ABDUL JALAL (2020)

473 28 1
                                    

                     _ABDUL  JALAL_

      _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
    (Daddy's girl)

               PAGE-  3
PART 1

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

       _My first novel_

Gaba daya suka waigo suna kallon inda jalila take maganar, taci gaba da fadin
"duk d'a nagari me fatan nasara a rayuwarsa, baya fad'i in fad'a da mahaifiyarsa wannan ba halin d'a nagari  bane me neman albarka,
wannan ba komaibane kake face tsantsar rashin tarbiyya!!"
ta kare maganar tana kallon cikin idon jalal,
ta kalli mummyn Jalal tace "mummy seda safe Nana ta taho da sakon"

      Idanuwansa ne sukayi jawur jijiyar kansa ta daddaga ganin yarinya Karama ta tsaya tana gaya masa miyagun maganganu,
    Wani yunkuri yayi da nufi ya karasa inda jalila take ya hukunta ta
Y7u
mummy tasha gabansa ta rikeshi gam, duk da ta danji ba dadi da Jalila takira Jalal Mara tarbiyya amma ta dake tare da fadin

"Karka kuskura ka tabata abinda tafada gaskiya tafada kadan kagani Indai haka zakacigaba dayiwa rayuwarka, indai zaka cigaba da gayamin maganganunu daka gadama kana wuakantani agaban mutane."

fizge hannunsa yayi da karfi 
"kicikani wallahi sena kakkarya yarinyar nan ni zata gayawa wannan maganganun wallahi sena koyamata darasin da harta mutu bazata mantaba,"
Da gudu jalila ta ruga ta fice daga palourn.

hannunsa ya fizge daga cikin na mummy ya rufa mata baya a zuciye, amma kash kafin ya fito harta bace kaman walkiya yanemeta yarasa, har bakin gate yafito amma be ganta ba, yanufi dakin me gadi Yakama buga masa kofa iya karfinsa,
a sukwane me gadi  ya fito babban mutum amma haka ya zube agaban jalal jiki na bari "ranka ya dade...." Begama ba JALAL ya katseshi

"kaii yarinyar da ta fita yanzu INA tayi,"  jalal ya katseshi

"Ranka ya dade sallah nakeyi banga fitar kowa ba"
" shut up!!! Useless man Sam bakasan aikinkaba dakiki kawai,"

A fusace ya shiga part dinsa zuciyarsa na tafasa, he wish Yakama yarinyar nan da ya nuna mata waye jalal,
'me yasa kika rikeni kika hanani daukar mataki akanta yafada a fili Dan karamin flower base din dake kan side bed dinsa ya dauka yayi jifa dashi yana huci,

"Waima Yar uban waye daga ina take"
Kaman yataba ganinta amma yamanta a ina ne

wayarsa CE tafara  ringing, bros jawwad ne yafito akan screen din wayarsa, yadaga wayar yakara a kunnensa, "
"Dan uwana meyasameka  tun dazu nake nemanka kazo ka karbi ajiyarka,
Wai yanaji kanata hucine me yafarune,"
"bari bros bakomai zan fitane inna dawo zamuyi magana wata Yar iskar yarinyace ta zageni kuma idona idonta sena lahira yafita jin dadi" JALAL yayi maganar a hasale,

"Subhanallah haba Dan uwana ya kake fadin haka kaifa me hakurine fushi banakabane nasan maybe wani   Abun kayi mataa kamanta da ita kawai yanzu dai kana ina"

"Bazan mantaba din wallahi sena koya mata hankali" cewar JALAL

"Easy bross karkayi fushi Manzon Allah salallahu"

"...........alaihi wassalam" Jalal yakarasa masa, "zaka fara Toni fita zanyi semun hadu da anyi magana sekace mutum yayi hakuri ka dauka kowa irin Kane"

"Dan uwana ina maka nasiha kaji tsoron Allah Dan an bata maka rai kar in kafita kasha giya Dan Allah kar kasha giya koka aikata abinda ba shikenanba babu abinda zata qara maka se bacin rai,
garaka... .."

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now