ABDUL JALAL (2020)

273 22 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 18

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢
Your comments give me courage

-My First Novel-

"Da kasake ka tafi da yanzu ka gane illar hawayen iyaye"

"Kinmanta kashedin danayi miki game dani ko? Har yanzu baki fasa min shishigi ba ki ji da rayuwarki, ba ruwanki da rayuwata"
Ya katse wayar ya aje tare da fadin
"Jarababbiya kawai, ko ina ruwanta dani oho, zan sauke mata wannan taurin kan"

Jawwad ne ya dawo ya tarar dashi
"Yunwa fa nakeji, find something for me to eat"
"Kamar me kake so"
"Komeye ma amma banda tuwo
Yarinyar nan ta kaimin abinci nazata wani abun kirkin ne ashe wannan abinne dabana ci saboda tsabar ta rainani aikuwa zan koyamata hankali"

"Ai kai abunda baka ci dayawa wanne daga ciki"
"Kaga ni abar wannan maganar me kukayi yau"
"Nima banci abincin ba alala sukayi yau"
"What alala kuma,"

Ya Dan girgiza kai
"Kasan itama bana ci"
"Anyway bari in canza kaya muje restaurant se muci"

"Kar ka kaini inda za abani abunda za bata min ciki kasan bana son jagwal gwalo"
Murmushi Jawwad yayi

"Jalal kaima yakamata ka canza kayan nan kasaka manyan kaya"
"Nifa bana son wannan kayan nauyin isa ta suke da zafi"
"Please dan Allah kasa manyan kaya"

Jawwad ya fada yana Ciro masa wata hadaddiyar Shadda coffee colour yaita lallaba shi har ya yadda ya karba ya canza kayan yasaka shaddar nan,
Ba karamin kyau Jalal yayi a cikin kayan nan ba manyan kaya ba karamin fito da kamalar namiji yake ba Jawwad yaita koda shi, yana masa hotuna yana yaba masa yayi kyau,
Haka suka shirya suka tafi restaurant cin abinci

Jalila ce a office din malamai ta inda suka shiga ba ta nan suke fita ba suna mata fada akan rashin ji
Saboda ankawo kararta akan jiya ta tsokanowa yan uwanta dalibai yan daba, masu zaginta sunayi irinsu malam Naziru, masuyi mata nasiha sunayi ita dai Jalila shiru tayi batace komai ba suka gama ta tashi ta koma aji tanata cika tana batsewa
Ba a jima ba malam Naziru ya shigo ajinsu da hanzari yana kiranta
"Jalila zancen musabakar nan ne ya taso wadda za ayi a Abuja sati me zuwa insha Allah"
Wani irin mugun kallo Jalila tayi masa tai masa banza
"Jalila da ke nake fa kije ki jadadda hadda abun yazo mana a bazata dukda nasan bani da damuwa akanki"
"Ba inda zani kunemi me zuwa karkuje inja muku magana, yaza ayi kamata taje musabaka "

Tafada tana hade rai
Sekuma ya Dan sha jinin jikinsa
"Wai meye hakane Jalila ana magana kina wani zance daban ina miki magana"
Mikewa tsaye tayi tare da kara hade rai

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now