ABDUL JALAL (2020) 35

259 12 1
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 35

PART 1
Share please

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
ABDUL JALAL NOVEL FANS
Love u all guys ❤❤❤❤❤

-MY FIRST NOVEL-

Nana ta bude motar ta shiga, motar tayi kyau matuka, Jawwad ya kalli Jalila
"baby shigo mana"
Jikinta a sanyaye ta bude motar ta shiga, Jalal yai musu banza yacigaba da danna wayarsa
Jawwad ya kalleshi "muje ko"
"Ina zuwa" yacigaba da aikin wayarsa sun shafe kusan minti goma shabiyar a zaune sannan yayiwa motar key, aikuwa kamar yadda Jalila take fargaba a guje ya fafari motar nan kaman zasu tashi sama, Jalila se rarraba ido take tana karanta adduo'i daban² a zuciyarta, tabbas Jalila ta yadda sun hau motar Dan giya, yadda yake gudu dasu sekace a Action movies kaman ba mutane ya dakko ba haka yake ratsa manyan motoci yana overtaking
"Wayyo Allah Nikam nashiga uku gaskiya a tsaya in sauka wallahi, na hakura da duba Jarrabawar, ni kadai Ummi ta Haifa baza a kasheni a wannan gangancin ba"
Jalila tayi maganar da karfi
"Yi hakuri baby, Jalal Dan Allah sassauta gudun nan Jalila a tsorace take, guri yasamu yaja wani arnen parking
" ta sauka ta fita in bazata iya zama ba"
"Wallahi bazan sauka ba sedai kai ka sauka ai ba......." Bata gama ba Jalal ya juyo yana kallonta tai saurin yin shiru
Jawwad yace
"Baby kiyi hakuri babu abinda ze faru lafiya zamuje insha Allah"
"Ni gaskiya tsoro nakeji"
Nana ta kalli Jalila tana dariya
"Runtse idonki ki kwanta akan cinyata zaki denajin tsoron"
Ba musu ta kwanta akan cinyar Nana ta runtse ido Jalal ya Dan kalleta, ya maida kai ya cigaba da bawa sabuwar motar Jawwad wuta
Jalal Ya samu cafe a hanya yayi parking
Suka fito daga motar gaban Jalila se faduwa yake tana fargabar me zata gani a result dinta, Jalal yana zaune a cikin mota be fito ba
Jawwad yai musu Jagora suka nufi shiga cafe Jalila ta tsaya a kofar shiga
"Ya dai muje mana"
Nana tai maganar tana janyo hannun Jalila
Jalila tayi ajiyar zuciya
"Nana karbi exam card dina ni bazan shigaba abinda kuka duba seku gayamin"
Ta karasa maganar kaman zatayi kuka
"Haba Jalila in kika karaya nikuma ince me, karki damu taho mushiga"
"Nana Allah bazan shigaba, ina nan sekun fito"
Haka Nana ta hakura ta kyale Jalila, tabi bayan Jawwad yayinda Jalila ta tsaya a kofar gurin, kallon da mutane kewa Jalila ne yafara bata haushi Dan ita bata San kallo
Jikin motarsu ta koma taje ta jingina ta tsaya, Jalal ya bude kofar motar ya kashingida a jikin kujerar mota
Jalal ne yake waya tana iya jiyo abinda yake cewa dukda a hankali yake maganar
"Hannah meyasa kike takuramin a rayuwata, kin uzzuramin wallahi,
Ke ko zuciya baki da ita, haba Dan Allah nifa bazan iya wannan shirmen nakiba, kozanyi aure Hannah kinsan bazan iya auren mace kamarki ba"
Jalila ta Dan waiga ta kalleshi,
Taja tsaki
"Mtseeew shirme, sekace wani mutumin kirki, suna zubarwa da Kansu mutunci a gurin wannan Dan giyar, wahalallu dagasu har shi, kowace wannan Hannah oho" ta cigaba da mita daga inda take
Wayarsa yacigaba da yi Dan besan tanayi ba
Jawwad ne da Nana suka fito daga cafen, fuskarsu babu annuri suka nufo inda Jalila take
Hankalinta ne yai mummunar tashi ganin yanayin fuskarsu, suka karaso bakin motar
"Na fadi ko yaya, banciba, na fadi Jarrabawar ko?"
Mikomata paper yayi sannan yace
"Congratulations my dear u got it, am proud of you"
Yai maganar yana murmushi tareda Jan hancin Jalila, bude result din tayi
A¹ bakwai tasamu B guda biyu
Rungumeta Nana tayi
"Ina tayaki murna Babyn Abba"
Jalila ta kalleta "Nana me kika samu"
"Nine credits ne"
Murna suka cigaba dayi
"Is OK murnar ta isa haka, kushiga muje, aje shan ice cream, proud of you all, Allah yayiwa karatunku albarka"
"Ameen suka fada a tare"
Suka bude motar suka shiga, Jawwad ya dubi Jalal yace
"Jalal kaga results din su Nana, Alhamdilillah, result yayi kyau, mussaman na Jalila"
Dan kallon papers din hannun Jawwad yayi yana kokarin kunna motar
"Mmm yayi kyau Allah yasa ba satar amsa tayiba"
Kutmelesi Jalila taso gayamasa bakar magana Dan dai Jawwad yana gurinne, Jawwad ya kalleshi
