ABDUL JALAL 69

357 22 3
                                    

.🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 1️⃣6️⃣ 69_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com


_MY FIRST NOVEL _

WANENE ABDUL JALAL???!!!!!

Khadija munir shine cikakken sunan mahaifiyar Jalal, malam munir shine mahaifinta suna zaune a unguwar dorayi dake cikin garin kano, malam munir malamin makarantar secondary ne, sannan yana yan sana'oinsa domin rufawa Iyalansa asiri, yanada mata uku, hauwa itace uwargida, se sadiya itace matarsa ta biyu, da zulaihat itace matarsa ta uku, yanada yara goma sha uku, khadija 'yace ga sadiya matar malam munir ta biyu, khadija su ukune agurin mahaifiyarsu, itada yayyenta maza biyu, Abubakar da Aliyu, itace yarinya ta tara a gurin mahaifinsu, khadija tana da kyau daidai gwargwado, wanda har wasu suke cewa duk tafi yaran gidan kyau, dukda kasancewar ta ba fara tas ba amma tanada kyau, khadija yarinyace mara kunya, bata dagawa kowa kafa, duk wanda yayi mata duk yarintarsa duk tsufansa zata cimasa zarafi babu ruwanta, tun yayyenta na kamata su daka intayi rashin kunya harsuka gaji suka kyaleta, saboda rashin mutuncin ta bata bar kowaba ciki harda matan babanta da yayyenta.
mahaifiyarta ta sangarta ta kasancewarta ita kadaice yarinyarta mace, duk wanda ya daki khadija ranar se anyi tashin hankali da mahaifiyarta, har kirari takewa khadija cewa
"ni 'yata matar manyace, se wanda yaci yatada kai zan bawa, dan khadija na ba kalar talakawa bace" hakan yasa abun yafara tasiri a zuciyar khadija tun tana yarinya, takejin cewa kota isa aure seta samu me kudi zatayi aure idan kuwa bata samu me kudiba, gara ta tsunduma ita tanemi kudin dan bazata iya auren talaka ba, kuma batason rayuwar wahala.
indai khadija nason abu, kaya kona uban waye koda kudi ko a bashi, mahaifiyar khadija zata siyamata su.
Saudat kanwace ga khadija sakuwarta ce khadija tabata shekara daya da rabi, ita saudat 'yace ga zulaihat amaryar malam munir, itace ta biyu a dakinsu, wani lokacin suna matukar shiri ita da khadija saboda halinsu yazo daya dukkaninsu tsagerune, Sedai Khadija tadama saudat ta shanye a tsageranci, dukda wannan shiri dasukeyi baya hana in tsiyar khadija ta motsa tayiwa babar saudat rashin mutunci a hadu aita masifa a gidan nan, makaranta da yan unguwa babu wanda besan halinta ba, karamin aikintane ta zagi malami agaban dalibai, in an koreta mamanta seta canza mata makaranta, dama islamiyya tuni ta dena zuwa, a cewarta tunda tasamu na salla shikenan, dan bazata jure wannan masu gemun kaman brush suna dukan kyakyawar fatarta da fatar bunsuru ba, abun dukan doki, malam munir yayi iyayinsa gurin ganin khadija ta nutsu amma abu yaki yuwuwa.
Abinci se wanda taga dama zataci, sutura se wadda takeso zata saka, wani wanki da guga almajiri uwatta take biya yayiwa khadija, haka dai rayuwar khadija ta tashi a mugun sangarce, ga rashin tarbiyya.

Tun tana jss2 tafara samari, inda a nan ne ta hadu da saurayinta Kabir, Kabir yana matukar sonta kaman yayi hauka, Kabir marayane, mahaifinsa ya rasu, dagashi se mamansa da kannensa mata biyu, shikadaine namiji gashi mahaifinsa bebar musu wani abun kirkiba se gidan dasuke ciki, seyaje yayi aikin wahala yake samo abunda zasuci yake biyan kudin makarantarsu, tunda yafara soyayya da khadija abubuwa suka fara tabarbarewa saboda yawan bani2, yazamana da kyar yake iya morawa mahaifiyarsa da kannensa wani abu sedai yayiwa khadija haka yadinga dawainiya harta shiga sss, nan manyan mutane suka dinga fitowa suna sonta, duk cikin mane manta babu wanda yayi mata saboda ita burinta ta auri namiji kyakyawan gaske sannan wanda ya tada kai da naira, sannan tanada burin tazaga duniya, tayi ilimi me zurfi a kasashen waje, yadda zata goga kafada da manyan mata a kasar Nigeria dama nahiyar Africa gaba daya, shiyasa duk wanda yazo indai yanada kudi zata wankeshi son ranta sannan ta sallemeshi, dan har yanzu bataga dai dai da itaba, malam munir yayi iya yinsa dayimata nasiha itada yar uwatta saudat amma abu ya gagara, ana cikin wannan haline Allah yayiwa malam munir rasuwa, mutane sunji mutuwarsa saboda mutumin kirki ne kwarai dagaske, bayan an gama makoki khadija tacigaba da tsiyarta daga inda ta tsaya, ganinda Kabir yayi masu kudi na neman aurenta yasa kara zage damtse, daya samu kudi ko anmusu albashi dayake yasamu aiki a wani kamfani, seyaje ya kashewa khadija su, har rawar jiki yake wasu kudin sushigo yakuma kaimata, alhalin gidansu wataran se a kwana biyu ba a dora tukunya ba, se ayi term biyu ana korar kannensa saboda kudin PTA, amma baze iya basu ba sedai khadija.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now