ABDUL JALAL (2020) 36

294 21 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 36

PART 1
Share please

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
ABDUL JALAL NOVEL FANS
Love u all guys ❤❤❤❤❤

-MY FIRST NOVEL-
Ilham ce da yaseera gurfane a gaban malamin nan, malamin ya kalli ilham sannan yace
"Ya kikazo keka dai yau ina babartaki?" Ilham ta Dan gyara zama
"Malam akwai matsalane fa"
"Matsalar me?"
"Malam, nifa na fara gajiya da wannan wahalar danakeyi akan Jalal, ina ta nawa kokari amma, wata Matsala na kokarin kunno kai, duk wannan wahalar danake yana kokarin fara soyayya da wata yarinya daban, hankalina duk a tashe yake"
Malamin ya numfasa ya kalli Ilham sannan yace
"Anya kuwa dagaske kike yafara soyayya, a aikin damukayi akansa bana tunanin ze iya fara soyayya cikin sauki, har se burinku yacika,"
"Malam nifa tsoro nake, kar inje shirin ya rushe gaba daya"
"Hakane in dai ba wancan sharadin ne ya afkuba, to aikin damukayi masa yana tareda shi har yanzu, koda kuwa yayi soyayya da wata, sedai in wancan sharadi ya karya"
"Wallahi ji nake kamar kawai in aiwatar da me gaba dayan tunda har yanzu yaki yadda ya soni, balle ya aureni"
"Wannan kuma ya rage naki sekije kicigaba da kokari, ko be sokiba daya aureki shikenan aiki ze kammala"
Yaseera ta kalli malamin
"To yanzu malam babu yadda za ayi da wannan shedaniyar yarinyar, tunda akwai yiwuwar ya iya fara soyayya"
"Wannan kuma Ku zakuyi wannan aikin ni nayi muku kokarin da yakamata sekije ki bada himma, zanyi bincike akanta, muga abinda za ayi akanta"
"To shikenan malam zanje in cigaba da kokarin"
"Yayi kyau, abinda ake ciki zan sanarda ke"
Suka mike suka fito yaseera ta kalli Ilham
"Wai Ni kuwa Ilham wace wannan yarinyar"
"Hmm wallahi kanwar abokinsa ce wata Mara mutunci da ita, yaseera yarinyar nan bata da mutunci Sam, idan banyi wasa ba fa zata bata min aiki, kinga rashin mutuncin da take masa amma ko kallonta ba yayi balle ya dau mataki, kuma da nice na gayamasa abinda take masa da tuni ya hukuntani"
"Kince sonshi take, kuma kince tana masa rashin mutunci, anya kuwa son nashi takeyi"
"Nima abinda nake ta tantama kenan, amma nafi tunanin borin kunya suke a gabana amma sonshi take, kinga a yadda nagansu kuwa ranar a gidansu, wallahi bantaba tunanin haka kishi yake ba se ranar"
"Wai ma inane gidansu"?
"A gidansu Nana take fa cousin dinsu ce"
"Muje gidan inga wace ce, inga iya rashin mutuncin nata se mu San ta inda zamu bullo mata"
"To shikenan mu karasa, ki ganta,"
Hannah ce kwance akan gadonta tana zancen zuci, "mace kamarni ace Jalal yake wulakantawa, ga yadda maza kemin layi amma akan wannan Dan tahalikin, nake wahala har wani cewa yake ko ze aure baze aureniba, na tabbatar ranar Dana kirashi wannan kanwar tasa ce ta daga har take zagina, zanyiwa Jeje aikinsa sannan itama kanwartasa senayi maganinta, nita zaga saboda tana son Jalal, zata ga tsiya, indai Hannah ce ta taro daidanta"