"Wuce nan bros, duk cikinsu ba wadda take satar amsa"
"How sure are you?"
Jalal ya tambayeshi
"Obviously na yadda da kannena, ranar graduation dinsu Jalila awards din da aka bata sun isa su tabbatar daba ta satar amsa"
"Hmmmm" shine abinda Jalal yace ya fizgi motar a guje yabar gurin
Jalila kuwa se kunkuni take tana magana a ranta, ita kuwa Nana se hira take mata, tana kuma jinjinawa Jalila dangane da result dinta, itakuwa Jalila Kalmar satar amsa ta bakanta mata rai sosai
"Ashe dai ba iya Neman maganar aka iyaba kan yana kawo wuta, shiyasa kike burgeni mutuniyata, baki da wasa"
Nana ta fada tana Jan hancin Jalila
Jalila ta rirrike Nana, saboda gani take a kowane lokaci motar nan zata kife saboda tukin da Jalal yake
A wani joint sukayi parking Jawwad yayi musu rakiya sukaje suka sai abinda sukeso, sannan suka fito suka nufo hanyar gida
Suna cikin tafiya Jawwad yace
"Baby, Nana dai mass com takeso, kekuma fa?"
"Yaya ni nursing nakeso,"
"Wow, u can do it, Allah ya temaka"
Wayar Jalila tafara ringing bakuwar lamaba ce, kamar karta daga, sekuma ta daga tare da yin sallama
"Wa alaikum salam, Jalila Ashe kinkoma kano babu labari?"
Jalila ba ta dau muryava Dan haka tace "wake magana"
"Kai Yar baba, kardai kice baki ganeniba"
"Subhanallah, Yaya Abdallah yi hakuri kasan banida lambarka se yanzu nagane, barka da yamma"
"Yawwa Jalila, yakike?"
"Lafiya kalau ya daddy"
"Yana lafiya, Ashe kinkoma kano, nazo Gida attending birthday Hanan, take gayamin"
"Aikam dai Yaya Abdallah ina kano,"
"Kice zamu dinga haduwa kinsan a bayero nake karatu, na dinga kawomiki ziyara"
"To shikenan Yaya nagode sosai"
"Insha Allah weekends din nan zamuzo, da daddy da Hanan"
"Dagaske Yaya"
"Dagaske nake"
Zuwa yanzu Kishine yake cin Jawwad jin yadda Jalila ta saki jiki tana waya, da wani namiji, Jalal ya Dan kalleshi yaga yadda ya wani hade rai, Dan murmushin gefen baki Jalal yayi yacigaba da tukinsa
Jalila suka gama waya da Abdallah ta kalli Nana
"Nana da weekends insha Allah usainata zasuzo, zasu kawomin ziyara"
"Wa kenan?"
"Hanan mana"
"Dan Allah dagaske"
"Wallahi Nana"
Jawwad ya Dan gyara zama
"Baby da wa kike waya?"
"Yaya Abdallah ne"
"A ina yake?"
"Abokin nan nakafa, Dan gidan captain Rasheed"
"Hmm nagane"
Daga nan be kuma cewa komai ba harsukaje gida, lokacin ana kiran sallar magariba,
Suna zuwa gida suka tarar Maama tana salla Abba kuma ya tafi masallaci, Dan haka suka tafi dakinsu, halimace ta biyosu a baya, tana fadin
"Jalila ya akayi,? Ya jarrabawar kuwa?" Jalila ta tsaya tana murmushi, Nana kam bata tsayaba ta wuce dakinsu
"Leemart jarrabawa Alhamdilillah, kinga results dinmu" Jalila ta mikamata result din
Karba halima tayi ta duba
"Masha Allah, Jarrabawa tayi kyau kam, Allah ya sanya alkhairi, Yasa a ci gajiyar karatu"
"Ameen my leemart, bari inje zanyi salla"
"To shikenan"
Bayan sunyi sallar magariba suka tarar da Abba a part dinsa Maama ma tana part din, suka bashi result din yayi murna sosai yai musu addu a, da fatan alkhairi
Sannan ya dauki kayan da yakawo musu tsaraba yabasu, na Jalila harda brown din Teddy da kayan sawa na alfarma, sukayi masa godiya
Nana se tsokanar Jalila take wai ta ci sunanta baby ta girma amma tana wasan teddy
Maama ta tabe baki
"Nima haka Nagani, yarinya da girmanta amma kana sai mata teddy, wannan ai sangarta ce"
Murmushi Abba yayi
"A ganinkine sangarta, ni a gurin kyautatawane"
Da Jalila taji haka ta mike ta bar part din gaba daya ta koma dakinsu
Suturar da Abba yabasu manyan suturune masu tsada matuka
Bude trolley dinta tayi ta debo wasu kaya masu kyau kala hudu, ta Dora turare body spray da roll on, ta bude kayan dasuka siyo, dazu dasuka fita ta dakko ice cream roba daya ta hada ta fito, sukayi clashing da Nana ta kalli kayan hannunta
"Wannan kuma fa? Me zakiyi dashi"
" Halima zan bawa"
"Saboda me"?
"Nima Allah yabani wasu, ba tare da yayi shawara daniba"
"Kudi fa ake biyanta meyasa zaki dauki kayanki masu kyau kibata"
"To meye a ciki Nana, naci jarrabawa Alhamdilillah Abba yamin kyautuka, yakamata mu farantawa wasu muma"
Dan tabe baki Nana tayi ta wuce daki yayinda Jalila ta nufi dakin halima

