ABDUL JALAL 63

355 22 1
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 1️⃣0️⃣/63_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com


_MY FIRST NOVEL _

Ita kanta Jalila setaji kaman tace A'a amma taji nauyin yin hakan, daddy yakuma cewa

"Jalal maza kunna motar ku tafi karta makara"

Jalal kaman yace bazashi ba amma yasan yana fadan hakan tasamu abunyi, ta samu abun masa gori, bece komai ba ya bude motar ya kunna, Jalila ta tafi ta bude gaba ta shiga,

Daddy yace

"yawwa Allah yayi muku albarka sekun dawo"
Jalila ce kawai tace Ameen, Jalal ya kunna motar yajata da gudun tsiya, yadda yake gudu yasa Jalila ta kalleshi

"ni gaskiya in wannan ganganci za'ayi da rayuwata ka saukeni, akanme inkasaba kasada da rayuwarka to badaniba"

banza yamata yacigaba da tukinsa, yadda yake ratsa tsakanin manyan motoci yasata runtse ido tana ambaton Allah, kallo daya yayi mata ya dauke kansa,

"dan Allah ka tafi a hankali koka tsaya in sauka" jitayi an tsaya hakan yasata bude idonta, gani tayi yayi parking, yasa hannu yana dakko taba yana kokarin kunnawa,

"kutmelesi meye haka ne?" banza yayi mata ya kunna tabarsa, sakin hayakin yayi fuuu a cikin motar, juyawa tayi zata bude kofar motar amma taji a kulle gam, yasa lock ta kalli agogon hannunta ta makara sosai ana daf da shiga exams.

"wai meye haka dan Allah? nika budeni in tafi zan makara, ga warin hayaki ya isheni"

Shiru yakumayi ya kwanta sosai a jikin kujerar yana busa hayakinsa, ji tayi kaman ta wanka masa mari, yanajinta amma yayi banza da ita kamar wani itace, dafe kanta tayi, wayarsa tafara vibration ya dauka yaduba message din Hanna ne danhaka ya ajiye wayar tareda fadin

"wasu matan are just useless" Jalila ta dago ta kalleshi,

"ai Useless din ba iya mata bane hada maza, dan gara mata da wasu mazan dabasa jin magana" wani dan guntun murmushi yayi, wanda shikadai yasan yayi shi, gani tayi ya shanye sigari kusan uku tana zaune yakuma kunna wata, hannu tasa ta fizgeta ta jefata waje

"wallahi baka isaba, akanme ina zaune zaka dinga shan taba ka cikani da hayaki salon inje aji a dauka ninasha tabar, ka budeni in tafi in yaso kaima kazama tabar, batareda ya kalleta ba yace

" warin taba ai kin dade kinayinsa, ba iya taba ba harda na giyama kinayi, kece baki saniba amma nakusa dake sun san hakan" kallonsa tayi alamar bata fahimta ba
"ya za'ayi nida bana shaye2 indinga warin giya, Allah ya kiyaye"

"bakiyi addu'ar a inda ya daceba, dan kinriga kin makara, kuma ba lallai sekina sha zakidinga warinsu ba"

hannunta ya kamo, ya nunamata

"a jininki abun yake, akwai jinin 'yan giya a jikinki dan haka sekidena cika baki" ita Jalila sam batagane inda maganganunsa suka dosa ba.

wayartace taketa ringing tasa hannu ta dakkota Alhaji Kabiru ne akan screen din wayarta, screen din Jalal ya tsurawa ido yai shiru kaman me nazari, ya kalleta ya kalli wayar, kashe wayar tayi ta mayar cikin jakarta, kallon tuhuma yayi mata na wani dan lokaci, sannan ya dauke kansa.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें