikenan tunda bacci zakayi bari in tafi,"
Durkusowa tayi da nufin tayi kissing dinsa se ya juyad da kansa alamun baya so, kallonsa tayi
"Why?"
"Ki tashi ki bani guri nace miki bacci zanyi"
Gabanta ne ya fadi dataji yayai normal magana ba tare da maye ba, kallonsa tayi taga ya bude idonsa fes akanta, sekuma ya mayar ya lumshe yacigaba da bacci Ajiyar zuciya tayi tare da fading
"Allah ya temakeni na dauka giyar tasakeshi ne"
Kissing dinshi tayi akan lips dinsa sannan ta mike ta fita ta nufi cikin Gida, me gadi ya hango fitowarta daga part din Jalal

"Kai me yarinyar nan take a bangaren yaron nan a wannan tsohon daren,
Allah ya kyauta bayan shan giya kuma yafara biye² mata, abun kunya kuma da kanwarsa Allah ya shirya"

Da safe Jalila tanata shirin makaranta, wata makwabciyarsu bata  wuce sa ar Jalila ba ta shigo tacewa Ummi Dan Allah ta sammata abunda ta girka ita tayi girkin takasa ci dayake tsohon ciki ne da ita
"Allah sarki hawwa'u Allah yaraba lafiya bari azuba miki
Jalila zubomata abinci"
Jalila kam zuwa yanzu Hawwa haushi take bata gani take tsabar kwadayine da iskanci komai bazata iya Ciba sena gurin ummi, Ummi kuma bata taba hanata ba ko kyararta
Jalila tana zumbura baki taje ta zubomata dataga ummi bata kallonta ta dungurar mata da kwanon da kayan tea
"Gashi nan kwadayayyiya seki hada Sa kanki niba Yar aikinki bace"
"Eh naji kwadayaiyiyyar ce ke in naki yazo maga yadda zakiyi"
"Bawani nan komai kidorawa ciki, dayana da baki se yace karya kike masa"
Dariya Hawwa tayi ta hada abincinta ta fara ci suna hira da ummi tana gama ci ta kama aman abincin nan dataci seda ta amayar tsaf
"Kai kekam kin banu sekace akanki aka fara ciki ga rakin tsiya ni bari in bar gidan nan tun kafin nima kisani aman"
Jalila tai maganar tareda daukar jakar makarantarta tayi waje
Girgiza kai ummi tayi indai Jalila ce bazata canza ba

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now