Nana ta fito ta tarar da Jalila a kwance akan kujera tana danna waya
"Jalila zan Dan fita, zanje bayan layi ne Maama ta aikeni"
"To sekin dawo"
Fitar Nana ba dadewa aka turo kofar palourn ba ko sallama, mutane taji tsaye akanta
"Dan Allah ina Nana"?
Shiru tayi ba tako daga kai ba, balle ta ga suwaye
" magana fa nake miki"
Ba ta dago kanta ba tabada amsa
"Taje akoya mata sallama, inzaka shiga guri"
Yaseera ta kalli Ilham, sannan tace
"Yi hakuri Dan Allah, salam alaikum"
"Wa alaikum salam warahmatullah"
Jalila ta amsa sannan ta tashi zaune
Ta dubesu ta danyi murmushi
"Sannunku da zuwa bismillah ga guri Ku zauna"
Ilham se wanj hura hanci take
Jalila ta Dan kalli Ilham sannan ta maida idonta kan yaseera
"Nana ta Dan fitane ba nisa tayiba yanzu zata dawo insha Allah"
Yaseera ta danyi murmushi,
"To mungode"
Suka samu guri suka zauna
Jalila tace
"Ilham ya kike,? Ya Gida"
Ilham tai mata wani irin kallon up and down
"Da nazo nayi miki maganane? Kokuma ke a dole sekinshiga harkata"
"Ko in shiga harkarki ko kar inshiga harkarki babu abinda zaki kareni dashi ko ki rageni dashi, tunda ba abunda nake nema a gurinki nayi hakanne kawai Dan sauke hakkin addinina, ke Yar uwatace musulma, kuma makociya, muna da hakki akan juna shinake kokarin saukewa kawai, bawai wani abuba"
Tabdijan yaseera a zuciyata tace "lallai wannan yarinyar yar duniya ce tana da baki, gashi komai nata abin birgewa yanayin yadda take magana kawai ya isa ya dau hankalin mutum, ga iyayi kuma dajin maganarta kaga shgwababbiya gashi ta iya juya ido in tana magana" yaseera kallon Jalila kawai take
"Bakuwa bari in kawo miki abin tabawa kafin Nanan ta dawo, naga Ilham se wani cika take tana batsewa bansan menayi mataba"
Jalila ta mike tana tafiya a gayance ta nufi fridge
Lallai dole Jalila ta tafi da imanin duk Wanda yai tarayya da ita dukda Ilham tace mata bata da mutunci amma tana ganin hakan duk cikin iya takunta ne
Lemo Jalila ta kawo musu da ruwa sannan ta kira Nana a waya, ta gayamata tayi baki, Nana tace mata takusa karasowa tana daf da Gida
Yaseera ta kalli Jalila
"Nagode Yar uwa"
"Bakomai yiwa Kaine bakin Nana ai baki nane"
Ilham bata kuma cewa komaiba, tunda Jalila takuma gaya mata magana, sema haushin yaseera daya kamata ganin yadda ta zage suna hira da Jalila kamar sun saba
Ana haka Nana ta dawo,
"Yawwa ga Nana nan ta dawo"
Nana ta kalli inda su Ilham ke zaune
"Yaseera dama talaka na ganinki gaskiya akwaiki da zumunci"
"Yanzunma unguwa mukaje nacewa Ilham mu biyo mu gaisa kwana biyu bamu haduba"
Nana tace "hmm kin kyauta ya Gida ya kwana biyu?"
"Lafiya kalau"
Jawwad ne yayi sallama a palourn suka gaisa dasu Ilham
Sannan ya kalli Jalila
"Baby yunwa fa mukeji kuma munji ki shiru, Jalal ze sha magani beci abinci ba"
Kallon Jawwad tayi ta danyi murmushi
"Aini yau banyi girkiba, in kuma kunajin yunwa to kuzo kuyimin wanke² wani yayi gyaran kayan miya" murmushi Jawwad yayi ya nufi hanyar kitchen Jalila ta mike tabi bayansa, Ilhaam kam Dan bude baki tayi
"Hmm Yaya Jawwad manyan"
Nana ta fada tana Dan murmushi
Ita dai yaseera ta jinjina yadda Jalila take gudanar da
al amuranta cikin nutsuwa, lallai indai da Jalila, Jalal yake
Shirin fara soyayya to se Ilham tayi dagaske, don Jalila bazata sha wahala gurin sace zuciyar duk Wanda taso ba
Jawwad ne yake bubbude kwanuka a kitchen
"What are you looking for?"
Yaji muryar Jalila a bayansa, juyowa yayi ya kalleta
"yunwa fa mukeji baby" yai maganar yana kwaikwayon JALILA
"Yi shiru karkayi kuka jeka zan kawo"
"Inyi kuka sekace wani baby, Babyce me kukan allura, kuma nasan in tanajin yunwa ma setayi kuka"
Dariya sukayi gaba daya
Wanda hakan yayi dai² da fitowar Maama tana kallonsu ta window kitchen, kwafa maama tayi ta nufi parlour
Su yaseerana suka gaida maama ta amsa musu sannan tace ma Nana taje tacewa Halima tana kiranta, tajuta ta koma dakinta
Su yaseera suka mike sukace zasu tafi, dama ba ziyarar Allah da annabine ya kawosu ba Dan ILHAM ta nunawa yaseera Jalilane, suna shirin tafiya
Jalila suka fito ita da Jawwad, suna dariya, Ilham ta kallesu taja uban tsaki
Jalila ta kallesu "har zaki tafi, yaseera, mungode ki gaida Gida, Ilham ki gaida mummy"
Ilham bata kula Jalila ba itama Jalila bata damuba Dan tasan ILHAM ba amsawa zatayiba, tai waje da kayan abincinsu Jawwad
Nana ta kalli Ilham
"Haba Ilham, Jalila tana miki magana amma kin wani shareta"
"Kinsan bana son rainin hankali, kuma kinsan halintane dan haka ni bana shiga sabgar mutum inaga hankali be isheshiba"
"Kut lallai Ilham amma kinsan da a gabantane dase ta gaya miki wadda tafi takin zafi"
"To yanzu tunda bata nan seki rama mata"
Ilham ta fada tana Harar Nana
"Rufamin asiri, ina ni ina iya shigarwa Jalila fada ai sedai inyi kallo"
"Ya fiye miki"
Haka Nana tarakasu ILHAM had bakin gate suna tafe suna fada,

