ABDUL JALAL 83

339 23 4
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 3️⃣0️⃣83

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com




_MY FIRST NOVEL _

Hanan takuma dawowa zata wuce
Abdallah yace

"Auta bakiga Jawwad din naki bane?" dan kallon Jawwad tayi, tayi murmushi tace
"Naganshi mana" Naja kamewa tayi a gurin musamman da taga Jawwad yana kallon Hanan, da alama beji dadin yadda Hanan taki kulashi ba.
Abdallah yace

"Wallahi Hanan totally dinta se a hankali, duk ta takuramin wai muyi Sauri muzo taganka amma ta ganka ta wani basar" Jawwad yai murmushi yace
"Kyaleta Abdallah zamu shirya ne, maybe gajiyar Hanya ne ya hanata yimin magana"
"Bawani gajiya tsabar wulakanci ne kawai" Hanan ta murgudawa Abdallah baki, suna hada ido da Jawwad ta kashe masa ido daya, gaba daya ya rikice, gani yake kaman kowa yaga Abunda Hanan tayi gaba daya yakasa sukuni,
ita kam Hanan ta wuce Naja takoma inda tabar Jalila a daki, ba kunya Naja takuma biyota dakin, Hanan tana shiga tace

"Ohh God, Jalila Haidar yakara kyau yakuma zama babban mutum, wayyo dadi kasheni, naga farincikin zuciya ta" Jalila tace
"Waye kuma Haidar?"
"So kike indinga kiransa da sunan da kike kiranshi ne, kowa yace Yaya Jawwad nima ince Yaya Jawwad, Haidar dai kaman in sace shi in gudu haaka nakeji, yawwa Queen ranar muna waya dake naji wata namin kashedi akan abunda yake mallakina, wacece dan Allah?"

"Nice nan, kuma wallahi duk maitarki iyayenmu sun tsaida magana, bashida wata mata in baniba, mayun banza dana wofi marasa zuciya" Naja ce taketa fiffika tana fadan maganganu Hanan taja wani dan tsaki tace

"Jalila aina dauka wadda take cewa zata auri Jawwad din mace ce, ashe mata maza ce mata ta rako duniya, ke cewa akayi ya Aureki, nikuma Jawwad yana sona ne" , dan saurin kallonta Jalila tayi, lokaci da dama Jalila tana daukar abunda Hanan take a matsayin wasa, dukda tana ganin tsagwaron gaskiyar abunda Hanan din ke nufi a idonta Jalila na cikin wannan tunanin Hanan tace
"zan tabattar da hakan anan kusa ba a nesa ba, ke Queen ina mutuminne tunda nazo ban ganshi ba"
"Wakenan?"
"kinfini sani, Jalal mana" tsaki Jalila tayi tace
"Nifa bana son maganar wannan shirmammen"
"Jalal dinne shirmamme?"
"Eh shidin, ke Akwai Labari amma semun je bauchi Lafiya insha Allah"
"To Allah ya kaimu lafiya"

Abdallah yace "Jawwad nikam ina Jalal ne naganka kai kadai?" Jawwad yace
"Yana part dina baya jin dadi"
"Allah sarki, muje inganshi, muyi salla Azahar sannan mu wuce"
Suka tashi suka tafi part din Jawwad, suka tarar da Jalal zaune akan kujera, yana kallon TV amma sam hankalin sa baya kan Tv, shigowarsu yasa ya daga kai, murmushi yayiwa Abdallah, ya mika masa hannu suka gaisa

"Jalal ashe bakaji dadi ba? Sannu gaskiya ka rame, Allah ya sawwake"

"Abdallah aini na warke tuntuni, Jawwad ne da zuzuta abu"
Jawwad yace

"Au ni nake zuzuta abu, dadinta kallo daya za'ayi maka asan baka da lafiya" sukayi Salla, suka zauna sukayi ta hira, Jalal ya sake sosai.

Can aka jima Abdallah ya kira Hanan a waya yace su fito yanzu zezo su tafi, Hanan tace masa to, Jalila ta nunawa Hanan akwatinta tace
"Hanan kaimin mota, bari in sa kaya" Nana tace
"bari inje ingayawa Abba zaku tafi" Hanan ta ja trolley Jalila ta kai bakin mota, amma motar a rufe, tasan Abdallah suna part din Jawwad kanta tsaye ta tafi part din, tun daga waje take iya jiyo hayaniya su , shiga tayi da sallama duk suka amsa mata, ta fadada murmushin fuskarta ta Kalli Jalal tace
"Yaya Jalal kwana dayawa, Yakake ya gida amma naga ka rame sosai" shima murmushi yayi mata yace
"lafiya kalau Hanan, amma aini haka nake dama can ban rame ba, yagida ya hanya?"
"Alhamdilillah, ina wannan kanwar taka, yama sunanta?"
Abdallah yace
"Kai Aku me magana, daga zuwanki kinfara zuba kaman kanya"
Dan hade rai tayi
"kace mufito kuma ka kulle mota, ga kayan queen can na fito dasu, kazo ka bude in samata a mota" Abdallah yace
"Sedai kizo ki karba kibude, bari mugama hira"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now