ABDUL JALAL 90

389 23 3
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 3️⃣7️⃣90

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com




_MY FIRST NOVEL _

"wakenan?" ya tambayi Mummy yana kallonta

"eh da ita yarinyar daka dawo dan ita mana, tunda tana maka abunda bana maka, wallahi kaji tsoron Allah, ba irin Magiyar da banyi maka ba, Amma kayi biris amma yanzu dayake tafini ai gashi kadawo"

Tsyawa yayi ya zubawa Mummy ido tagama masifarta, seda tagama, Yayi tsaki ya tashi ya fice yana masifa.

Haka yakoma dakinsa yana mita yana tunanin meyasa ma yaje inda take, Mummynsa bazata canza hali ba, Jalila tana matukar girmama ta, amma ta rufe ido se masifa takeyi, shiyasa bayason rabar Mummynsa.

Jalila tanata lissafi gobe su Abba zasu dawo, dan haka ta tsananta Addu'a Allah yabata sa'a yasa Abba ya janye batun Aurawa Jawwad Naja.

Yauma Jalila taje school, sun kammala lectures, sunfi to itada Zahra, Zahra tace

"Yawwa nikam Jalila naji Wata suna hira tace wai jiya wani hadadden gaye yazo yasaki a mota ya tafi dake, amma wai dagani dan shaye2 ne dan wuyansa hada sarka, ga wani irin Aski akansa, ina fatan lafiya ba wata matsalar bace?"

Dan karamin tsaki Jalila tayi aranta tace"
dan jaraba da masifar mutane komai kayi idonsu akanka
"Eh haka akayi, seme kuma?"

"A'a ba komai dama nayi tunanin ko mutanen baban Saleema ne"

"to basu bane, Yayana ne"
Jalila tabata amsa a takaice, Dan zare Ido Zahra tayi

Zahra tace "dama kinada yaya dayake shaye2, na zata Yaya Jawwad ne kawai Yayanki"

"Akwai wani to, kuma akansa nayiwa Alhaji Kabiru baban Saleema, abunda yanzu yana daf da zuwa prison shida 'yan tawagarsa"

"Amma Jali....

" Ke zahra kin isheni wallahi, nagaji ga yunwa ina ji se faman tambayoyi kikemin, sekace wata likita, haba se Allah ya kaimu gobe"

Inda sabo Zahra tasaba da halin Jalila, tanada saukin kai Amma tanada tsari a komai nata, in bakasan halinta ba zakace batada kirki ne kawai, bata da san yawan tambaya.

Mummy ta bawa Ilham kudi tace ta kaiwa Nana ta ajiyewa Maama in ta dawo a bata, Ilham ta karba harta shiga gidansu Nana wani tunani ya fado mata a rai, dan haka tayi murmushin mugunta tashiga gidan. Ilham Tana fitowa hakan yayi dai2 da dawowar Jalila daga makaranta sukayi karo a kofar gida. Ilham ta tsare Jalila da ido tana mata kallon zaki gamu dani ne.

Jalila tace "Ilham wai kin manta maganar danayi mikine? Ki dawomin da Al'qur'anina tun muna sheda juna dake?"

Ilham ta rike kugu ta kalli Jalila "idan naki fa? Me zakiyi?"

"Aimeyi baya fada se dai kigani a aikace, zakiga matakin dazan dauka, ki kawomin abina na gayamiki"

"ina jiran ganin matakin dazaki dauka din, amma kafin ki dauka ni ki saurari nawa"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now