Jalila tabi bayan JAWWAD da kwanukan abinci zuwa part dinsa, oga Jalal yana zaune yana kallo sekace dakinsa, Jalila ta ajiye kayan abincin tareda fadin "wash" JAWWAD ya Dan kalleta "kai baby har kin gaji"
"Niba gajiya nayiba"
"Hmm dagaske?"
"Eh mana"
"OK tunda bakgajiba serve us"
Seda ta kalli Jallal ta Dan hade rai
Ta dau plate tayi serving Jawwad, ta kalli JAWWAD "sekuma me?
"Baby Jalal fa, serve him too"
Yamutsa fuska tayi
"Ni na gaji"
"No Jalila, kefa kikace Baki gaji ba, hakan ba halinki bane"
Kafin tayi magana Jalal ya taso daga inda yake cike da gadara, yasa hannu ya dauke plate din gaban Jawwad da Jalila tayi serving din Jawwad, ya dau spoon ya samu guri ya zauna, ya fara cin Abincinsa

Bayan sun fitane yaseera ta kalli Ilham
"Tab wai yanzu kina nufin wannan itace budurwar JALAL din"
"Hmm gata nan kin dai ganta ko?
" ai ko ta hadu"
"Kamarya ta hadu, kinsan dai na fita kyau ko?"
"Ke dalla wayake ta wani kyau Ilham, duk kyanki akwai qualities din da in kika rasa, to kyan yazama shirme, banda abinki ma dame kika fita, hasken fatarne kawai amma wallahi kyakykyawa CE"
"Au yaseera hakama zakice dame ta fini?"
"Kallifa mu matama kalli da yadda take mana magana INA ga in agaban namijine, gashi ta iya iyayi da siyasa, kincemin fada kuke, amma dukda munzo tare kalli yadda ta mutuntani, gata Yar gayu"
Ilham ta hade rai sosai sannan tace
"Ni duk ban iya wannan abubuwan ba kenan?"
"Bahaka bane ba, amma kin San meyake cutarki"
Ilham ta girgiza kai
"Rashin hakuri, saurin fushi, ga garaje, gaki da sakaci, kinga in bakiyi dagaskeba akwai matsala kina ganin yanda take wani juya ido in tana magana"
"To yazanyi yaseera,?"
"Waima tukuna naji yayan Nana yana batun akai musu abinci shida Jalal, Abincin ma ita take kai musu"
"To inaga ita take kaimusun mana" Ilham tai maganar cike da damuwa
"Cab wato ita take kaimusu abinci, lallai ILHAM da sauranki, gaskiya akwai tendency na JALAL yafara soyayya, kuma abinda kike gudun yafaru"
Ilham ji tayi kaman ta Dora hannu a ka ta fashe da kuka
"Yaseera ya zanyi, nikam indai nabari shirin mami ya rushe batareda ta dau fansar nan ba nayi asara
Wallahi yaseera se yanzu nagane son gaske nakewa Jalal, wallahi zan iya komai akansa"
"Kina wannan sakalancin zaki iya komai akansa? Malama ki dage Dan wallahi wannan yarinyar da bariki zatayi zata Tara abun duniya,
Yanzu ki saurareni, batun kice kin gaji be taso ba, duk masifar daze miki kidena zuciya da shi, sannan kidena jin tsoransa, sannan kidinga kokari kema kina dafa abinci ki bashi, in wataran beci ba wataran zeci"
Ilham ta Dan girgiza kai
"Yaseera gani kike shawo kan Jalal abune me sauki ko? Mugun Dan taurin Kaine, ga shi jarababbe, yaseera tsawon shekarun nan danayi a gidansu ko inda yake bayaso inje, am about to give up"
"Ita Jalilan dayake daga mata kafa ba mace bace kamarki, iya bariki kawai tafiki, ki bar wani batun seya soki malama kawai ya aureki a wuce gurin"
"To yaseera insha Allah zan kuma jajircewa, Wallahi nida zuciyata tafara bani kawai inyi duk me yiwuwa kawai inyi me gaba daya"
Da sauri yaseera ta kalleta
"Baki da hankaline? Inkuma aka samu akasi fa"
"Nima abunda yasa nafasa kenan"
"Karki kuskura ki fara, kibi komai a hankali"
"To shikenan yaseera, zan cigaba da kokari"
Haka yaseera taita zigata sannan sukayi sallama, Ilham ta shiga Gida yaseera kuma ta tafi
Hannah ta kira wayar Jalal harta gaji dama seyaga dama yake amsa wayarta, yau ta kudurce wa ranta kome ze faru sedai yafaru Dan Gida zata bishi, lokaci yayi da yakamata tafara wasan kwallo dashi daga shi har kanwar tasa dole sugane wace Hannah,