Ilham tarasa abinda yake mata dadi yan kwanakin nan takasa gane inda Jalila tasa gaba shin da gaske Jalila tana son Jalal, kokuwa, amma in tana sonshi ya za ayi tagaya masa wannaan miyagun maganganun,
Amma kuma ya akayi Jalila take gaya masa maganganu son ranta amma be dau wani mataki akanta ba, Wanda ta tabbatar ita bata Isa tayi masa haka ba,
Kenan shima yana son Jalila, tunda take gaya masa maganar data ga dama amma ya kyaleta
"Kan uba karyane wallahi ina wani shirmen hakan ze faru"
Tai maganar a fili
"Ko mami zan kira in gaya mata abinda yake faruwa, yanzu ina gaya mata ni zatayiwa fada tace laifinane, kuma baze yiwu in gayawa Nana ba tunda Yar uwattace za a iya hada kai da ita a cuceni, yanzuma watakila bakinsu daya"
Tayi nannauyar ajiyar zuciya to ni yazanyine?
Ko gidan malamin nan zanje da kaina innemi yaseera ta rakani(kawar Ilham ce) hakama za ayi inje inji ya za ayi aimin maganin wannan tantiriyar
Da wannan shawarar da zuciyarta ta bata ta samu nutsuwa

Halima ta kalli Jalila
"Jalila inani inasaka wannan kayan masu tsada"
"Leemart to meye a ciki, ba wani kaya masu tsada, sedai in abun hannuna ne bazaki karba ba"
"A a Jalila ba haka bane,"
"To in ba hakabane kawai ki karba"
"Nagode Jalila, Allah ya faranta miki kaman yadda kikayimin"
"Ameen leemart"
Jalila ta koma daki ta kira Ummi a waya tagaya mata abinda tasamu a result dinta Ummi tayi murna sosai, sannan tace
"Jalila ya yanayin zamanki a kano? Naji muryarki cikin farin ciki ina fatan komai lafiya?"
"Komaiafiya Ummi, bakiga Mayan da Abba ya siyo mana ba,"
"Masha Allah, haka nakeson ji, yacigaba da hakuri da rayuwa Jalila,"
"To Ummi insha Allah, Ummi da weekends insha Allah Hanan zasu kawomin ziyara"
"Dagaske baby"
"Dagaske Ummi, dazu Yaya Abdallah ya gayamin"
"Allah sarki gaskiya suna kaunarki Jalila, Nima next week insha Allah zanzo, daga nan zan wuce garinmu"
Haka nan se Jalila tayi jikinta yaysanyi
"Ummi tafiyar tana nan Ashe zakiyi,?
"eh tana nan zanyi insha Allah"
"To Allah ya kaimu, next week din"
"Ameen ki gaida mutan gidan"
"Zasuji insha Allah"
Nana ta Dan kalli Jalila
"Yanaga jikinki yayi sanyi"
"Nana banason tafiyar nan da Ummi zatayi"
"Haba Jalila, Ummi yakamata tayi tafiyar nan yana da kyau taje taga danginta"
"Hakane Nana"
"Yawwa to kidena tayarda hankalinki, kiyimata addu a kawai"
"To Nana"
"Yawwa babyn Ummi"
Daren ranar Ilham batayi baccin kirkiba se tufka da warwara kawai tekeyi, kamar ta janyo safiya tayi domin taje gurin malamin nan
Washe gari da safe wajen karfe goma Ilham ta shirya tacewa mummy zataje gidansu
Ummi tace seta dawo, tana fita ta tafi gidan su yaseera, suka gaisa da Maman yaseera sannan ta wuce dakin yaseera, ta tarar yaseera ta shirya ita take jira ko zama Ilham batayiba suka fita ita da yaseera sukayi gidan malamin nan

Share please
More comments more typing................................

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz