ABDUL JALAL 106

1.1K 25 2
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣3️⃣ 106

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

_MY FIRST NOVEL _

Tunda suka doshi gidansu Jalal gaban Jalila ke wata irin mummunar faduwa ta dinga karanta duk abunda yazo bakinta, suna tun karar kofar da zata sadar da kai da cikin gidan gabanta na cigaba da faduwa kirjinta se bugawa yake da karfin gaske.

Anty ce tafara sa hannu ta murda handle din suka shiga.
A babban parlour suka zaunar da Jalila, Hajiya Salma ta kira daddy a waya tasanar masa sun iso amma basu ga kowa a parlour ba, da yake daddy ya koma, dan haka ya kira Mummy a waya yace taje parlour tana da baki.
Abun ya bata mamaki sosai, wani irin bakine haka da bazasu kirata ba, fitowa tayi ba tareda tayi tsamanni ba tayi karo dasu Hajiya Salma a zaune a palour, rabon da taga hajiya Salma tun lokacin da ta bar mata gidan, Salma tana nan da gayun ta ba kace ta haifi Mahmud ba.

A fusace Mummy ta dube su a wulakance tace

"lafiya daga ina? Mekuka zo yimin?"
Hajiya Salma tace.
"kwantar da hankalinki mana Hajiya khadija, ba abun zafi bane ba, Matar danki muka kawo miki, ki musu Addu'a ki sa musu Albarka zamu kaita gidan danki"

Wani tsinannen Kallo Mummy taiwa Hajiya Salma tace

"Albarkata ake nema a wannan Auren munafuncin, da kuka haďa kai kuka aura masa yarinya ba da izinina ba, shine zakuzo wani wai in sa muku Albarka, bazasu taba samun Albarkata ba, saboda bana son yarinyar nan, na tsaneta tun kafin ta Auri ďana take juya shi, abunda takeso shi zeyi danme zan kaunace ta? Auren nan baze taba Albarka ba, kuma wallahi sena ga bayansa, senaga bayan Auren nan "

Anty tace
"Allah sarki, abunda kike gudune se ya faru, sannan Jalila taimakawa Ďanki take, kin san ba dan mutunci da girmamawa ba, Baza'a dauki nutsatsiyar yarinya abawa ďanki ba"

"tunda ansan ba nutsatsen bane, uban meyasa a lika masa wannaan yarinyar?, se a kyaleshi da halinsa in aura masa yarinyar da nake so, wallahi bazan taba son yarinyar nan ba, da nake mata kallon mutuniyar kirki amma tunda tafara bin dana nagane makira ce mara mutunci "

Rirrike Hajiya Salma Jalila tayi ta kara sautin kukanta, Hajiya Salma tace

" ko ki sota ko karki sota Allah ya riga ya haďa Auren nan, zuwa yanzu yaci ace kinyi laushi kinyi hankali amma babu alamar hakan a tare dake, Allah shaida ne ba abunda yarinyar nan ta miki da ta cancanci wannan kiyayyar da mugun bakin daga gareki"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now