Jalila bin Jalal tayi da kallo, wannan akwai Dan rainin hankali, shima Yaya Jawwad sekace Jaraba kowa da gidan ubansa ya zauna a can amma shi inbe bishiba shi ze biyo shi, a ranta tace kacigaba zan rama ne wannan wulakancin da kakemin bakaci bulus ba
A zahiri kuma ta ba sar ta kuma serving din Jawwad
"Yawwa Yar Baby, mungode sosai"
"To yayan Baby, permit me to leave"
"U can leave dear"
Tana komawa cikin Gida Maama ta kuma aikenta gidansu Jalal, waita karbo kaya anjima wasu customers zasuzo tun safe Jalila take aiki bata huta ba gashi bata son abunda ze hadata da Ilham, ba tayi musu ba ta juya ta kuma tafiya aiken da akayimata,
Tana fitowa taga wata mota a tsaye a kofar gidansu Jalal, harta gifta mortar, aka danyi reverse da motar saitin inda Jalila take, sauke glass din motar akayi wata matashiyar budurwa ce a cikin motar
"Sannu dai" tacewa Jalila
"Yawwa sannu"
"Dan Allah tambaya nake"?
" Allah yasa nasani"
"Naga kamar cikin gidan nan zaki shiga"
"Au kamace baki tabbatarba"
"Ohh sorry Dan Allah Jalal nake nema"
Kallonta Jalila tayi, tayi nazarinta na wasu yan mintuna sannan tace
"Me Jalal ze miki"?
" inason ganinsane"
"Baki da lambarsane?"
"Nakira bata shiga"
"Injiwa zance masa"?
"Kawai kice masa yayi bakuwa"
"Bahaka nakeba, inkina son ganinsa kifadi sunanki"
"Hannah ce, koke ce Ilham din da Jawwad yake gayamin kanwarsa da kike sonshi"
Da sauri Jalila ta kalleta, ta Dan kuramata ido wasu yan mintuna sannan tai murmushi
"Hannah"
Jalila ta maimaita
"Yeah I am Hannah"
Jalila ta kuma murmushi
"Zata iya yuwuwa nice Ilham kuma zata iya yuwuwa bani baceba, for now bazaki ga Jalal ba ki tafi kawai inma kin tsaya bazan bari ya fitoba, kune masu kara ingiza lalacewarsa, kalleki, kalli shigar jikinki a matsayinki na ya mace kina yawo half nicked, kinzo gurin namiji saboda abun kunya, me kike tsammani in mutane suka ganshi da ke, kibari in yaje inda kuke haduwa kya Ganshi amma ba anan ba, juya kikoma inda kika fito" Jalila ta hade rai tareda nuna mata hanya

Share please
More comments more typing.........................
Masoyana abun alfaharina comments dinku yana kayatar dani Allah yabar kauna

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now